Gargaɗin Tijjani Faraga ga masu ɓata sunan ‘yan fim: Duk wanda ya ce mana kule, za mu ce masa cas!

 JARUMIN Kannywood, Malam Tijjani Faraga, ya bayyana cewa akwai isassun masu ilimi a masana’antar shirya finafinan, don haka duk wani wanda ya ƙara ɓata sunan ‘yan fim ba za su ƙyale shi ba.

Faraga ya yi wannan magana ne a cikin wani rubutu da ya yi ya kuma aiko wa da mujallar Fim, ya ce: “Mu na da isassun masu ilimi a masana’antar Kannywood, waɗanda duk lokacin da masu neman suna da mu za su ce mana kule, za mu ce masu cas.

“Don haka daga yanzu duk wanda ya ke tunanin zai ci mana zarafi, to mu ma ‘yan ƙasa ne, sai dai kotu ta raba mu da shi!

“Mu ba mu san wata sana’ar da ta wuce yin fim ba, mu shi mu ka karanta kamar yadda ake karanta likitanci ko sanin ilimin magunguna ko injiniya ko lauya da sauran su. Don haka ban ga dalilin da zai sa mutum bai taɓa shigowa cikin mu ya gane wa idon sa zahirin me mu ke yi ba, kawai ka yi ta ɓata mu da sana’ar mu a idon duniya. To gaskiya ba za mu lamunta ba. 

“Wace gudunmawa ku ka bayar wajen faɗakar da mu abin da ku ka gani wanda ba daidai ba?”

Da wakolin mu ya nemi jin ƙarin bayani a game da wannan rubutun nasa, sai Faraga ya ce, “Abin da ke faruwa, ai ka ji labarin wanda ya ke maganganu barkatai a kan ‘yan, wanda Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya kai shi kotu. Kishin abin ne wallahi ya sa na yi wannan rubutun, kuma na ke ja wa jama’a kunne lallai su san cewa mu ma mu na da masu ilimi waɗanda idan su ka yi mana abu ba za mu iya bari ba.

“Ka ga dai abin da Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya yi abu ne da ake ce wa ‘eye opener’. Da ma duk abin mun yi shiru ne ana kallon mutane ana jin irin abubuwan da su ke faɗa. Kuma mu a harkar tamu akwai abin da mun yi shi ne saboda mu nemi mafita a rayuwar mu, ma’ana ta kasance sana’a a gare mu, ta kasance gatan mu, ta kasance a kowane lokaci ita mu ka sani, ba mu yin wani abu. 

“To duk wanda zai kawo mana cikas, ya kamata mu tsai da shi, mu faɗa masa gaskiya ga inda mu ka doso. Idan mutum ya na buƙatar ya yi sharhi a kan mu, ya shigo cikin mu, ya zo ya tabbatar da abin da mu ke yi. Idan ya san akwai gyaran da zai yi mana, sai ya yi gyara ya ce abin da ku ke yi ba shi ne mafita ba, ga abin da ya kamata ku yi. 

“Amma mutum bai shigo cikin mu ba, bai taɓa tambayar yaya mu ke yi ba, sannan kuma ka je ka faɗi abin da kai ba ka sani ba, ai ka ga wannan ba adalci ba ne. In har ka shigo cikin mu ka ba da gyara ka ga ba a yi gyaran nan ba, daga nan sai ka fito ka faɗa wa duniya cewa mutanen nan fa ga inda su ka dosa, ko kuma ga a kan abin da mu ka ɗora su, amma sun ƙi. Ka ga wannan ‘is understood’. 

“Amma ba ka taɓa bincike ba, ba ka taɓa shigowa cikin mu ba, kawai sai ka tafi gidan jarida ko kuma ka faɗa wa duniya cewa ai mu na gurɓata tarbiyya ko kuma abu makamancin wannan. Wannan bayanin da na yi shi ne matashiya a kan wancan rubutun da na yi.”

A kan maganar ‘yan Kannywood masu ja masu zagi da cin mutunci kuwa, cewa ya yi, “Abin da ke faruwa a yanzu, za ka ga ba ɗan masana’antar Kannywood ba ne kaɗai ya ke yi ya ke tura wa duniya. Su kuma duniya abin da su ka sani kawai Kannywood. 

“To yanzu akwai tsari da aka fito da shi na rijistar duk wani ɗan Kannywood, in dai halastaccen ɗan Kannywood ne, dole sai ya yi wannan rijista da dokoki za su baibaye shi, wanda babu dama ya yi wani abu shi kaɗai, dole sai da sanin mahukunta na masana’antar. 

“Kawai ɓatagarin da mu ke da su su ne waɗanda su ba su cikin mu, amma kuma duniya ta ɗauka cewa ‘yan Kannywood ne. To su ba su san menene shugabanci ba, ba su san darajar shugabanci ba, shi ya sa ka ga duk abubuwan da ke faruwa su na yin shi gaba-gaɗi.

“Amma ina wadda ta ke cikin masana’antar Kannywood za ta samu dama ta je ta riƙa yin TikTok ko ta na yin abin da ta ga dama ko ta faɗi abin da ta ga dama? Ka ga ko ai dole shugabanci ya yi aiki a kan ta. 

“Saboda haka yanzu duk wanda ka ga ya na fim, lallai ya bi ‘proper channel’ na rijista, wanda gwamnati ta san da shi, dukkan ‘yan ƙungiya sun san da shi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button