ABITRAGE TSAKANIN KASUWANNI BIYU (ABITRAGE BETWEEN TWO EXCHANGES)

 ABITRAGE TSAKANIN KASUWANNI BIYU (ABITRAGE BETWEEN TWO EXCHANGES)


MA’ANAR ABITRAGE TRADING:-

ABITRAGE TRADING a takaicen takaitawa ba tare da dogon bayani ba muna iya bashi ma’anar “Siyan wani abu cikin farashi mai sauki da kuma siyar da shi cikin farashi mai tsada nan take ba tare da daukan dogon lokaci ba”


ABITRAGE TRADING kala-kala ne wanda a takaice a yanzu shafin www.nasara.com.ng zai yi bayanin guda daya daga ciki kafin zuwa wani lokaci sai mu yi bayani sauran,

Mun za6i mu yi bayani akan ABITRAGE TSAKANIN KASUWANNI BIYU (ABITRAGE BETWEEN TWO EXCHANGES) saboda shine yafi sauqi sannan yafi sauqin samuwa da aiwatarwa.

Shi wannan ABITRAGE din ana yinsa ne tsakanin kasuwanni guda biyu na Crypto Currency, Misali tsakanin BINANCE EXCHANGE  da KUCOIN EXCHANGE,

Za ka duba kasuwar (EXCHANGE) da take da COIN ko TOKEN mai sauqin farashi sai ka siyeshi daga nan sai kayi kaishi kasuwar (EXCHANGE) da farashin COIN ko TOKEN din yake da tsada ka siyar.

Misali:- A kasuwar BINANCE farashin TRON (TRX) N50, amma kuma a kasuwar KUCOIN N55, anan za ka siyeshi daga kasuwar BINANCE sai ka kai shi kasuwar KUCOIN ka siyar da shi,

Wanda hakan ya ke nuna banabancin N5 akan kowanne TRON qwaya daya tsakanin kasuwar BINANCE da KUCOIN, kuma hakan yana nufin za ka ci ribar N5 akan kowanne TRON, ribar N5K akan TRON guda 1000, wanda N50,000 ce zata siya maka TRON guda dubu,

Hakan kuma yana nufin akan dukkan N50,000 kana da ribar 5k, wanda daga siyan zuwa siyarwar ba zai daukeka sama da mintuna 10 ba, wanda ka ga kenan cikin qasa da awa 1 N50k dinka zata koma N80K. 

Wannan kalar ABITRAGE shine kusan mafi sauqi kuma mafi bada riba matuqar mutum ya samu damar hakan.


ABUBUWAN DA DOLE SAI KA KULA DA SU KAFIN FARA ABITRAGE TSAKANIN KASUWANNI BIYU 

  • TOKEN/COIN:- Dole kafin ka fara yin wannan kalar ABITRAGE din sai ka nemo COIN ko TOKEN din da yake da banbancin farashi tsakanin kasuwanni biyu, akwai hanyoyin da ake bi wajen gano irin wadannan coin ko token din wanda shafin www.nasara.com.ng zai yi bayaninsu nan gaba.
  • KASUWANNI (EXCHANGEs):- Bayan ka gano coin ko token, abu na gaba dole ka san kasuwar da take da farashi mai sauqi da kuma wadda take da farashi mai tsada, a wannan gabar dole ka tabbata kasuwannin da za kayi amfani da su kasuwanni ne sanannu wanda ba su yi qaurin suna wajen ba wa masu amfani da su matsala ba, domin gudun kar ka saka kudinka a kasuwar da take da matsala kudinka ya maqale. 
  • BLOCK CHAIN:- Abu na gaba shine dole ka san coin ko token din da za kayi ABITRAGE TRADING da shi akan wanne BLOCK CHAIN ya ke, domin akwai BLOCK CHAIN din da suke da tsadar GAS FEE ma’ana tsadar kudin caji na withdraw/transfer na coin ko TOKEN daga wata kasuwa zuwa wata kasuwa, BLOCK CHAIN mafi tsadar GAS FEE shine ETHERIUM BLOCK CHAIN, idan ka ga token ko coin din da za kayi ABITRAGE TRADING yana kan ETHERIUM BLOCK CHAIN to ka haqura da shi, sai dai idan ka lissafa ka ga akwai riba bayan an ciri GAS FEE, Nan gaba kadan zanyi bayanin yadda za ka lissafa ribar da zaka samu ko faduwa bayan an cire GAS FEE, amma akwai token ko coin da suke kan BLOCK CHAIN mai sauqin GAS FEE wanda shafin www.nasara.com.ng zai kawo wadannan BLOCK CHAIN Masu sauqin GAS FEE, haka akwai kasuwanni Masu tsadar GAS FEE akwai kuma masu sauqin GAS FEE suma InshaAllahu zamu kawo su.
  • CAJIN WITHDRAW (GAS FEE) :- Duk da  mun dan haska wani abu game da GAS  FEE wato cajin da akeyi lokacin da za ka cire wani coin ko token daga wata kasuwar zuwa wata, Dole a duk lokacin da ka samu damar wannan abitarage din ka lura da GAS FEE, ma’ana ka san nawa ne za cajeka a matsayin kudin withdrawal, sanin hakan zai qara haska maka shin za ka samu riba cikin wannan ABITRAGE din da za kayi, Za mu kawo bayani cikin lissafi dalla-dalla kan yadda za ka lissafa kudin GAS FEE da kuma meye zai rage maka a matsayin riba bayan ka cire GAS FEE. 
  • RIBA (PROFIT/GAIN):- Dole ne ka san yawan ribar da za ka samu kafin ka fara ABITRAGE, hakan kuma yana da buqatar ka yi lissafi, shima za mu kawo yadda za ka lissafa riba ko akasinta nan gaba. 
  • DAMAR WITHDRAW:- Duk lokacin da ka samu damar yin wannan ABITRAGE din dole ne sai ka lura da kasuwar da ka ga coin ko token yana da farashi mai sauqi shin ana iya cirewa (withdrawal) na wannan coin ko token din da kake son yin ABITRAGE zuwa wata kasuwar, domin a duk lokacin da masu kasuwar da coin ko token ya ke da farashi mai sauqi wanda ya sa6awa sauran kasuwanni su ka lura da cewa farashi coin ko token a kasuwarsu ya sa6awa sauran kasuwanni to suna rufe WITHDRAW, sabo da haka dole ka lura da wannan ga6a tana da matuqar muhimmanci domin matuqar an rufe withdraw to babu damar cire wannan coin ko token zuwa wata kasuwar wanda haka yana nufin babu damar yin ABITRAGE. 
  • DAMAR DEPOSIT:- Dole ne ka lura da kasuwar da coin ko token din yake da tsada ma’ana kasuwar da za ka kai coin ko token ka siyar acan, dole ka tabbata akwai damar yin deposit ma’ana damar turo wannan coin ko token din da kake son yin ABITRAGE da shi cikin kasuwar da za ka siyar, domin a duk lokacin da masu kasuwar da suka lura cewa farashin coin ko token a kasuwarsu ya fi na sauran kasuwanni tsada suna rufe damar Deposit, sabo da haka dole ka bincika kafin ka turo coin ko token, idan ba haka ba kudinka zai iya maqalewa, ya fito daga kasuwar da ka cireshi (withdraw) amma bai iso kasuwar da ka turoshi ba (deposit) wanda ko ba kayi asara ba zai dauki matuqar lokaci kafin ya shigo, tana iya yiwuwa ma sai farashin kasuwar ya daidaita da na sauran kasuwanni.

Yadda Ake Lissafa Gas Fee, Riba, Da Matakan Da Ake Bi Lokacin Da Aka Samu Damar ABITRAGE Tsakanin Kasuwannin Biyu

Cikin wannan rubutun shafin www.nasara.com.ng zai yi bayanin yadda za ka gane shin akwai riba ko faduwa cikin damar ABITRAGE da ka samu tsakanin kasuwanni biyu da kuma yadda za ka lissafa Kudin withdraw wato Gas Fee da matakan da za ka bi kafin farawa, 

Misali:- Ka gano cewa TRON yana da banbancin farashi tsakanin kasuwanni biyu (Tsakanin kasuwar KUCOIN da BINANCE),

Ka gano cewa Farashin TRON ya fi tsada a KUCOIN ya yin da yake da farashi mai sauqi a BINANCE,

Hakan yana nufin za ka sayi TRON daga kasuwar BINANCE sannan ka turashi kasuwar KUCOIN ka siyar da shi,

Cikin Misali da muke bayarwa, mu dauka farashin TRON a kasuwar da yake da sauqin farashi N50 ne, a kasuwar da yake da tsada N55 ne, banabancin farashi na N5 ko kuma ribar N5 akan duk TRON daya,

Kai kuma kudin da kake da shi wanda zakayi wannan ABITRAGE din N20,000 (Kusan Dala 35 [$35] ),

Saboda haka sai ka shiga cikin calculator ka ce N20,000 a rabata gida 50 zai baka 400, (20,000÷50=400),

Abin da ka lissafa anan shine kana so ka san yawan adadin TRON da kudinka zai iya siya maka, domin sanin adadin yana da alaqa da ribar da za ka samu, kuma za ka san adadin ne ta hanyar raba adadin kudinka da farashin TRON na kasuwar da yafi sauqi kamar yadda mukayi a sama, 

Yanzu kasan cewa kudinka N20,000 zai siya maka adadin TRON guda 400,

Abu na gaba shine ka san nawa ce RIBA/PROFIT da za ka samu, 

Shima za ka shiga cikin calculator, sai ka lissafa banabancin farashin TRON da ke tsakanin kasuwannin guda biyu sau adadin yawan TRON da kudinka zai siya maka idan ba a manta ba a sama mun gano cewa banbancin farashin N5 ne, sannan adadin yawan TRON da kudinka zai siya maka guda 400, 

Saboda haka sai ka ce Banbancin farashin TRON da ke tsakanin kasuwanni biyu sau adadin yawan TRON da kudinka zai siya maka, 

Wato ( 5 × 400 = 2,000 ), N2,000 itace amsar mu kuma itace ribar da za ka samu a duk TRON guda 400 da ka siya daga Binance ka tura KUCOIN ka siyar, idan ka yi haka sau biyu ribarka ta zama N4,000, ya danganta sau nawa ka yi, 

Abu na gaba cikin misalin da mu ke bayarwa shine dole ka san nawane Cajin da za a maka yayin da za ka tura TRON daga kasuwar da yake da sauqin farashi zuwa kasuwar da ya ke da tsada,

Za ka san haka ne ta hanyar zuwa ka shiga WITHDRAW na TRON a BINANCE ka ga TRON nawa suke dauka a matsayin GAS FEE, 

Wanda yawanci mun sani cewa TRON qwaya daya suke dauka,

Wanda hakan yana nufin GAS FEE din da za cajeka N50,

Saboda haka sai ka cire N50 daga cikin ribar da zaka samu ta N2,000, wanda abin da zai rage shine N1,950,

Bayan sanin GAS FEE na WITHDRAW, da abin da zai rage maka a matsayin riba bayan cire GAS FEE din,

Dole ka san GAS FEE na dawo da kudinka daga KUCOIN zuwa BINANCE, 

Domin bayan ka siyar da TRON a kasuwar KUCOIN dole ka maido shi kasuwar BINANCE domin ka sake siya ka sake turashi KUCOIN ka siyar da shi domin samun wata ribar, 

Shima za ka gani hakan ne ta shiga withdraw na coin ko token din da zaka siya ka dawo da shi Binance ka ga nawa ne  GAS FEE dinsa,

Idan USDT ne, Yawanci GAS FEE na WITHDRAW ana daukan 1USDT ne idan akan TRC20 Block chain ne, 

Saboda haka sai ka cire 1USDT daga cikin ribar da za ka samu abin da ya rage shine ainishin ribarka a duk ABITRAGE qwaya daya da zakayi. 

A lura wannan shafin www.nasara.com.ng ya bada shi ne a matsayin misali, amma kuma hanyar da muka bi muka ita lissafa komai da komai da matakan da muka bi kaima su za ka bi a duk lokacin da zakayi ABITRAGE akan kowanne irin coin ne ko token.

Wannan shine takaitaccen bayani akan ABITRAGE TSAKANIN KASUWANNI BIYU (ABITRAGE BETWEEN TWO EXCHANGES),

Rubutu na gaba da zamuyi shine “HANYOYIN DA AKE BI DOMIN SAMUN ABITRAGE TSAKANIN KASUWANNI BIYU”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button