Matsalolin Authenticator Tare Da Maganinsu

 Matsalolin Google Authenticator  A EXCHANGEs Tare Da Maganinsu


Matuqar kana amfani da Kasuwar Crypto Currency ta HOTBIT da sauran kasuwanni kamar BINANCE da KUCOIN shafin www.nasara.com.ng yana baka shawara ka tsaya cikin nutsuwa ka karanta wannan rubutun, domin yana da muhimmanci ga dukiyarka da take cikin kasuwar CryptoCurrency, 

Akwai matsaloli da suke faruwa ga masu amfani da kasuwannin Crypto Currency wanda suke da alaqa da Google Authenticator, Shafin www.nasara.com.ng ya binciko wasu daga cikinsu tare da bayanin yadda za a magance su.

Ga matsalolin:- 

1. Da yawa suna canja waya yayin da suka zo shiga (Log In) ko withdraw a cikin exchange ko wallet a sabuwar wayarsu sai a buqaci Google Authentication Code, wanda sun bar Authenticator accounts din a tsohuwar wayarsu.

2. Wasu kuma ana sace musu wayarsu wanda hakan ya ke zama silar rasa Authenticator Accounts dinsu na wallet ko exchange. 

3. Wasu kuma suna restore/reset din wayarsu wanda hakan ya ke zama sanadiyar rasa Authenticator Account din su, Da wasu matsalolin da shafin www.nasara.com.ng bai ambata ba. 

Da yawa masu amfani da Google Authenticator suna mantawa da cewa duk lokacin da za ka rabu da wayar da Google Authenticator dinka yake kanta to dole ne ka dauki wasu matakai wanda shafin www.nasara.com.ng zai yi bayaninsu nan gaba cikin maganin matsalolin da ake fuskanta a Google Authenticator. 

Shiga Nan Ka Karanta Yadda Ake Transfer Na Google Authenticator Daga Wata Wayar Zuwa Wata Wayar

Maganin Matsalolin AUTHENTICATOR Da Ake Fuskanta A Kasuwar HOTBIT Da Sauran Kasuwanni Na Crypto Currency 

1. Magani na farko shine duk lokacin da zakayi activating na Authenticator akan wata EXCHANGE ko WALLET akwai wasu haruffa da lambobi wanda ake kiransu da “PRIVATE KEY” ko “SETUP KEY”, wanda EXCHANGE ko WALLET din da zakayi activating na Authenticator za su baka wannan PRIVATE KEY din wanda za ka daukesu (copy) ka je ka shigarsu da su cikin Authenticator,

To wannan PRIVATE KEY din dole ka ajjesu ta hanyar rubuta su a wata takarda ko littafi, saboda suna bada wannan PRIVATE KEY din sau daya ne, idan ka rasa su baka ajiyesu a wani waje ba to kamar ka rasa Authenticator Account wannan WALLET din ko EXCHANGE, 

Kuma sune RECOVERY PHRASE na wannan Authenticator account din na wannan EXCHANGE ko WALLET din,  da su ake dawo da Authenticator account a wata wayar, 

Bayan private key, akwai “QR CODE” shine za ka gani kamar wata akwai fa digon baqi a cikinta, 

Shi QR CODE yana da matsayin PRIVATE KEY ne, shima ana activating din Authenticator da shi, shi yasa duk EXCHANGE din da za ta baka PRIVATE KEY domin activating Authenticator to za ta baka QR CODE, sai ka zabi da wanda za kayi amfani da shi,

Shima QR CODE ana ajiyeshi ta hanyar hoto, ma’ana za kayi screenshot dinsa sannan ka ajiyeshi a matsayin hoto, yadda nan gaba idan ka rasa wayarka za ka iya amfani da shi domin activating din Authenticator account dinka a wata wayar.

2. Magani na Biyu:-  Da yawa daga cikin kasuwannin Crypto Currency ba dole ba ne sai ka saka musu Google Authenticator ba, daga cikin irin wadannan kasuwannin akwai HOTBIT, BINANCE, KUCOIN da sauransu, 

Tinda ba dole bane sai ka saka Google Authenticator a wasu kasuwannin ba, to shafin www.nasara.com.ng yana baka shawarar ka haqura da sakashi domin gudun abin da zai je ya dawo, 

KAMAR BINANCE DA KUCOIN DA HOTBIT, mafi qanqatar abin da za ka saka na tsaro wato security sune guda biyu, za ka zabi guda biyun daga cikin wadannan; Phone Number, Authenticator, Email. 

Tinda kana da damar hada tsakanin phone Number da email sun isheka ka haqura da su ba sai ka qara da Authenticator ba. 

3. Magani na Uku:-  Shine abin da da yawa daga cikin masu amfani da Authenticator ba su sani ba, 

Shi wannan maganin sunansa TRANSFER OF  AUTHENTICATOR ACCOUNT,  Ma’anarsa shine ka dauke account dinka na Authenticator wanda yake kan EXCHANGE ko WALLET dinka daga wata wayar zuwa wata wayar,

A lokacin da za ka canja waya ko za kayi restore/reset din wayarka, domin kar ka rasa account dinka na Authenticator sai ka nemi wata wayar ko kuma idan waya ka canja sai kayi transfer din Authenticator account dinka zuwa sabuwar wayar.

SHIGA NAN ka karanta yadda ake Transfer na Authenticator Account daga wata wayar zuwa wata wayar

4. Magani na Hudu:-  Wannan maganin yana da matuqar amfani domin maganine sadidan, 

Authenticator suna da yawa a Playstore, amma mafi shahara shine GOOGLE AUTHENTICATOR, 

Bayan Google Authenticator akwai wasu Authenticators din wanda suna da abin da Google Authenticator bashi da shi, 

Daga cikinsu akwai wani Authenticator wanda, yana da features din da Google Authenticator bashi da shi, 

Shi wannan AUTHENTICATOR din kana iya dawo da Authenticator accounts dinka ko da bayan an sace maka wayarka ko kuma ka yi restore/reset dinta ko kuma ka sake sabuwar waya ko da baka da Private Key na Authenticator account din, 

Ka ga kenan wannan Authenticator din shine mafi cancantar Authenticator da ya kamata mu yi amfani da shi, 

Domin kiyaye kanmu daga yin asara ta dalilin rasa Authenticator account dinmu,

Amma shi wannan AUTHENTICATOR yana da dokoki da dole sai ka kiyaye su,

SHIGA NAN ka karanta cikakken bayani akan wannan Authenticator da yadda zakayi rijista da shi da kuma abubuwan da za ka kiyaye lokacin rijista

5. Magani na Biyar:-  Wannan maganin a gaskiya yafi kowanne tsada kuma ya fi wahalar samuwa, 

Maganin yana da alaqa da wanda suka rasa Authenticator Account dinsu bayan an sace musu wayarsu ko sun canja waya ko sunyi restore dinta ko kuma wata matsala dai da ta janyo suka rasa Authenticator Account dinsu a cikin Google Authenticator, 

Da yawa daga cikin masu amfani da kasuwar HOTBIT suna da wannan qorafin, ba iya kasuwar HOTBIT ba har da sauran kasuwanni, 

Babbar matsalar itace akwai dukiyarsu a cikin kasuwar,

To a gaskiya akwai buqatar ka nutsu domin fahimtar bayanin da zanyi kan hanyar da za ka bi domin dawo da Authenticator account dinka, 

Domin cikakkiyar fahimtar yadda zaka dawo da shi ina mai baka shawara da ka karanta wannan bayanin da zai zo a qasa sama da sau daya, 

Domin ka tina fa dukiyarka ce kake son dawowa da ita akwai buqatar kyakkyawar fahimta kan yadda za ka dawo da ita, 

Ina baka tabbacin matuqar ka tsaya ka fahimta sosai Authenticator account dinka zai dawo kuma ka samu dama zuwa ga dukiyarka. 

SHIGA NAN ka karanta Yadda za ka dawo da Authenticator Account dinka na HOTBIT 


Wannan shine qarshen bayanai da shafin www.nasara.com.ng ya tattaro akan wasu matsalolin Authenticator tare da maganinsu, 

Idan akwai wata tambaya ko neman qarin bayani sai a tura saqo ta hanyar whatsapp a wannan Lambar:-
 07035791120

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button