Hira Da Matashin Da Ya Kashee Mahaifiyar Sa a Kano Kan Dalilin Kashee Ta

Hira Da Matashin Da Ya Kashee Mahaifiyar Sa a Kano Kan Dalilin Kashee Ta

Wani saurayi ya je gurin wani Malami ya ce, “Allah ya gafarta Malaml! Ni saurayi ne amma kuma sha’awata tana da yawa, duk inda na ga mace sai na kalleta, shin ko akwai wata addu’a da za a taimaka mini da ita?

 

Malam ya juya gefe, ya zuba Nono har ya cika kofi taf, ya miƙowa saurayin ya ce masa, ka tafi da wannan ka kaiwa wane da gidansa yake guri kaza, zan haɗaka da ɗalibina, komai ƙanƙantar abin da ya zube na nonan nan to zai tsula maka bulalar hannunsa a cikin mutane.

In ka dawo zan gaya maka maganin cutarka.

 

Wannan saurayi ya karɓi aiken tare da ɗalibin dake raka shi, suka ratsa ta kasuwa, makaranta da wajen biki, duk a kan hanyarsu ta kai saƙon.

 

Da suka dawo, Malam ya tambayi saurayi, ka kai saƙon? Saurayi ya ce: ƙwarai ma kuwa, ba tare da kuwa nonon ya ɗisa a ƙasa ba.

 

Malam ya cewa saurayi: mata nawa ka kalla a hanyarka? Saurayi ya ce: ko ɗaya ban gani ba, saboda ina kula da nonan kada ya zuba a ƙasa ɗalibinka ya yi mi ni bulala a cikin jama’a ya kunyata ni.

 

Malam ya ce: haka halin Muminai yake, ko da yaushe cikin jin tsoron Allah (Subhanahu wa Ta’ala) suke, kuma suna tsoron kunyatar ranar Ƙiyama. Ko da yaushe tsoronsu kaɗai ranar da zasu haɗu da Allah (Subhanahu wa Ta’ala).

 

Sukairaj Hafiz Imam ✍️

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button