Kasuwanni 4 Mafi Dacewa Ga Sabon Dan Crypto Ko Kuma Mai Qaramin Jari Domin Samun Riba Mai Yawa

 Kasuwanni 4 Mafi Dacewa Ga Sabon Dan Crypto Ko Kuma Mai Qaramin Jari Domin Samun Riba Mai Yawa


Kamar yadda sanin duk wani dan Crypto ne cewa akwai kasuwanni da ake hada-hadar cinikayyar Cryptocurrencies a cikinsu, wanda wađannan kasuwannin kashi daban-daban ne, akwai manya akwai qanana sannan akwai matsakaita, haka kuma akwai na kasashen waje sannan akwai namu na nan gida Nigeria, 

Daga cikin manyan kasuwannin akwai BINANCE, COINBASE, CRYPTO.COM, OKX, KUCOIN da sauransu, 

Daga cikin matsakaita akwai BITGET, BYBIT, HOTBIT, COINEX. 

Daga cikin na gida Nigeria akwai ROQQU da BUNDLE.

A matsayinka na sabon dan Crypto ko kuma mai qaramin jari akwai kasuwannin da suka fi dacewa da kai, sabo da yanayin ka na kasancewa sabo a kasuwancin ko kuma mai Qaramin jari, 

Domin ko a zahiri duk dan kasuwa yana zuwa ne kasuwar da ta dace da jarinsa ko kuma yanayin wayewarsa a harkar wannan kasuwancin, 

Misali:- akwai masu kasuwancin da qarfin jarinsu ya kai su yi kasuwanci na qasa-da-qasa wato international business kenan, wadannan yan kasuwa suna iya zuwa kasashe kamar irinsu su Dubai ko china domin siyayyar kayan da suke kasuwanci akansa, 

Sun sami damar zuwa qasashen ne domin jimawarsu a cikin kasuwanci wanda ta basu wayewar fita kasashen waje domin kasuwancin da kuma qarfin jarin da suke da shi, 

Amma sabon dan kasuwa wanda ya fara kasuwanci a yau wanda yake da qarancin wayewa a kasuwancin da kuma qaramin jarin da bai fi kudin Ticket din jirgin wani dan kasuwan ba garaje ne ya ce zai fita kasashen waje domin kasuwancin,

Haka abin yake a kasuwancin Crypto Currency iya qarfinka da wayewarka da iliminka a harkar kasuwancin iya kasuwannin da suka dace da kai, 

Abin da zai qara tabbatar maka da hakan shine akwai kasuwannin da cikin qasa da mintuna 5 kana iya yin rijista kuma ka fara amfani da su sabo da daman sun fi dacewa da sabon dan Crypto ko kuma mai qaramin jari zamu iya kiransau da Newbie Friendly Exchanges, misalinsu akwai KUCOIN, COINEX , BITGET da HOTBIT, 

Akwai kuma kasuwannin da sai kayi KYC verification wato KNOW YOUR CUSTOMER sabo da girman kasuwar, Misalinsu akwai BINANCE, COINBASE GATE IO dss.


KASUWANNI 4 MAFI DACEWA GA SABON DAN CRYPTO KO MAI QARAMIN JARI 

KUCOIN 

GATE IO 

COINEX 

MEXC

Dalilin da yasa nace wadannan sune kasuwannin da suka fi dacewa ga sabon dan Crypto shine akwai dalillai kamar haka:-

  • Kasuwanni ne da suke da coin da token masu sauqin farashi, a domin akwai tokens masu farashin da basu kai $0.01 ba, wanda kuma suna bada alkairi sosai yanda ba ka zato, domin suna iya linka maka kudinka cikin lokaci qanqani.

  • A cikin wadannan kasuwannin ne za ka ga da yawa daga cikin Token wanda sai anyi listing dinsu anan Kafin su je manyan kasuwanni irinsu BINANCE, wanda hakan yana nufin wa idan ka yi Sa’a ka sayi wani token ba ka ankara ba sai dai ka ji ana cewa BINANCE ko COINBASE zasuyi listing din wannan Token din  wanda hakan yana nufin za ka samu kyakkywawar riba kenan saboda daman kai kana da token din,  Misali Kafin $GALA ko kuma $GALAX “duk sunansa ne” Ya shiga BINANCE sai da ya shiga COINEX, akwai irin wadannan tokens din da yawa ba adadi. 

  • Da yawa daga cikin wadannan kasuwannin da suka fi dacewa ga sabon dan Crypto ko kuma mai qaramin jari za ka ga suna da qarancin Gas Fee lokacin da za ka tura wani token zuwa wata kasuwar, A yanzu kamar $TRON TRX shine Coin da aka fi yin amfani da shi wajen Transaction na Withdrawal sabo da qarancin Gas fee, amma akwai Coins da suke da qarancin Gas fee qasa da na $Tron, Misali akwai $SOLANA $SOL kenan,  akwai wanda Gas fee dinsu ko qwandala daya bai kai ba, daga cikin kasuwannin da na tabbata suna da qarancin gas fee akwai COINEX ka je ka duba za ka gani, domin a kwanakin baya suna đaukan 0.8 TRX a matsayin Gas Fee yanzu ne suka qara. 

  • Cikin wadannan kasuwannin ne za ka samu tokens wanda suke da Low Market Cap wanda kuma suna da Use Case wanda hakan yana nufin ba abin mamaki bane su iya lillinka maka kudinka cikin lokaci qanqani. 

  • Cikin wadannan kasuwannin ne za ka samu Coins masu feature, da yawa za ka samesu suna da BLOCKCHAIN nasu na kansu wanda hakan yake nufin cewa nan gaba zasu bada mamaki domin suna da Case Use mai qarfin Gaske. 

  • Cikin wadannan kasuwannin ne za ka samu akwai qarancin WHALES ma’ana masu qarfin Jari wanda mutane kadan daga cikinsu suna iya dumper token cikin qasa da minti daya ya fadi qasa warwar, amma qarancinsu cikin wadannan kasuwannin yana kawo qarancin dumping din token cikin qanqanin lokaci. 

  • Wadannan kasuwannin suna da sauqin registration kamar yadda na fađa a sama, kana iya yin register da su kuma ka fara amfani da su cikin qasa da mintuna 5, sa6anin manyan kasuwannin da suna iya daukan ka tsawon kwanaki kafin ka gama KYC dinsu sannan ka fara amfani da su. 


Idan Har ba ka da daya daga cikin wadannan kasuwannin to ga Referral link nan ka shiga ka yi registration da su. 

GATE IO

https://www.gate.io/signup/6910887

KUCOIN 

https://www.kucoin.com/r/rf/r3NNV6K

COINEX 

https://www.coinex.com/register?refer_code=runxs

MEXC

https://m.mexc.com/auth/signup?inviteCode=1E4oc





 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button