Hanyoyi 2 Da Za Ka Magance Cajin N100 A P2P Lokacin Sayar Da USDT Ko Wani Coin

 

Hanyoyi 2 Da Za Ka Magance Cajin N100 A P2P Lokacin Sayar Da USDT Ko Wani Coin


Kusan yanzu duk lokacin da za ka sayar da USDT ko wani coins a P2P na Kasuwar Binance sai an cajeka N100, wanda hakan yana damun wasu, especially masu qaramin qarfi irina, 

Ni dai akwai wasu dabaru guda biyu da nake yi wanda nake daqile cajin N100 lokacin da zanyi p2p a kasuwar Binance, wađannan dabaru guda biyu su zan yi bayaninsu yanzu, 


1. Dabara ta farko itace; A cikin abin da na fahimta sakamakon P2P da nake yi shine, kamar yadda sanin kowa ne ba iya USDT kadai ake sayarwa a p2p ba, akwai BNB, BTC, BUSD, ETH DAI, NGN duk kana iya sayar da su ko ka sayesu, 

Ka ga kenan idan kana da BNB sai ka ke so ka sayar da shi, to ba dole bane sai ka shiga Market ka sayar ya koma USDT sannan ka taho p2p ba, a’ah kawai kai tsaye za kayi transfer dinsa zuwa Funding Wallet, sai ka shiga p2p, sai ka ta6a sama wajen da BNB yake dai ka nemi merchant ka sayar masa da BNB, 

yawwa Dabarar anan itace, abin da na fahimta a mafi yawancin lokuta idan zan sayar da BNB, Merchant da suke sayan BNB ba sa cajin ko ficika, za ka iya samun wasu suna cajin N100, amma ni dai ban fiya samu ba, 

Sa6anin idan na zo sayar da USDT, abun da na qara fahimta shine, ina ganin saboda mutane sun fi sayan USDT a p2p shiyasa Merchant su ka fi saka Caji na N100, 

Ko kuma Za ta iya yiwuwa Binance ba sa sakawa P2P Merchant Cajin Talla wato “Ads Fee” akan BNB, ko kuma idan har suna sakawa to bashi da yawa idan ka kwatantashi da na USDT, amma fa bani da tabbas akan hakan domin ni ba Merchant bane, 

Abu dai mai muhimmanci anan shine a gaskiya akwai qarancin Caji na N100 lokacin da za ka sayar da BNB a p2p sa6anin USDT. 


2. Dabara ta 2 itace; Idan har zan sayar da USDT ina duba Merchant wanda suke da Trades da yawa, mafi yawancinsu ba sa cajin komai shiyasa suke da trade da yawa, ko kuma na yi ta shiga ina dubawa idan har na ga wanda bai cajin komai sai na sayar masa, 

Amma wani lokacin na kan haqura na baiwa Merchant abin da bai wuce N50 ba idan har merchant ya nuna zai cajeni N100 wanda ni kuma ina sauri, sai na ce masa ya dauki N50, idan kuma bai masa ba ya yi cancel din trade din, wanda nan da nan za ka ga ya yarda a hakan, duba wađannan hotuna da suke qasa, yadda mukayi kenan da wasu Merchants.

1
2Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button