Hukumar Qidaya Ta Qasa Za Ta Đauki Ma’aikata Na Wucin Gadi Don Gudanar Da Qidaya Ta 2023
NPC launches e-recruitment portal for 2023 Census.
Hukumar Qidaya ta qasa (National Population Commission) ta bude portal domin đaukan ma’aikata na wucin gadi domin gudanar da aikin qidaya na shekarar 2023,
Da ya kewa Manema labari bayani a Abuja ranar Litinin, Manajan Qidaya na qasa Inuwa Jalingo yace Hukumar ta na tsammanin samun masu neman aikin Qidayar har mutum miliyan 25, ya qara da cewa đaukan Ma’aikatan na wucin gadi zai kasance cikin adalci.
Inuwa Jalingo yace Ma’aikatan da za a dauka sun hada da facilitators, training center administrators, monitoring & evaluation officers, data quality managers, data quality assistants, supervisors, enumerators, da special workforce.
Abubuwan da ake buqata domin cike neman wannan aikin :-
- National Identification Number
- Valid and Functional Gmail Account,
- Valid and Functional Phone Number,
- Valid and Functional /Operational Commercial Bank Account (No student/NYSC Account)
- Valid Educational Qualifications,
- Access to and knowledge on the use of computers, tablets & smartphones is an added advantage.
Yadda Za Ka Cika Neman Aikin
Za ka latsa wannan adireshin da ke qasa zai kawoka zuwa ga shafin da ke qasa a hoto http://doanncx4d1b7d.cloudfront.net/

Sai ka danna Start Application sai ka ta6a “Start as Ad-hoc Staff“

Sai ka dannan wasu Boxes da suke farkon kowanne rubutu a wannan hoton da ke qasa

Sai ka danna PROCEED zai đaukeka zuwa ga shafin da za a buqaci ka shigar da NIN NUMBER, bayan ka shigar sai ka danna VERIFY,

Za ta rubuta maka verification is successful, za ta buqaci ka ajiye Application ID đinka, bayan ka ajiye sai ka danna OKAY,

Bayan ka danna OKAY Zai kaika shafi na farko domin fara yin Application dinka,
Sai ka bi ka cike duk abin da kake buqata a kowanne shafi, bayan ka cike sai ka danna NEXT zai kaika zuwa ga shafi na gaba, za ka cigaba da haka har ka kai wajen da zakayi submitting Application dinka
Hukumar NPC za su rufe portal na đan lokaci a ranar 7 ga watan November zuwa 13 ga watan November 2022