Allah yayaiwa matashiya mai haddar Al’Qurani Rasuwa

Allah yayaiwa matashiya mai haddar Al’Qurani Rasuwa
An hori malamai da su daina fassara alkur’ani mai tsarki ba tare da samun ilimin tafsiri ba
Daga Saadu Ukasha
An hori dukkanin malaman tafsiri da za su fassara Alkur’ani mai tsarki da su yi amfani da tafsiran da magabata suka yi amfani da shi ko kuma su tabbatar da samun ilimin fari na ilimin addini goma sha bakwai.
Shugaban majalisar Malamai na jihar Kebbi kuma malamin da ke jagorantar tafisrin Alkur’ani mai tsarki na watan Ramadan a hedikwatan Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamattis Sunnah, wadda As-sheikh Isma’ila Idris Ibn Zakariya ya assasa reshen jihar Neja, Ash-sheikh Abdurrahman Isah Jega ne ya yi kiran lokacin gabatar tafsirin.
Shehin malamin, ya cigaba da cewar tsoron kar malamai su rika fassara alkur’ani ba daidai ba, ya sa aka ga dacewar yin amfanin da tafsiran da aka amince da su bisa fahimtar mutane na kwarai. “Wajibi ne al’ummar musulmi su yi karatu kuma su yi aiki da abinda suka karanta, don haka dole ne malamai su kiyaye wajen fassara ayoyin alkur’ani domin kauce wa fasaara ba daidai ba.
Da ya juya wajen hidimar azumi kuwa, malamin ya yi tsokaci ne a kan muhimmancin ciyarwa don neman yardar Allah, domin bushara ce ta farin ciki a gidan aljanna.
“Don haka muna jawo hankalin al’ummar Musulmi dangane da yawaita aikata ayyukan alheri domin samun kusanci ga Allah SWT, musamnan a kan marasa karfi da mabukata.
Sheikh Jega, ya yi karin haske a kan illar munafunci ga Musulmi, domin bai da makoma mai kyau ranar alkiyama. Wajibi ne mu yi aiki da abinda manzon Allah ya zo da shi daga Allah SWT, duk musulmin da bai tsayu bisa kafafuwansa ba ya zama mai fuska biyu a addinin musulunci, tabbas wannan ya tabe domin bai da makoma na gari gobe kiyama.” Mal. Jega ya nanata.
Ya kara da cewar wajibi ne duk abinda Manzon Allah ya ce, mu rike shi hannu bi-biyu ba tare da inkari ko tsoro ba wajen aiwatar da shi, saboda muna kallo a kasar nan an hana sallah saboda tsoron Korona, an hana karatun Alkur’ani mai tsarki saboda tsoron Korona, tabbas wadanda aka hana sun hanu amma wadanda suka yi riko da igiyar Allah sun ci nasara.
Ya zama wajibi, shugabanni su ji tsoron Allah, su daina yi wa addini musulunci zagon kasa, domin fuska biyu wa addini ba zai haifar masu da da mai ido ba.
Al’ummar Musulmi kar su zama masu fuska biyu wa addini, domin yin hakan alama ce ta munafunci ga addini musamman wajen rashin yin aiki da koyarwar Manzon Allah SAW yadda Allah ya aiko shi ga musulmi domin kusantar da su ga Allah SWT da samun makoma na kwarai ranar alkiyama.
JIBWIS NHQ JOS