INTER-BANK TRANSFER CODE

  LAMBOBIN YIN TRANSFER NA BANKUNA || INTER-BANK TRANSFER CODE 

wađannan lambobi sune ake amfani da su domin yin transfer ta kuđi daga wani banki ko zuwa wani bankin, Haka da sune ake amfani da su wajen saka kati ko kuma sayan Data daga asusun banki zuwa layin sadarwa, 

Da su ake amfani wajen duba adadin kuđin da ya rage cikin asusun banki (CHECK BALANCE),

Da su ake amfani biyan kuđin wuta (power Tariff), biyan Bill na ruwa ko wasu abubuwa masu alaƙa da hakan, Subscription na tashohin tauraron đan Adam Wato Satelite duk ana iya amfani da waɗannan wađannan lambobi wajen biyan kuđaden abubuwan da na ambata a sama da wasu abubuwa masu yawa wanda ban ambata a sama ba Kamar duba lambar BVN, 


JERIN BANKUNA DA LAMBOBIN GUDANARWARSU||| INTER-BANK TRANSFER CODE


Access Bank *901#

Diamond Bank *426#

Eco Bank *326#

Fidelity Bank *770#

FCMB Bank *329# ko *389*214#

First Bank *894#

Guaranty Trust Bank *737#

Heritage Bank *322#

Jaiz Bank *389*301#

Keystone Bank *322*082#

Polaris/Skye Bank *833#

Stanbic IBTC Bank *909#

Starling Bank *822#

Union Bank *389*038#

Unity Bank *7799# ko *389*215#

United Bank for Africa UBA *919#

Wema Bank *945#

Zenith Bank *996#


Sai kuma lambar da ake amfani da ita wajen duba lambobin BVN Wato Bank Identification Number *565*0#, amma duk lokacin da zakayi amfani da wannan lambobi domin duba BVN ya kasance akwai kuđi a layinka domin ana cajin ₦20, Sannan ya kasance layin da kake amfani da shi a bankinka wajen samun Alert ko yin transaction da shi zaka duba BVN. 

Sai kuma lambar da ake amfani da ita wajen duba lambar đan-ƙasa wato National Identification Number NIN a takaice, Ana amfani da *346# wajen duba wannan lambar NIN, Shima ana cajar ₦20 duk lokacin da zaka duba, Sannan ya kasance layin da zaka duba shine kayi amfani da shi lokacin yin katin dan-ƙasa.


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button