DaDumiDuminSa: Fatima Ali Nuhu Tafitar Da Mijin dazata Aura Yanzu a…

DaDumiDuminSa: Fatima Ali Nuhu Tafitar Da Mijin dazata Aura Yanzu a…

Yadda Ake Amfani da Aloe Vera Wajen Gyaran Fata:

 

Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul babu ƙuraje ko kaɗan. Wannan ganyen yana ɗauke ne da sinadarai da dama waɗanda sukan iya dada tsawon gashin mace, sanya fuska sheƙi, gyaran jiki da dai sauransu. Saboda haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za’a bi domin amfani da ganyen wajen gyaran fata da kuma gashin kai. Inaso masu karatu su gane cewa a duk rubutun da nake yi, idan na lissafo ababen hadin kwalliya, guda ɗaya daga ciki nake so a rika amfani dashi. Domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar ƙuraje.

 

ABUBUWA DA ALOE VERA KEYI:

 

1. Koɗewar fuska: yawan aiki ko shiga rana na sanya fuska ta yi baƙi ko kuma launinta ya zama biyu. A sami ganyen ‘aloe bera’ sannan a matse ruwan sai a matsa ruwan lemun tsami sannan a kwaba a rika shafawa a fuska domin gyaran irin wannan fatar.

 

2. Yanƙwashewar fata: wannan ganye na rage shekaru daga fuskar mutum. A matso ruwan sa sannan a haɗa da ruwar ‘rose’ sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.

 

 

 

3. Domin fuska mai yawan gumi/maiko: a sami ganyen sai a dan kankare bayansa sannan a ɗora a tukunya da ruwa har sai ya yi laushi sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce sannan a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.

 

4. Domin gautsin fata: a markaɗa dabino da gurji sannan a matsa ruwan ganyen ‘aloe vera’ da ruwan lemun tsami sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti talatin kafin a wanke.

 

5. Gyaran gashi: a matse ruwan ‘aloe bera’ sannan a haɗa da man zaitun a kwaɓa su kwaɓu sosai sannan a riƙa shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke . Yin hakan na sanya baƙin gashi da kuma daɗa wa gashin tsawo da ƙarfi.

AMFANIN DABINO (Date fruits)

***************

Dabino yana daya daga cikin

kayan itacen da Annabi (saww) ke so.

1. Yana saurin narkarda abinci

2. Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure

3. Yana taimakawa wajen kara jini

4. Yana taimakawa Ma’aurata maza/mata

5. Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi. 6. Yana karawa Ido lafiya

7. Yana Rage Nauyin kiba da teba.

8. Yana Maganin Gudawa

9. Yana Saurin Saukarda Hawan jini

10. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun basira..

11. Yana kariya daga Sihiri

12. Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun sauqi wajen

haihuwa.

13. Yana kariya daga Sihiri.

 

**YADDA ZA’AYI

AMFANI DA DABINO.

CIWON NONO GA WACCEN DA TA

HAIHU;

Anacin dabino guda 7 asha man

tafarnuwa karamin cokali sau 1

arana kwana uku.

 

**DOMIN SAMUN NI’IMA GA MA’AURATA;

Ana daka dabino a zuba cikin madara (freesh milk) sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya kafin a kwanta. GA MATA MASU JUNA BIYU;

Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan anyi kusan haihuwa Wannan yana hanawa

macce yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin Allah.

 

**GUDAWA;

Ana daka garin dabino a saka a

ruwan zafi a sha In shaa Allahu

yana tsayar da gudawa.

 

**SAMUN KUZARI;

Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1

da safe da yamma.

 

**SAMUN LAFIYAYYAR FATA;

Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska awa

daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan yana saurin gyara fuska.

Bin cike ya nuna Yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon

CANCER ko wacce iri.

 

**Haka Kuma MANZON ALLAH (saww) YACE DABINO AJWA YANA MAGANIN DUKKAN

CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA KACISHI,BABU WATA

CUTA DA ZATA SAMEKA AWANNAN RANA, KO

KUMA SAMMU KO SIHIRI.

Wasu MALUMMAN MUSULUNCI kuma sunce

Annabi (saww) Yana

nufin kowanne dabino ba wai sai

Ajwaba (Wallahu A’alam)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button