BIDIYO: Masha Allah Ku Kalli Bidiyon Yadda Yan Banga Da Mutanen Gari Sukai Nasarar Kama Yan Fashin Daji.

 BIDIYO: Masha Allah Ku Kalli Bidiyon Yadda Yan Banga Da Mutanen Gari Sukai Nasarar Kama Yan Fashin Daji.

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu-Yanzu Na Cewa, ‘Yan Fashin Daji Sun Halaka Basarake Da Wasu Mutane 13 A Jihar Nejan Najeriya.

Kamar Yadda Zaku Kalli Bidiyon, Har yanzu dai ‘yan fashin daji na ci gaba da kai hare-hare da kisan jama’a a wasu yankuna na Jihar Nejan Najeriya, wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin kakar debe amfanin gona ke kawo jiki.

Gwamnatin Jihar Neja dai tayi Allah wadai da wannan mugun aiki, sakataren gwamnatin Jihar Nejan Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya ce sun tura karin jami’an tsaro a yankin, kuma ya zuwa yanzu hankali ya fara kwantawa a wajen.

Ita ma rundunar ‘yan sanda ta Jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Monday Bala Kuryas ya ce suna daukar mataki.

A yanzu dai akwai fargaba sosai musamman wajan debe amfanin gona a wadannan yankuna.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button