Ali Nuhu ya mayar da martani a kan Rigimar da ke faruwa

Ali Nuhu ya mayar da martani a kan Rigimar da ke faruwa
Maza ku ga ne…….
Yanayin sha’awar mace da na namiji akwai banbanci.
Ku maza sha’awa da so abubuwa biyu ne da kuke iya banbancewa, shiyasa ko da bakwa son mace zaku iya saduwa da ita har ku samu yadda kuke so. Shiyasa kuke iya biyan mace kudi dan ku biya buqatar ku ko da kuwa bakusanta ba.
Shiyasa zaku iya kuna fushi da mace ko kuna fada da iyalin ku bazai hana ku biyo dare da buqatar kuba dan ita sha’awar ku da abunda ke zuciyar ku basa haduwa.
Ita kuma mace………
Sha’awarta yana tafiya da son da takema mutum ne, natsuwarta da kai a zuciyarta gwargwadon jin dadin da zaka samu a kan shimfida. Shiyasa yakanyi matuqar wuya mace in bata son mutum ta kusance shi, asalima kyamar sa takeyi komin tsabtar sa.
Shiyasa ko fushi tayi da miji zata iya qaurace masa, balle in kuna da matsaloli tsakanin ku da baku magance shi ba zaiyi matuqar wuya kaji dadinta a shimfida, wasu shiyasa suke baku hakkin ku amma zuciyar su ya qaurace muku.
Shiyasa ku da zaka kusanceta cikin jin dadi ta amince, wani abu qalilan zakayi, ko ka taba wani wajen da bata so ya kawar mata da sha’awarta wata har ta iya hakurin ayi domin ita zuciyarta yana da alaqa da sha’awarta.
Shiyasa mafi sauqin abunda mace zatayi in tana sonka shine ta nemi kusantarka misali riqe hannu, hugging, kiss da sauransu cikin sauqi da aminci.
Matuqar kuna son ku ji dadin mu’amalantar iyalanku a shimfida sai kun fahimci yanayin zuciya, jiki da sha’awar mace da inda sukayi tarayya.
Wannan zai baku damar juyasu da samun su yadda kuke so, wadda ita da kanta zatana buqatarka ko guiding dinka cikin sauqi yadda take so.
✍️ Fatimah Chikaire
Rayuwar Bazawara Na Cikin Hatsari
Babu abinda yafi mutuwar aure musiba da tashin hankali a rayuwar aure.
Duk lokacin da naga bazawara hankali na kan tashi saboda tashigo wata sabuwar rayuwa wacce bata saba da ita ba. Babbar musifar da bazawara zata fara fuskanta itace ɓullowar samari da zawarawa kamar ruwa, wanda kaso casa’in cikin ɗari ba don Allah suke sonta ba.
Da yawan su suna zuwa ne domin su tattaɓa jikin ta ko kuma suyi zina da ita domin biyan buƙatarsu, saboda su a tunanin su ai ta saba da kwanciyar aure yanzu kuma gashi ta rasa wannan damar.
A wannan lokacin ne za tayi ta cin karo da mazajen bariki tare da samarin zamani suna yi mata kyauta tare da bata kulawa kamar gaske daga nan kuma sai su hure mata kunne a shiga wani sabon babin na daban.
Allah ne kaɗai yasan adadin zawarawan da suka afkawa zinace-zinace tare da yawon bariki sakamakon yaudarar ƴaƴa maza. Da zarar ance ga bazawara nan to a wannan lokacin za kayi ta ganin gantalallun mazaje da mayaudaran samari kowa yana kai caffar sa wurin ta domin neman sa’a.
Da yawan zawarawa hankalin su kan gushe, karasa inda tunanin wasu ya tafi da wayonsu, saboda yadda shedan ke saurin yi musu huɗuba su karɓa.
Yakamata ƴan uwa na maza muji tsoron Allah saboda munfi matan laifi, sannan mu tuna da cewar zawarcin nan ƙaddarace zata iya faɗawa kan kowa, wasu mazajensu ke mutuwa wasu kuma ƙaddarar aure ce idan tazo sai an rabu.
Idan ka dauwama a lalata rayuwar zawarawa to yakamata kasani kaima fa kana da mata ko ƴa ko uwa ko ƙanwa kuma babu wacce bazata iya samun kanta a zawarci ba, kuma wallahi duk abinda ka yiwa ƴar wani ko uwar wani kaima sai an yiwa naka.
Mu tausayawa zawarawan nan mu basu kulawa ta musamman muma sai Ubangiji ya bamu kulawarsa, dukkan inda ƴa mace take komai ƙanƙantar ta uwace mu girmamata mu ɗora su akan madaidaitacciyar hanya, kada mu saka su kan hanyar da rayuwar su zata watse.
Muna roƙon Ubangiji ka kawowa zawarawa ɗauki, ka basu mazajen aure nagari ka tsaresu daga sharrin mazajen zamani