Innalillahi Murja ‘yar Tiktok ta Zagi Turji shugaban ‘yan bindiga ta janyowa kanta Masifa yakirata..

Innalillahi Murja ‘yar Tiktok ta Zagi Turji shugaban ‘yan bindiga ta janyowa kanta Masifa yakirata..
TIKTOK BARAZANA NE GAREMU
Duk wani dan iska da ‘yar iska marassa kunya fitsararru sun kare a dandalin Tiktok, yau Tiktok ya zama babban barazana ga tarbiyyan yaran da suke tasowa suka fara mu’amala da kafofin sada zumunta
‘Yan iskan Tiktok ba sa jin nasihar Malamai, basa ganin kima da darajar kowa, hake suke yada masha’arsu da barnan su babu kunya ba tsoron Allah
Ko baka Tiktok, Facebook zasu kawo maka bidiyo na ‘yan iskan Tiktok, don haka hatta wadanda basa Tiktok basu tsira daga ganin barnan da ake yadawa a Tiktok ba, don haka ya zama wajibi a magantu
A ka’ida ta rayuwa, duk yaron da bai da kunya, yana iya fitowa fili ya aikata fasadi da iskanci a bainar jama’a, to da kyar ne idan sun kasance ‘ya’yan da aka samar da cikinsu ta hanyar aure
Dan halal da wahala ya aikata abinda ‘yan iskan yaran nan suke aikatawa a dandalin Tiktok Wallahi jama’a, ku tambayi Malamai akan wannan ka’ida ta rayuwa dangane da alakar mutum da rashin kunya
Sannan a rayuwa duk wanda ya rasa mafadi ta ya zama annoba a cikin al’ummah
Idan kana da hankali, sai ka kalli irin abinda su Murja Ibrahim suke yi a Tiktok, zaka tambayi kanka anya suna da iyaye ko mafadi?
Ko kuma da sanin iyayensu da magabatansu suke yin abinda sukeyi a Tiktok?, idan kuwa hakane to sun yi gadon rashin albarka daga magabatansu kenan, domin duk Uban da ya haifi yaro dole ya zama yana da cikakken control akan yaron sai dai idan Uban ya kasance lalatacce ko mutumin banza
Fatan mu shine Gwamnatin Nigeria ta rufe wannan shafin na Tiktok a Nigeria, gashi duk lalacewan tarbiyya da muke gani a Amurka sai da aka samu wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka shigar da kuduri na neman a rufe shafin Tiktok a Amurka, dalilinsu sunce yana bata tarbiyyan yara kanana
Idan rufe Tiktok ba zai yiwu ba a Nigeria, to hakkin Gwamnati ne tayi amfani da duk wani mataki da zai tsare mana mutunci da tarbiyyan yaran mu, Gwamnati ta bi diddigin lalatattun yaran Tiktok irin su Murja Ibrahim, idan ya tabbata ‘ya’yan shegu ne ko basu da mafadi to ya zama wajibi Gwamnati ta kamasu ta killacesu su bace daga cikin al’ummah
Yaa Allah Ka kare yaran Musulmi daga sharrin ‘yan Tiktokأمين يا حي يا قيوم