Authenticator Da Ake Iya Dawo Da Account Bayan An Rasashi
Authenticator Da Ake Iya Dawo Da Account Bayan An Canja Waya Ko Anyi Restore
Da yawa cikin masu amfani da kasuwannin Crypto Currency suna saka Authenticator a cikin EXCHANGE ko WALLET dinsu domin inganta tsaro da bada kariya ta musamman ga dukiyarsu,
Sai dai shi Authenticator da muke amfani da shi na kamfanin Google wato Google Authenticator yana da wani hatsari ko illa ko tashin hankali guda daya, wanda yau muna tafe da maganinsa,
Illar da Google Authenticator ya ke da ita shine idan ka yi activating dinsa a wata EXCHANGE ko WALLET dinka amma dalilin sace wayarka ko restore ko kuma canja wayar to za ka iya rasa wannan Authenticator account na wannan exchange ko wallet din,
Rasa Authenticator account na wallet ko exchange kamar rasa dukiyar da take cikin wannan exchange ko wallet din ne,
Domin wani Authenticator account din idan ka rasa shi shikenan har abada ka rasa ba zai dawowa ba, wani kuma zai dawo amma sai da ji6in goshi, domin sai ka tinti6i Customer Care Service na wannan exchange din,
SHIGA NAN ka karanta yadda ake dawo da Authenticator Account na HOTBIT EXCHANGE
Bayan Google Authenticator akwai sauran Authenticators masu inganci a Playstore,
Cikinsu yau shafin www.nasara.com.ng ya zo da wani Authenticator wanda ake iya dawo da Authenticator Account cikin qasa da minti daya ko wani abu mai kama da haka bayan an canja waya,
Duk da cewa Google Authenticator shine ya shahara a wajenmu bayan shi akwai wani Authenticator din wanda yafi Google Authenticator features,
Domin shi kana iya dawo da Authenticator Account dinka ko da an sace maka wayarka ko ka yi restore dinta ko kuma ka canja wayar,
Sai dai shi wannan Authenticator din yana da wasu abubuwa da dole sai ka kiyaye su lokacin da kake rijista da shi,
Shafin www.nasara.com.ng yayi cikakken bayani akan wannan Authenticator din.
Abubuwan Da Za Ka Tanada Kuma Ka Kiyaye Lokacin Da Za Kayi Rijista Da Wannan Authenticator Din
Na san mai karatu zai so shafin www.nasara.com.ng ya sanar da shi sunan wannan Authenticator din, amma akwai abubuwa masu muhimmanci da shafin www.nasara.com.ng yake so ya kawo maka bayaninsu domin suna da alaqa da dawo da shi wannan Authenticator Account din bayan ka rasashi, haka kuma suna da alaqa da yadda zakayi rijista,
Amma duk da haka Sunan wannan Authenticator din AUTHY AUTHENTICATOR, yana cikin Playstore, kana iya saukeshi,
Ga abubuwan da za ka kiyaye kuma ka tanada domin yin rijista da wannan Authenticator din da kuma yadda za kayi rijista da shi:-
- Abu na farko lambar wayarka ta ainishi wadda kake amfani da ita, domin da itane ake dawo da wannan Authenticator Account din bayan an rasashi saboda verification code da suke turowa.
- Ka tabbata idan ka sake waya wannan Lambar da ka yi rijista da, ita kayi amfani wajen shiga AUTHY AUTHENTICATOR.
- Abu na biyu dole ka tanadi adireshin email wato email address.
- Wadannan sune farkon abubuwan da ake buqata domin fara yin rijista.
- Bayan ka tanadesu sai ka sauke AUTHY AUTHENTICATOR ka shiga cikinsa, ka shigar da lambar waya da adireshin email za su baka za6i ta wacce hanya kake so a turoma da verification code, ko ta hanyar SMS ko whatsapp ko ta kira.
- Bayan sun turo maka code kayi verifying, zai kai ka zuwa ga shafi na gaba wanda anan ne zai buqaci ka yi adding na Authenticator account da kake so ka shigar.
- A shafin za su ce maka ka ta6a alamar tarawa wato ➕ domin shigar da account.
- Sai ka bi irin hanyar da kake bi domin sakawa wallet ko exchange Authenticator,
- Zai buqaci ka shigar da Private Key wanda shine ake daukowa daga cikin exchange ko wallet din da kake son sakawa Authenticator.
- Bayan ka dauko su ka shigar sai ka danna CONTINUE, zai kaika wani shafi, a saman shafin an rubuta BACKUPS PASSWORD.
- A wannan shafin ne zaka shigar da PASSWORD da za ka dawo da Authenticator Account dinka bayan ka rasashi, sai ka shigar da Password ka qara maimaita ta, sai ka danna ENABLES BACKUPS, ka tabbata Password din da ka shigar ka kiyaye ta.
- Bayan ka danna ENABLES BACKUPS zai kai ka zuwa ga wani shafi, a saman shafin za ka ga wajen searching an rubuta “Search Logo By App”, abin da hakan yake nufi shine wai ka yi searching din alamar exchange ko wallet ko App din da kake so ka saka masa Authenticator, idan BINANCE ce sai ka rubuta BINANCE sai ka danna Search za ka ga Logo na BINANCE ya bayyana sai ka dannan CONTINUE, idan ba ka samu LOGO da kake nema ba akwai wani hoton mukulli sai ka ta6ashi sai ka danna CONTINUE.
- Bayan ka danna CONTINUE zai kai ka shafin da za ka shigar da sunan App din da kake so ka sakawa Authenticator, sai ka rubuta HOTBIT idan itace, za kaga a saman shafin an rubuta Account Nickname.
- Bayan ka rubuta Account Nickname sai ka danna SAVE, kana danna SAVE shikenan ka gama shigar da wannan Authenticator Account din, za ka ga ya kawoka shafin da za kaga AUTHENTICATION CODE sannan ga lokaci yana reading.
- A gefen lambobin wato Authentication Code za kaga wata alama kamar ta littafi ita za ka ta6a duk lokacin da za kayi copy na Authentication Code.
- Idan kuma za ka qara wani Authenticator Account na wani exchange ko wallet ko wani App din, Idan ka duba daga sama gefen dama akwai wasu digo ( ⠇) guda uku a jere su zaka ta6a, za kaga Add Account sai ka ta6ashi.
- Bayan ka ta6a zai kaika shafin da za ka shigar da Private Key/Setup Key.
- Sai ka bi irin hanyar da mukayi bayani a sama.
- Sai dai shi BACKUPS PASSWORD sau daya suke tambaya, shine a farkon fara amfani da AUTHY AUTHENTICATOR, amma kuma duk Account din da za ka yi adding dinsa bayan na farko ba za su tambayeka ba.
Yadda Za ka Dawo Da Authenticator Account Da Yake kan Authy Authenticator Bayan ka Canja Waya
Dawo da Authenticator Account a Authy Authenticator abu ne mai sauqi matuqa,
Matuqar BACKUPS PASSWORD dinka yana nan, yana da kyau ka kula da shi,
Kawai za ka sauke AUTHY AUTHENTICATOR a wayarka, sai ka shiga cikinsa,
Zai buqaci ka shigar da lambar wayarka da ka yi rijista da shi, bayan ka shigar zai turo maka da verification code ta hanyar SMS ko whatsapp ko kira,
Bayan ka shigar da verification code zai kai ka shafin da yake dauke da dukkan Authenticator account din da ka dora akan ita Authy Authenticator,
Amma kuma za ka ga alamun mukulli akansu, ma’ana sai ka budesu,
To ya za ka bude? Shafin www.nasara.com.ng zai maka cikakken bayani, biyomu a sannu.
Za ka ta6a daya daga cikin Account din, bayan ka ta6a zai kai shafin da za ka shigar da BACKUPS PASSWORD dinka, sai ka shigar da shi,
Bayan ka shigar da shi sai ka danna DECRYPT ACCOUNT, za kaga an rubuta maka YOUR ACCOUNTS HAVE BEEN DECRYTED, sannan za kaga an bude maka shafin da duk Authenticator Accounts dinka suke.
Idan Na Manta BACKUPS PASSWORD Dina ya Zanyi ?
Matuqar ka yi sake da BACKUPS PASSWORD dinka to anan matsalarka ta fi qarfin shafin www.nasara.com.ng a gaskiya, domin shikena ka rasa duk wani Authenticator Account da yake kan Authy Authenticator,
Shafin www.nasara.com.ng ya bibiyi Shafin Authy Authenticator domin binciko yadda ake dawo da BACKUPS PASSWORD sai dai abin da Authy Authenticator suka rubuta a shafinsu shine ba a dawo da Backup password bayan an manta ta.
Saboda haka ka tabbata lokacin da kake creating na BACKUPS PASSWORD ka za6i password wanda ba zaka manta ba, kuma duk sauqinsa ka tabbata ka rubuta a wani wajen da kake ajiye abubuwa masu amfani, Gargadi ne daga shafin www.nasara.com.ng zuwa gareka kai wanda za ka yi amfani da AUTHY AUTHENTICATOR.
Wannan shine cikakken bayani kan duk wani abu mai muhimmanci da ya shafi AUTHY AUTHENTICATOR wanda shafin www.nasara.com.ng ya binciko kuma yayi rubuta akansa.
Domin neman qarin bayani ko wata tambaya akan Authenticator ana iya mana magana ta hanyar saqon whatsapp a wannan Lambar 07035791120