Matar Hariji Hausa Novel Complete Book

Matar Hariji Hausa Novel Complete Book. Miqewa tayi da sauri ta daga kanta tana kallon me shigowar ya tafa hannu tare da tuntsirewa da dariya yace “kin dauka wannan raggon mijin nakine ko?

Nifa ina mamakin yanda mace kamarki zaki tsaya kina auren wannan sullutun mutumin da baya iya biya miki buqatarki itafa mace tafi kowa yanci kuma tanada zabin daya dace da ita namiji dai har namiji a riga Amma a gado babu fuss sai jinkai da izza a waje,

koda yake hakanma ni yayimin ya auromin mata babu ko sisina nayi mata ban ruwa kuma ta cikamin aljihuna da kudi hhhhhhhh!”

Suka kwashe da dariya ita kuma ta tsuke fuska tace “amma kasan nace maka kada kazo gdannan yau yayanka zai dawo kuma kasan cewa banason ya fahimci akwai alaqa tsakaninmu mu zauna a matsayin abokan gaba haka nakeso shirin ya kasance.

Dara² idanunsa ya sauke akan me tallan furar da ya tsayar ta dago da hardaddiyar hausarta tace “Kado ka hiya niman magana wallah in zaka shiya jaka hudu ka shiya in bakka shiya kuma ka bareshi dama kai ka cika son araha toni komi nawa mi tsadane kajima in hwadi maka”

Yanda take mgnr ne yayi bala’in bawa pillot Lameer dariya yayi murmushi yace “komanki me tsadane nikuwa idan babu damuwa mu buga wani wasa mana ki fadamin komai kikeso zanyi miki zan aureki kawai dan ki rinqa bani dariya ko sau daya kika bari nazo gurinki baki bani dariya ba zan sanya karnukan gdana su cijeki idanfa kin yarda”

Matar Hariji Hausa Novel Complete Book
Matar Hariji Hausa Novel Complete Book

Wani murguda baki Jiddoh tayi tace “hohoho aura kado mi akai akayika da har zan kasa baka dariya yo ko innarka da baffanka ai nabawa dariya kai bura ma kaji wani abu kwanaki da naje burni har wani me qaton ciki nabawa dariya bare kai dan tatsitsi dakai amma fah tsaya kaji ni bani auren kado kado bashi riqon aure saki a jininku shike yawwa kuma jauro Madi ma ya fika kyau gashi dan gayu har agogo fah yake sawa🤣🤣🤣

 

Matar Hariji Hausa Novel Complete Book

 

Sake gyara zaman hularsa yayi ya zuba mata maganadisun idanunsa yana qare mata kallo sama da qasa yace “nononki baiyi tsami ba ko?” Turo baki gaba tayi ta qara tura cokalelen dankwalinta gaba tace “yo nonon shanuwa idan yayi tsami ai saidai akai juji” dariya yayi da ganin bata fahimci me yake cewa ba yace “amma akwai ranar da nonon naki zaiyi tsami fah” wani tsalle tayi tace “ariyyy hege Kaɗo da muguwar alkaba’i kake idan nonona yayi tsami ai goggo kasheni takayi kai barima kaji ranar nan da mukaje dandali ana ajon auren me yar butta da tsalha da nashiga ina rawa kowa saida ya liqamin takarda”

Matar Hariji Hausa Novel Complete Book

Ɗan ƙaramin bakinta ya zubawa ido yana kallonta yarinyar kyakkyawa sai bambadanci daya dami rayuwarta miqewa yayi tare dayin miqa yace “kisamu leda ki juyemin a ciki zan baki jaka uku da rabi” miƙewa tayi ta zari qwaryarta zata tafi ya riqo hnnunta da sauri yace “tsaya mana Hauwa” sakin ƙwayar tayi jikinta ya dauki rawa ta zube a gurin ta fasa uban ihu ya saki bottle  ɗin hannunsa yayo kanta yayi saurin rufe mata baki yace “ke kinada hsnkali kuwa JIDDAH uwar me nayi miki da zaki zunduma wannan uban ihun salon kisa yan uwanki su bugeni”

Karanta Wannan: Maganin Girman Nono Budurwa Da Matar Aure

sake rintse idonta tayi ta zunduma ihu tana fadin “shikenan na mutu na lalace jiyannan goggo ta gama hwaɗi mami cewa idan kaɗo ya tabaka mutuwa kakeyi yanzu nima shikenan mutuwata tazo zan tafi inda Allah wayyoh ni goggo wayyoh ni baffa wayyoh ni Madi dan burni kaɗo ya cutamin shikenan walakiri zaya kasheni…”

Download Matar Hariji Hausa Novel Complete Book
  • NOVEL NAME: Matar Hariji Hausa Novel Complete Book
  • UPLOADER: AIHAUSANOVELS
  • WRITTEN BY: OUM HAIRAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button