Allahu Albar Kalli Cikakken Bidiyon yadda Akai Jana’izar Jarumin Kannywood Awarwasa

Allahu Albar Kalli Cikakken Bidiyon yadda Akai Jana’izar Jarumin Kannywood Awarwasa
ALLAHU AKBAR RAYUWA
Na saurari bayani mai ratsa zuciya da tsoratarwa game da rayuwa daga bakin Attajirin mai kudi Alhaji Aminu Dantata
Wasu ne suka kai masa ziyara gidansa jiya a Kano bayan ya cika shekaru 92 a duniya, a jawabin da yayi yace duk sa’anninsa a Nigeria wadanda ya sani suka taso tare sun mutu, da kyar ne idan mutane 10 da ya sani suna raye
Yace yana neman yafiyar kowa, kuma duk wanda ya bata masa ya yafe, yace shi yanzu baya jin dadin rayuwar duniya, fatan mutuwa yakeyi ya cika da imani, da bakinsa ya fadi haka, Jama’a wannan babban darasi ne na rayuwa
Alhaji Aminu Dantata attajirin mai kudi ne wanda idan aka tashi lissafa masu kudi a Nigeria dole sai an sanya sunansa, ga kudin ga komai na rayuwa Allah Ya bashi, amma tsufa ya sa ya dena jin dadin rayuwar duniya, yanzu mutuwa da imani kawai yake fata
Ga misali da Sarauniyar Ingila Elizabeth, duk abinda take bukata a duniya Allah Ya bata, karshe ta kwanta ta mutu ba tare da jinya ba, kwararrun Likitocin Ingila sukace tsufa ne yayi ajalin rayuwarta
To haka fa rayuwar take, idan ka bi Allah Ka zama mutumin kirki idan baka mutu ba dole zaka tsufa, zaka kai matakin da ka dena jin dadin rayuwar duniyar, harcenka ya dena jiye maka dandanon dadin abinci, Kwankwasonka ya gaji balle ka iya sarrafa mace, haka ita ma mace tsufa zai sa ta dena jin sha’awar namiji da komai na rayuwa, ko da tayi tsirara wani namiji ba zai ji sha’awarta ba
Haka duk wanda ya zama dan iska ko ta zama ‘yar iska, bata jin magana, ta sa iskanci da karuwanci a gaba, gani take ba zata tsufa ba, to dole sai tsufa yazo ko ba’a mutu ba, kuma karshe dole a mutu, kuma gashi tsufan mutanen banza da na ‘yan iska yafi muni, domin suna koma wa yin kashi da fitsari a kwance su rasa masu wanke musu
Babban ribar da mutum zai samu a rayuwa da bayan mutuwa shine bin Allah tare da karfafa zuciya wajen dauriya da hakuri akan kiyaye dokokin Allah, ko da tsufa yazo to za’ayi tsufan alheri da rufin asiri
Muna rokon Allah Ya mana muwafaka duniya da lahira, Ya sa mu gama da duniya lafiya da imani