Bankin Da Duk Dan Crypto Ya Kamata/Dole Yana Amfani Da Shi, ATM Card Kyauta Ne, Ba Transaction Ko Maitainance Charges, Ga Saurin Transaction

Bankin Da Duk Dan Crypto Ya Kamata/Dole Yana Amfani Da Shi, ATM Card Kyauta Ne, Ba Transaction Ko Maitainance Charges, Ga Saurin Transaction. 

Sanin duk wani dan Crypto ne cewa akwai bankuna da dama wanda ake amfani da su ta hanyar P2P a kasuwancin Crypto Currency, 

Harkar kasuwancin Crypto Currency tana da buqatar banki wanda yake da saurin transaction, wanda bashi da matsalar network, wanda yake da sauqin caji yayin transfer ko maitainance fee, 

Haka kasuwancin Crypto Currency a yanzu a qasar Nigeria masu kasuwancin Crypto suna da buqatar banki wanda yake ba zai cutar da su ba ta hanyar rufe musu asusun bankisu ba, saboda haramcin da babban bankin Nigeria wato CBN ya saka na hana bankuna mu’amala da kudaden Crypto Currency, 

Kusan duk wadannan abubuwan da na lissafo a sama akwai bankin da ya tattare su baki daya sannan akwai wasu abubuwa masu muhimmanci wanda za su sauqaqawa mai kasuwancin Crypto matuqar yana amfani da wannan bankin wanda ban anbacesu ba,

Kuma kana iya bude Asusu a wannan bankin a wayarka ta hannu cikin qanqanin lokaci da bai wuce mintuna 10 ba,

Wannan bankin hatta transaction fee ba ya dauka, ma’ana tura kudi daga asusunka na wannan bankin zuwa wani bankin kyauta ne, 

Idan ka yi rijista da wannan bankin hatta katin ATM Visa Card kyauta zai baka kuma har gida zai kawo maka shi ba tare da ficikarka tayi kuka ba, Kuma kana iya amfani da shi akan kowanne ATM da POS da wasu online transaction, 

Bank statement na wannan bankin kana iya cireshi nan take cikin sauqi idan har kana da buqata ko da kun samu matsala tsakanin kai da wanda ka turawa kudi ko ya turo maka, 

Shi wannan bankin hatta idan ka je zakayi P2P za ka siyar da USDT ko wani coin din matuqar kana amfani da wannan bankin to wanda za ka siyarwa zai turo maka ne ba tare da ya cire maka ko da sisin kobo ba, sa6anin idan kana amfani da wani bankin wanda ba shi ba, masu siyan USDT za su cajeka har N100 saboda bankinka ba wannan  bankin bane a matsayin transaction charge. 

Da yawa daga cikin Merchant na P2P suna amfani da wannan bankin saboda rashin caji da qarancin matsalarsa sa6anin sauran bankuna, 

Da wuya ka ga wani Merchant bashi da asusun banki a wannan bankin. 

Haka domin kiyaye kanka da dukiyarka ya kamata ka bude asusun ajiya a wannan bankin sai ya kasance shi kadai kake amfani da shi wajen hada-hadar kasuwancin Crypto, 

Saboda haka duk lokacin da za ka sayi USDT sai ka turo kudinka cikin wannan asusun banki sannan daga nan sai ka turawa Merchant din da kayi order a wajensa,

Haka idan har za a turo maka kudi daga P2P sai a turo maka zuwa ga asusun wannan bankin sannan sai ka turashi cikin ainishin asusunka na banki.

KUDA BANK Shine Bankin da muke bayani akansa, Banki ne na Online ma’ana Bankin da ake gudanar da shi akan yanar gizo sa6anin sauran bankuna na zahiri wanda suke da ofisoshi na zahiri. 

Babs Ogundeyi da Musty Mustapha ne suka kafa Bankin KUDA a shekarar 2019, KUDA BANK ya samu lasisi ne daga babban bankin Najeriya,

Bankin Kuda a yanzu yana da masu amfani da shi har sama da miliyan 1.4, karuwar kashi 124 cikin 100.

Yadda za ka Bude Asusun Ajiyar Kudi A KUDA BANK 

Bude asusun ajiya a kuda band abune mai matuqar sauqi sa6anin sauran bankuna na zahiri wanda dole sai ka tattaro wasu bayanai da takardu, 

Shi kuda BANK kawai za ka shiga cikin Rumbun Manhaja ne wato Playstore sai kayi searching na KUDA BANK MOBILE APP za ka ganshi sai ka saukeshi zuwa kan wayarka, 

Bayan ka saukeshi zuwa kan wayarka sai ka shiga cikinsa zai buqaci wasu takaitattun bayananka wanda mafi yawancin bankuna suke buqata kafin bude Asusun Ajiya.

Daga cikin bayanan da za ka buqata akwai:-

 1. Bvn Number
 2. Legal Name
 3. Email Address 
 4. Password 
 5. Gender 
 6. Date of Birth 
 7. Phone Number 
 8. State 
 9. LGA 
 10. City/Town 
 11. Address 
 12. Pin Number 
 13. Selfie 
 14. Identity Card

Matuqar ka tanadi wadannan bayanai to ka cancanta da ka fara amfani da KUDA BANK, abin da ya rage kawai garzaya Playstore domin sauke KUDA BANK MOBILE APP. Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button