Innalillahi Abokanan Karatun Sane Suka Yimasa Dukan Tsiya Har Sai Da Ya Mutu

Innalillahi Abokanan Karatun Sane Suka Yimasa Dukan Tsiya Har Sai Da Ya Mutu

INNA LÍLLAHÍ WA’INNA ILAIHÍ RAJI’ÚN

 

Wasú Dalibaí Sún Yi Sanadíyar Mútúwar Abokín Karatúnsú A Makarantar Lafíya Daké Jìhar Sókótó

 

DÁGA Real Buroshi Mawaka Sókótó

 

Wasu ɗalibai a makarantar kiwon lafiya ta Sultan Abdurrahman School of Health Technology Gwadabawa dake jihar Sokoto, sun kashe abokin karatun su har lahira ta hanyar yi masa bugun kawo wuƙa har ya zamo sanadiyar mutuwarsa a daren jiya Lahadi.

 

Ɗalibin mai suna Lukman wanda aka fi sani da Khalifa ɗan garin Kalambaina mai karatu a sashen lafiyar haƙori (Dental& surgery department) aji na biyu (200L) ya rasa ransa ne a sanadiyar wani zargin da abokan kwanansa ke yi mishi wanda ba su da tabbacin hakan, bayan cece kucen da ya faru a tsakanin shi margayin da abokan nasa ne har yakai suka yimasa taron dangi suka zamo sanadiyar rasa rayuwarsa.

 

Wannan mummunan lamarin ya faru ne a wajen makaranta cikin gidajen hayar kwanan su, inda yanzu haka hukuma na kan ƙwakkwaran bincike game da lamarin.

 

Allah ya Jikansa da Rahamarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button