Abubuwa 3 Da Duk Đan-Crypto Yake Buqata
Abubuwa 3 Da Duk Đan-Crypto Yake Buqata
Matuqar kana son rabauta da kwanciyar hankali a harkar kasuwancin crypto currency dole ka samu guzurin wađannan abubuwa gida uku masu muhimmanci.
1. ILIMI :- ILIMI cikin kasuwancin crypto currency dole ne, domin duk wani abu na rayuwa ba iya kasuwacin Crypto ba dole ka nemi iliminsa matuqar ka na so ka yi nasara, a matsayinka na musulmi hatta Annabin da Allah SWT ya turo mana farkon wahayin da aka masa shine yayi karatu, shiyasa tsawon rayuwarsa Allah SWT ya yi ta masa wahayi a matsayin ilimin da zai amfani da shi wajen isar da saqon Allah SWT,
Kasuwancin crypto kasuwancine da yake tafiya bisa doron ilimi da zamani matuqar ka ce Za ka shige shi bisa jahilci to Tabbas a qarshe za ka tafka asarar da baka ta6a yinta ba a rayuwarka.
Saye da sayarwa cikin kasuwancin crypto yana da alaqa da ilimi, Wanda hakan yana nufin rashin ilimi zai sa ka saya a lokacin da yakamata ka sayar ko kuma ka sayar a lokacin da yakamata a saya.
Hatta token din da ya kamata ka saya ilimine zai maka jagoranci, domin wani token ko coin din kana saya sunanka sorry domin da shi da bola duk đaya ne,
Akwai abubuwa ba adadi cikin kasuwancin Crypto da dole sai da ILIMI zaka yi su, yin su ba tare da ilimi daidai yake da sayan asara da kudinka,
Akwai makarantu da yawa na online da offline wanda ya kamata ka shiga zasu koyar da kai duk wani abu da kake buqata a harkar kasuwancin crypto, ina ga ba laifi ba ne don ka ware N15,000 daga cikin jarin N100,000 ka shiga makaranta an koya maka yadda za ka juya sauran N85,000 ta koma Miliyoyin kuđađe,
Sannan Akwai YouTube channel da website da zaka iya bibiya domin samun ilimin wannan kasuwancin na Crypto.
2. JARIN DA BA KA DA BUQATARSA A LOKACI NA KUSA :- Da yawa suna đaukan kudin da rayuwarsu ta yau da gobe ta dogarashi su zuba a cikin kasuwancin crypto currency, Wanda hakan garaje ne da rashin azanci, domin shi kasuwancin Crypto ba kamar yadda mutane suke đaukansa bane, da yawa suna đaukan cewa yau idan ka fara yau za ka samu maqudan kuđađe sai ka ga mutum ya dauki kudinsa na buqata ya zuba, wani ma bashi yake ci wani kuma kudin ajiya da aka bashi ya ke zubawa duk da sunan cewa cikin lokacin qanqani zai samu riba sai ya maida kudin da ya nema bashi ko ya ara, amma kuma yana zuba kudin sai ka ga kasuwar ta bashi mamaki a maimakon riba sai dai ya lissafa fađuwa, wanda kuma zai iya daukan lokaci kafin kudinsa su dawo, ka ga kenan kana buqatar kudin da yake naka ne mallakin kane sannan ba ka da buqata akansa yadda ko da kasuwa ta yi qasa da kai to za ka iya jira har lokacin da kudinka za su dawo kai har ma da riba matuqar ka sayi token mai inganci,
A takaice dai shi kasuwancin Crypto ana shigansa da kudin da yake mallakin kane sannan ba ka da buqata akansa anan kusa.
3. HAQURI:- Shine kishiyar gaggawa, kasuwancin Crypto yana da buqatar matuqar haquri, kai duk wani kasuwanci yana buqatar haquri kafin nasara ta zo, ko kasuwancin Sata yana buqatar haquri, nature yana cewa “Rome wasn’t built in a day”,
Babban abin da ya ke illata sabbin masu kasuwancin Crypto shine rashin haquri, za ka ga mutum ya shiga da sunan yau ko gobe yake son samun maqudan kuđađe, ko kuma ka ga mutum ya sayi token ya bashi fađuwa a maimakon ya jira token din ya tashi ya maida masa kudinsa har ma da riba sai ka ga mutum ya sayar da fađuwar ya kuma zuwa ya sayi wani token din shima da ya bashi faduwa sai ya qara zuwa kan wani haka zai yi ta yi har kudinsa su qare, idan da ace yayi haquri a token na farko da ya bashi fađuwa da ya dawo masa kudinsa har da riba,
Dole duk wanda zai shiga kasuwancin Crypto ya shiga da cewa ba ya shigo bane don yau ko gobe ko nan da wata đaya ne yayi kudi ba, a’ah ya shigo ne nan da wani lokaci a kusa ko a nesa, kuma dole sai ka ladaftar da kan ka akan haqurin domin ba zaka iya zama mai haquri a rana daya ba matuqar ka saba da tashi daga kan token din da ya baka faduwa zuwa wani, daga cikin abbuwan da za su taimaka maka ka zama mai haquri shine ka rage yawan leqa cikin wallet dinka ko exchange, ka tabbata kudin da ka zuba ba ka buqatarsa anan kusa, ka rage gaggawa da ci da zuci, ka samu wani abin da zai ke dauke maka hankali har ma ka manta ka na kasuwancin crypto da sauransu.
Wadannan ba iya su bane kake buqata a matsayinka na sabo a kasuwancin crypto ba, akwai wasu abubuwa masu yawa wanda bincikenka da kuma daukan kasuwancin da muhimmanci zai sa ka gano so anan gaba, Allah ya shige mana gaba.