Ƴan Ta’adda Sun Kashe Mutane 62 A Garin Zuru Dake Jihar Kebbi, Da Wasu Yankuna A Jihar Neja

 Kungiyar “Arewa Media Writers” tana kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar marubutan Arewa “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, tayi Allah wadai da kisan da ƴan ta’adda suka yiwa al-ummar garin Zuru dake jihar Kebbi da wasu yankuna na jihar Neja da suka haɗa da ƙaramar hukumar Rija’u da sauran su.

Arewa Media Writers” tayi takaici da jimamin faruwar wannan mummunan ta’addacin da aka yiwa ƴan uwan mu dake yankunan.

ƙungiyar tana sake kira da kakkausan harshe ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa, don al’ummar yankin su zauna cikin kwanciyar hankali.

Arewa Media Writers tayi Addu’ar samun rahama ga mamatan da suka rasa rayukan su, wa ƴanda suka rasa ƴan uwansu Allah ya basu ikon jure rashin.

Daga ƙarshe Ƙungiyar tana Addu’a tare da rokon Ubangiji ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa a yankin mu na Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya. Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button