CIKAKKEN BAYANI AKAN YADDA AKE AMFANI DA COINGAPP WAJEN ABITRAGE TRADING TSAKANIN KASUWANNI BIYU
CIKAKKEN BAYANI AKAN YADDA AKE AMFANI DA COINGAPP WAJEN ABITRAGE TRADING
Kamar yadda mukayi cikakken bayani akan ABITRAGE TRADING, sannan cikin kalolin ABITRAGE mukai bayani akan yadda ake yin ABITRAGE TRADING tsakanin kasuwanni biyu,
Yau shafin www.nasara.com.ng zai yi bayani akan daya daga cikin hanyoyin da ake abi wajen nemo ABITRAGE TRADING tsakanin kasuwanni biyu,
Amma matuqar ba ka karanta cikakken bayanin da shafin www.nasara.com.ng yayi akan yadda ake ABITRAGE tsaknin kasuwanni biyu ba sai ka SHIGA NAN ka karanta,
Domin dole sai ka samu cikakkiyar fahimta akan matakan da ake bi wajen yin shi ABITRAGE tsakanin kasuwanni biyu kafin ka fahimci COINGAPP kuma ka iya amfani da ita.
SHIGA NAN ka karanta cikakken bayani akan Yadda Ake ABITRAGE TRADING Tsakanin Kasuwanni Biyu
COINGAPP
COINGAPP Manhaja ce da aka ginata domin ganowa da nuna banabancin farashin coin ko token a tsakanin kasuwanni biyu ko sama da haka,
COINGAPP tana nuna farashi mabanbanta na coin ko token a kasuwanni daban-daban,
Misali:-
Farashin BNB a kasuwar KUCOIN $630, amma kuma farashinsa a kasuwar OKEX $640 ne,
Yayin da ka shigo COINGAP za ta nuna maka cewa ga irin farashin BNB a wadannan mabanbanta kasuwanni,
Abin da ya rage sai ka yi amfani da cikakken ilimin da ka samu a rubutun da shafin www.nasara.com.ng yayi akan yadda ake ABITRAGE tsakanin kasuwanni biyu.
Akwai wasu alamu da manhajar COINGAPP yake nunawa akan kowanne coin ko token da yake da farashi daban-daban a kasuwanni,
Haka akwai wasu alamomi da ita wannan manhaja take nunawa akan kowacce kasuwa,
Duk mai son yayi ABITRAGE Tsakanin Kasuwanni biyu dole ya san wadannan alamomi ya kiyaye su kuma yana lura da su a duk lokacin da ya samu wani coin ko token da yake da banbancin farashi a kasuwanni.
Idan ba ka da manhajar COINGAPP kana iya samunta cikin rumbun manhajoji wato Playstore .
CIKAKKEN BAYANI AKAN ALAMOMIN COINGAPP
ALAMOMI NA DAYA :-
Cikin wannan hoto da ke sama akwai lambobi 1,2,3, Wanda kowacce lamba akwai rubutu a gefenta, 1. DIFFERENCE . 2. BUY FROM. 3. SELL AT.
Ga Bayaninsu Dalla-Dalla
1. DIFFERENCE :- Wannan yana nufin banbancin farashin coin ko token da ke tsakanin kasuwanni biyu, yana nuna banbancin ne a percentage.
2.BUY FROM :- Wannan yana nufin za ka siya da ga kasuwar da ta zo a qasan shine BUY FROM.
3. SELL AT:- Wannan yana nufin kasuwar da za kaje ka siyar da coin ko token da ka siya daga kasuwar da take qasan BUY FROM.
Saboda haka DIFFERENCE yana nufin banbancin coin da ke tsakanin kasuwanni biyu, BUY FROM yana nufin kasuwar da farashin coin yafi sauqi wadda kuma daga nan zaka sayi coin, sai kuma SELL AT yana nufin kasuwar da coin yafi tsada wanda anan za kaje ka siyar da coin din.
ALAMOMI NA BIYU:- sune wanda suke bayyana cikin kaloli (colors), gasunan cikin wannan hoton da ke qasa, sannan kuma sai bayanansu zai biyo baya.
Su wadannan alamomi suna bayyana ne a jikin COIN DIFFERENCE (Alama ta farko kenan da mukayi bayani a sama), bayyanarsu suna baka bayanan yanayin da kasuwar da za ka sayi coin ko ka sayar da shi,
Kala ta farko itace (Green Color) wannan kala bayyanarta a jikin coin yana sanar da kai cewa za ka iya yin ABITRAGE da wannan coin din tsakanin kasuwannin da suka bayyana a qarqashin BUY FROM da SELL AT, bayyanarta yana nufin withdrawal da deposit tsakanin kasuwannin biyu duka a bude suke, abin da ya rage shine kayi amfani da ilimin da ka koya a rubutunmu na ABITRAGE TRADING Tsakanin Kasuwanni Biyu.
Kala ta biyu itace (Yellow color), bayyanar wannan kala yana gaya maka cewa shi kansa wannan manhaja ta COINGAPP ba ta da masaniya akan shin yin ABITRAGE Tsakanin wadannan kasuwani akwai matsala ko babu, saboda haka yanzu kai ya kamata ka je ka duba me yake faruwa a cikin wannan kasuwanni.
Kala ta uku itace Jā (Red color), bayyanarta yana nufin akwai matsala a kasuwannin da zakayi ABITRAGE, Za ta iya yiwuwa kasuwar da coin din yafi sauqin farashin sun rufe withdrawal, ko kuma kasuwar da coin din yafi tsada sun rufe Deposit.
ALAMOMI NA UKU:- Sune suke cikin wannan hoto da ke qasa, su wadannan alamomi suna bayyana akan kasuwar da zaka sayi coin (BUY FROM) ko kuma kasuwar da zaka sayar da coin a cikinta (SELL AT).
Alama ta daya itace alamar mukulli 🔒 bayyanar wannan alama akan kasuwa yana nufin an rufe withdrawal ko deposit na wannan coin din a wannan kasuwar, saboda haka babu damar ABITRAGE.
Alama ta biyu itace alamar “Triangle” ⚠bayyanar wannan alama akan kasuwa yana nufin manhajar COINGAPP ba ta san shin akwai damar withdrawal/deposit ko babu, yanzu kai ya kamata ka je ka bincika wannan kasuwa ka ga shin akwai damar withdrawal/deposit ko babu.
Alama ta uku itace alamar screwdriver da spanner 🪛🔧bayyanar wannan alama akan kasuwa yana nufin wannan kasuwar suna cikin gyara wanda hakan yake nufin shima babu damar ABITRAGE domin za su rufe withdrawal/deposit yayin da suke gyara.
Abubuwa Masu Muhimmanci Cikin COINGAPP
A cikin wannan manhaja ta COINGAPP kana da damar daidaita wasu abubuwa wanda sune zamuyi bayaninsu yanzu.
Domin sanin wadannan Abubuwa masu muhimmanci, bayan ka shiga cikin manhajarka ta COINGAPP, daga sama gefen dama akwai wata alama mai layi uku jere, gatanan cikin hoto a qasa.
Ita zaka ta6a yayin da zata kawoka shafin da wadannan abubuwa masu muhimmanci da zamuyi bayaninsu suke.
1. TRADE MANAGEMENT sune alamomi na uku da mukayi bayani a sama, kana da damar kunna kowacce alama ko kuma kasheta, kunnata yana nufin zata bayyana duk lokacin da abin da take wakilta ya faru kasheta kuma yana nufin kishiya haka.
2. MARKET MANAGEMENT wannan yana wakiltar “TRADING PAIR” wato kudin da ake yin amfani da su domin sayan coin a exchange, misalinsu akwai USDT, USD, EUR, BTC, TRY, abu ne sannane cewa duka wadannan ana amfani da su domin yin siyayya a kasuwannin Crypto Currency, saboda haka kana da damar daidaita TRADING PAIR din da kake so ana nuna maka, Misali idan ka kunna USDT, iya coin din da ake saya da USDT kadai za a nuna maka, haka yake akan sauran.
3. EXCHANGE MANAGEMENT wannan yana da alaqa da kasuwannin da kake so ana nuna maka idan an samu banbancin akan wani coin, idan BINANCE da KUCOIN kadai ka za6a, to iya coin din da aka samu banbanci a wadannan kasuwani zai nuna maka, Idan ka za6i kasuwa sama da biyu, za ana nuna maka farashi wannan coin din a dukkan kasuwannin da ka za6a, saboda haka idan ka ga wani coin da yake da banbancin farashi, abin da zakayi domin ganin sauran kasuwannin shine ka ta6a wannan coin din zai nuna maka sauran kasuwannin, zakayi hakanne akan BUY FROM ko SELL AT, kowanne kana da damar ka za6i sama da kasuwa sama da daya.
Wannan shine takaitaccen bayani da shafin www.nasara.com.ng ya binciko akan wannan manhaja ta COINGAPP,
Amma duk da haka kaima kana iya yin naka bincike domin gano abin da shafin www.nasara.com.ng bai iya ganowa ba.