Dama Yan Kwankwasiyya Barayi Ne Sunyimin Satar Da Takai Naira Millions (800) A Gida Na

Dama Yan Kwankwasiyya Barayi Ne Sunyimin Satar Da Takai Naira Millions (800) A Gida Na
Wasu mutane da ake zargin ‘yan daba sun cinna wuta a gidan mawakin siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara.
Haka na zuwa ne sa’o’i kalilan bayan sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi nasara.
Wani ganau ya ce ‘yan dabar sun afka cikin gidan, inda ba su yi wata-wata ba suka rika lalata kayayyaki kafin cinna masa wuta.
Sai dai ƴan mintoci bayan nan, ‘yan sanda suka isa wurin tare da tarwasa ƴan dabar, amma wutar na karaɗe sassa gidan mawakin.
Rarara ya kasance a sahun gaba lokacin yakin neman zaɓen jam’iyyar APC, inda ya yi wa ɗan takarar jam’iyyar Nasiru Gawuna waka.