Fasinjoji 133 sun mutu a sanadiyyar hatsarin jirgin sama a Kasar China

 Jirgin saman China Eastern Airline wanda yake dauke da fasinjoji dari da talatin da uku 133 ya yi hadari a kusa da birnin Wuzhou da ke Guangxi a kudancin China a yau Litinin.

Hukumomin sufurin sama be suka tabbatar

da faruwa hadarin hatsarin jirgin saman, wata kafar yada labarai ta kasar ce ta fara fitar da labarin hadarin inda tace, mutane 133 ne suka rasu.

A halin yanzu dai babu wani baya akan fasinjojin da kuma sanadiyyar hadarin, inda Rahotanni suka bayyana cewa jirgin Boeing 737-800NG, mai MU5735 ya taso ne da ga Kunming a lardin Yunnan zuwa Guangzhou dake lardin Guangdong

Rahotanni sun kara da cewa, ma’aikatan jin kai na kan hanyar su ta zuwa ceto a inda jirgin ya fadi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button