KA DA KA SAKE KA RIQE KASUWANCIN CRYPTO A MATSAYIN KASUWANCIN DA KA DOGARA DA SHI


 KA DA KA SAKE KA RIQE KASUWANCIN CRYPTO A MATSAYIN KASUWANCIN DA KA DOGARA DA SHI


Yana da kyau mu fahimci cewa ba qaramin garaje bane a matsayinka ka riqe kasuwancin Crypto a matsayin kasuwancin da ka đora rayuwarka kake yinsa, wannan shawarar ina bayar da ita ne ga sabbin Yan crypto wanda suke da qaramin jari da kuma qarancin ilimi, 


Ba laifi bane lokacin da ka timbatsa ka cika ka yi tatul da ilimin crypto ka riqeshi a matsayin kasuwancin da ka dogara da shi domin wannan ilimin shine babban jarin da  da zai baka riba kuma zai riqe ka har tsawon rayuwarka a cikin kasuwancin crypto ba ka je qasa ba, 

Domin wannan ilimin zai zame maka fitilar da zai haska maka lokacin da ya dace ka sayi coin ko ka sayar da shi cikin kyakkyawar riba, 


Qarancin ilimin crypto shine yake janyo mana tafka asara, sabo da haka a lokacin da ka riqe crypto a matsayin kasuwancin da ka dogara da shi kuma kana da qarancin ilimin kasuwancin to tabbasa kamar ka zuba ruwane a cikin rariya cikin lokaci qanqani zai zube qasa, 

Ka ga kenan idan ka zuba duka dukiyarka cikin wannan kasuwancin za ka wayi gari cikin da-ma-na-sani, Allah ya kiyaye. 


Yana da kyau ka mallaki wani kasuwanci na zahiri domin zai zame maka garkuwa da zakayi amfani da ita wajen tafikar da rayuwarka ko da kasuwar crypto ta shiga cikin DIP kamar yadda muke ciki kenan a yanzu, 


A kullum dai shawarar shine duk mai son yin kasuwancin cryptocurrency to dole ya tashi ya nemi iliminsa matuqar da gaske yake kuma ba ya son yin Asara. 


Allah ya sanyawa wannan kasuwancin namu Albarka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button