Girma Yafaɗi Kuduba Sosai Kuga Abun Da Tahir Fage Yake 

Girma Yafaɗi Kuduba Sosai Kuga Abun Da Tahir Fage Yake

SAQO ZUWA GA IYAYENMU

 

Bayan Sallama irin ta addinin musulunci ina mai farawa dacewa duk tsayin rubutun nan ya kai mai karatu kayi qoqari ka karanta, ka nazarci me aka rubutu, kaga inda akayi kuskure kokuma inda kake da qarin bayani, in duk haka bai samu bah toh ka gwada tattauna maganar da manya wato (Iyayen mu)

 

Nakanyi dogon nazari akan yanda aka dauki al’amuran aure a qasar hausa, duk da qarancin shekaru na. Da za’ace banyi aure bah nayi wannan maganar toh da nasan mutane da dama zasuce da wata manufa nayi maganar kokuma mutuwar zuciya ce dakuma tsoron kashe kudi, amma toh nima nayi auren wanda hakan shi yaban kwarin gwuiwan fadin duk abin da zan fada

 

Duk da nasan Malamai da dama sunyi makamanciyar

maganganu da zanyi haka kuma wasu daga cikin manazarta dakuma iyaye amma abin mamaki shi ne ba wanda yake shirye dan yaga ya gwada daukan mataki akai.A nawa dan qaramin tinanin na fahimci gabobi guda uku inda matsalar take in anxo maganar aure. Sunee kamar haka:

 

*IYAYE(Daga duka bangaren miji da kuma matar)

*Macen da za’a Aura

*Shi namijin da zaeyi Auren

 

IYAYE: Kusan kullum iyayenmu korafi suke akan lalacewar tarbiya daga fannin ‘yaya maza dakuma ‘yaya mata.sae yazamo ba wanda yadamu daya zauna yaga wai meye ma dalilin aukuwar wannar fitina, inma sun zauna sun san dalilin aukuwarta , toh fah ba’a shirye suke da su gyara bah. Bayan nagama bayanan da zanyi dan Allah duk wanda yake da budurwa su gwada wannan jarrabawa a tsakaninsu nanne zaifi ganin zahirin gaskiyar maganata. MUDDIN FA Aure zaeyi tsada to wallahi dole barna ta yadu.Yau da iyayen mu zasu zauna a tsakaninsu sucewa juna muddin akaci gaba da tafiya a haka kanmu muke cuta. koda na WATA daya ne mu gwada bude wata qofa da zata bayar da dama yayanmu suyi aure ko mu aurar dasu a bisa tsarin da Addinin musulunci ya tsara aure, acire maganar alfahari,nuna isa dakuma daurawa kai abin da Allah bai dorawa mutum bah da iyayenmu sunsha mamakin chanji da zasu gani dakuma albarka domin musulunci ba makahon addini bane daya tsara hakan

 

Macen da za’a Aura:A kullum nakance yawanci yan mata sunfi damuwa dakuma daukan hidiman da za’ayi a bikinsu da muhimmanci fiye da zaman auren kansa, baka yadda bah? In kanason tabbatar da maganata yau ka gwada cewa budurwarka “wance Allah ya horemin i da zamu zauna, kuma ya horemin hanyar da zan dau nauyinki na abin da ya shafi ci ko sha ko lapiyarki ko tufatar dake, haka kuma Allah ya horemin sadakin da zan biya don Auran ki, abin da nakeso dake muyi aure a haka ba tare da wani kayan aure, ko dinner, ko red night ko wasu abubuwa bah” kaga yanda zaku qare.Akwae wacce duk son da take maka akan wannan kayan auren da ba wajibin bane zata iya haqura dakai, kokuma ta gwada maka kofa ta wace hanya sai anbi anyi, matsalar anan tafi yawa akan ita macen, zaka iya in kasamu iyayenta masu dottaku ne kamusu wannan bayanin su amince, amma ita kuma zata iya qin amincewa da hakan, inkuma akayi rashin sa’a iyayen suqi itama taqi

 

Namiji mai yin Auren: Mufara magana akan namiji mai dan qaramin jari da bai wuce naira dubu dari uku ko hudu bah, Allah cikin ikonsa ka tanadi inda zaka iya ajiye mace haka kuma da wannan kasuwancin naka zaka iya riqeta haka already ka tanadi sadaki.wadannan abubuwa sune wajibai inaga. Amma a haka sai kaxo kayi ta fadi tashi ka kashe naira dubu dari uku ko hudu wajen hada kayan aure, kaida gaba daya jarin kasuwancin naka bai wuce haka bah, wanda da za’ace instead of ace a kayan Aure ka kashe wannan da jarinka ka qara sai yafi amfanarka dakai da matar da zaka aura din. Toh amma matsalar mu itace Nuna Alfahari dakuma daurawa kai abinda Allah bai daura mana bah dasunan wai Al’ada(Nabi al’ada da gudu har kwanan mutuwa😅😅😅).

 

Akwai kuma wata kuskure da maza keyi wai ba ruwan soyayya da matsayi, wallahi akwai ruwan soyayya da matsayi, akwai wacce kai kanka kasan bazata dauku bah , so karkaje irin wannan gida kace wai kai tsarin Auren addinin musulunci kakeso kayi, Oga you dey waste your time, amma babban abin damuwar shine mu gamu talakawa, babu qarfin, haihuwan yaran akeyi, da maza da matan qara girma kowa yakeyi, auren yayi tsada kuma ance a haka za’a ci gaba da tafiya

 

Exercise

1.Duk wacce tsakaninta da Allah zaman auren ne a ranta

yau tacewa saurayinta wanda tasan cewa yana da zae ajiyeta, kuma yana da hanyar riqe, tace masa wallahi ta shirya suyi aure tunda ae kullum kowa cewa yakeyi ae zaman lapiya ake buqata

 

2 .Duk wani namjin da yasan yana da hanyar da xae riqe mace, kuma yana daa inda zae ajiyeta kuma ita yakeso yau ya ce mata wance mu ajiye alfahari a gefe murufawa juna asiri muyi aure kar akawoki da komai nima bazan kai komai bah kaga Ikon Allah

 

3.Iyayen mu su yadda su gane duk yanda muke kaucewa matsala fah maganinta shine maganinta bawai ayi ta yi kamar ba abin dake faruwa bah, Idan iyaye sun gamsu da tarbiyan mutum, sun gamsu yana da wata sana’a halartacciya ko aiki wanda zai iya riqe yarsu kuma yana da inda zae ajiyeta, kuma sunason juna toh wallahi abarsu suyi aure

 

4.Malaman mu dazaiyiyu su maida topic of preaching nasu for now yazamo wannar matsalar, asakata a gaba har sae anga chanji, A komai sae ace maka ga yanda Annabi Muhammad (S.A.W) Yayi kokuma yace ayi, kuma iyayen mu da malamanmu sun san yanda Allah da manzonsa suka tsara Aure a musulunci, toh meyesa wannan ba’a damu da ita bah

 

Zan dakata anan maganganu ko amsoshin mutane shi zai determining mezan qara cewa a posting na gaba🙏🙏🙏

LALACEWAR ‘YA ‘YA MATA LAIFIN WAYE???

.

Kafin yanzu muna kallon mace mai bin maza ita

tafi kowace mace lalacewa a duniya… Amma a

halin da ake ciki yanzu mun zo wani zamani

wandaa wurin ‘yan mata shaye shaye da

mad’igo shine wayewa…

Tun suna yin abinsu a boye har abin ya fito fili

domin idan yarinya tana irin wannan harkar zaka

ga kowa ya sani har misali ake yi da ita ana

nunata a unguwa… Munin wannan harkar ta sa

‘yan mata yanzu ba su da kunya kuma sun daina

mu’amula da maza sai dai su dinga kula mata

‘yan uwansu…

A shekaru da dama da suka wuce ana danganta

‘yan mata masu harkar mad’igo sun dauko

wannan dabi’ar daga boarding school ne… To

amma yanzu abin da zai baka mamaki ‘yan mata

masu matsakaicin shekaru wadanda suke karatun

boko da islamiya gaban iyayensu zaka ji labarin a

cikin gari cewa tana daga cikin masu irin wannan

dabi’ar…

Iyaye da shuwagabanni sun kasa mayar da

hankulansu domin a shawo kan wannan matsalar

wacce ta zama ruwan dare gama duniya… An sa

ido tarbiyyar ‘ya ‘ya mata sai qara lalacewa take

yi fiye da tunanin mai tunani wai har lalacewar ta

kai ana kunnen doki tsakanin ‘yan mata da

samari wurin mummunan dabi’u…

Idan har da gaske ana so a shawo kan wannan

matsalar to fa dole sai an bi wadannan hanyoyin

sannan :-

– Dole iyaye su sa ido akan su waye qawayen’

yar su… Matuqar basu gamsu da wadannan

qawayen ba to su gimtse wannan alaqar…

– Handset, musamman Android domin ita ce

babbar hanya mafi saurin lalata tarbiya… Da

waya za’a hurewa yarinya kunne kuma da ita

za’a kirata ta je kuma da waya ce za’a fara turo

mata wasu picts ko video masu nuna tsiraici har

sha’awarta ta motsa… Saboda haka yakamata a

daina barin ‘yan mata suna rike waya… Idan

kuma rike wayar ya zama dole to a bata qarama

wacce zata amsa kira kawai…

– Fita ba bisa qa’ida ba… Kullum iyaye suna kallo

yarinya zata dauki hijabi ta fita akan wani dalili

wanda bai zama dole sai ta fita din ba… Idan ta

fita shikenan duk inda ta ga dama zata leqa

kuma sai lokacin da ta ga dama zata dawo…

– Yarinya ta shigo da babbar kyauta da sunan

qawa ko saurayi ya bata… Lallai a dakatar da

yarinyar daga amsar irin babbar kyauta daga

hannun ko waye…

Lallai yakamata iyaye su saka idanu kuma su

kula da kiwon da Allah ya basu akan ‘ya’yansu

domin wallahi rashin sa’ ido da rashin bibiyar

halin da ‘ya’ yanmu ke ciki ya sa ‘yan matan ga

halaka…

Jiya wani yana bani labari yace wallahi akwai

hotel din da mata ke kamawa mata ‘yan uwansu

d’aki… Daga baya da masu hotel din suka lura

sai suka sa dokar hana mata d’aki… Yanzu cewa

yayi matan da suka fahimci haka sai su kira

namiji su bashi kudi ya tafi ya kama musu d’aki

su bashi ladanshi… Yace kuma ba wai ‘yan mata

kawai ba yace har da matan aure da zawarawa…

Haka dai wani yana bani labarin yace jiya jiyan

nan wata ke bashi labarin cewa qawarsu wata

tayi mata sayayya tafi ta dubu d’ari ciki har da

sutura kala 12… To wallahi idan zamu farka mu

farka domin wannan al’amari qara gaba yake yi…

Zaka ga yarinya mai nutsuwa da tarbiya bata

kula samari amma daga baya ta fada tarkon

wadannan mutanen ta hanyar jan hankalinta da

abin duniya…

Wasu ‘yan matan kuma sharri ake musu dan

kawai a bata musu suna ko kuma dan suna

qawance da wacce take yi ko ake zargi…

Lallai mata ku kula domin watarana ku iyaye ne

kuma ku ne makarantar farko… Ya kenan

tarbiyyar ‘ya’yanki zai kasance idan aka ce kina

da irin wadannan mutanen dabi’un???

YA ALLAH KA KAREMU KA KARE ZURI’ARMU

DAGA AIKATA DUK WANI AIKIN ASHSHA…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button