BIDIYO: Mutum 51 da suka mutu sakamakon wannan ambaliyar ruwa data faru a jahar jigawa danna nan

 BIDIYO: Mutum 51 da suka mutu sakamakon wannan ambaliyar ruwa data faru a jahar jigawa danna nan

AMBALIYAR RUWA A JAHAR JIGAWA AN CI ZARAFIN DAN JARIDA

Yadda Aka Min Dukan Mutuwa Ina Tsaka Da Daukan Rohoton Ambaliyar Ruwa A Garin Ganuwar Kuka Karamar hukumar Auyo Jahar Jigawa

Daga Abubakar Tahir 

Dayake lamarin Ambaliya ya kazanta a garin na Ganuwar Kuka inda cikin mintuna Sha biyar ruwa ya kusa gamawa da garin.

Haka tasa muka fara magana da abokanen aiki dake gidajen radio da jaridu kamar Bbchausa, Daily Trust, Humanangle, Liberty, JallaFm, Vanguard Hausa/Radio Raypower dss domin dauko abinda yake faruwa kai tsaye.

Bayan isa ta Garin na gabatar da ID Card dina na aiki inda wasu Matasa da nake ga sun waye suka biyo ni domin yin hirasa dasu.

Bayan na Dora musu Camera na fadi abun da suke da bukata sai na dan gusa kan domin cigaba da dauka.

Katsam sai naji an bugeni da karfi a kaina inda wayoyin dake hannuna kirar Infinix da Itel suka zuge cikin ruwa.

Dagowar da zanyi ashe naga wanne dalili sai naji an cigaba da dukana ta koina ana bugani cikin wani rafi da suke kira ruwan Makasa.

A haka sukayi ta dilmiya kaina suna dukana wasu suna cewa ku dake shi Nikwa inata kokarin nusar dasu ID card dina ina ce musu aiki nake.

A haka de wasu mutane suka yi maza suka hana su wanda daba dan an kawo min daukin ba da tuni sun kasheni tun da a take wasu sun zare wukake.

Haka aka ka ini Gidan Maigari ya bani Ruwa nayi wanka ya bani sabin Kaya na saka Inda ya bukaci na dawo na cigaba da aiki nace masa A’a.

Ya bada babura aka kawoni Hadejia inda a take na tafi babban asibitin Hadejia domin jinya.

Ya zuwa yanzu na dawo gida ina cigaba da karban magani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button