Muna Sane Da Irin Hukuncin Zaluncin Da Aka Yankewa Sheikh Abduljabbar, Muna Kira Ga Abba Gida-Gida Yayi Duba Acikin Lamarin Abduljabbar….

Muna Sane Da Irin Hukuncin Zaluncin Da Aka Yankewa Sheikh Abduljabbar, Muna Kira Ga Abba Gida-Gida Yayi Duba Acikin Lamarin Abduljabbar….

AMFANIN DADDAWA GA DAN ADAM:

 

daga| bbchausa.com

 

1 – Tana taimakawa wajen al’amarin da ya shafi iyali

Kalwa wadda ake amfani da ita wajen haɗa daddawa – locust beans a Turance – na kunshe da sinadarin zinc, wanda kamar yadda bincike ya nuna yana kara mizanin kwayoyin halittta na testosterone, wanda ya fi yawa a jikin maza.

 

Har wa yau, bincike ya nuna cewa tana da sinadarin mineral, wanda ke kara ingancin kuzari da inganta rayuwar jima’i.

 

Wani dalili na sa Daddawa cikin abinci shi ne tana bunkasa kwayoyin halitta waɗanda suke jikin mutum, saboda ta kunshi sinadarin zinc, wanda shi ma yake taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa daga wata cuta.

 

2 – Tana taimaka wa lafiyar idanu

Kalwa ta kunshi sinadarin gina jiki na Vitamin A wanda kuma yake taimaka wa idanu da kuma hana kamuwa da cutar makanta.

 

Tana yin hakan ne ta hanyar samar wa wani bangare na ido da ake kira ‘cornea’ kwayoyin halitta na antiodidants waɗanda suke taimakawa wajen hana kamuwa da matsalolin da kan shafi idanu.

 

3 – Nagartar kasusuwa da lafiyar haƙora

Kalwa har ila yau ta kunshi sinadarin calcium wanda shima yana taimakawa wajen samar da nagartattun kasusuwa, hakan ma yana taimakawa wajen lafiya da kuma ingancin hakora.

 

4 – Narkar da abinci da kuma amfaninsa

Sinadaran Lipids wanda ke cikin jiki na taimakwa matuka wajen narkar da abinci kamar yadda ya kamata da kuma wasu abubuwan da ya kunsa.

 

Sinadaran lipids ana samun su cikin kalwa, ana kuma bukatarsu ne saboda daukar dawainiyar nau’in abinci na fat, ya mayar da shi wanda zai iya narkewa, domin samar da sauran sinadari da jiki ke buƙata na bitamins A, D, E, K daga cikin kanana da manyan hanji, har zuwa inda jini yake.

 

Ana yin hakan ne aboda tabbatar da cewa abinci ya kai zuwa wuraren da suka kamata da kuma aikin su.

 

5 – Tsokar jiki mai lafiya

Kalwa ta kunshi sinadarin abinci na ‘protein’, wanda yake aiki mai muhimmanci wajen gina ƙasusuwa, da tsokar naman jiki, da jijiya, da kuma jini.

 

Jikin mutum yana amfani da sinadari na protein ne saboda ya ginu da kuma yin wasu gyare-gyare na wasu kananan kwayoyin halitta na jikin mutum.

 

Sinadarin protein na amfani wajen samar da ƙwayoyin halitta na enzymes, wadanda ke cikin baki kuma suke taimakawa wajen daddatsa abinci ko kuma rage masa girma saboda ya samu narkewa domin yin aikin da ya kamata a jikin mutum.

 

6 – Taimakawa wajen ciwon sikari da kuma mizanin cholesterol

 

Bincike ya nuna ita Kalwa ta kunshi fibre wadda kuma ana iya narkar da ita, tana taimakawa wajen lura da yadda, mizanin sikari yake, da kuma rage yawan mizanin cholesterol. Don haka wadanda suke fama da cutar sikari, ya kamata su rika amfani da Daddawa a cikin abincin su.

 

7 – Rage hawan jini

Haka nan, daddawa na taimaka wa wajen rage hauhawar jini da kuma rage haɗarin kamuwa da shanyewar ɓarin jiki, wato stroke a Turance.

 

8 – Ana maganin gudawa

Masana harkon lafiya na cewa daddawa na ƙunshe da sinadarin tannins da ake samu a ganyayyaki da abinci da dama.

 

Suka ce duk abincin da ke ɗauke da sinadarin tannins mai yawa, akan umarci mai fama da gudawa ya ci domin rage yawan fitar ruwa a jikinsa.

 

9 – Tana gina ƙwaƙwalwar jarirai

Amfani da daddawa na taimaka wa wajen hana zurarewar sinadaran folic acid da ke samar da neural tube, waɗanda su ne ke haɓaka ƙwaƙwalwar jariran da ba a haifa ba tukunna.

 

Wannan dalili ya sa masana harkokin lafiya ke son masu ciki su dinga amfani da ita daidai gwargwado.

 

10 – Amfani wajen kaurara kayayyaki

Kazalika, ‘yan kasuwa da ke sayar da kayyayyakin da ake ci kan yi amfani da daddawa ko kalwa wajen haɗa abubuwa don su yi kauri.

Illolin istimna’i (masturbation) ga ma’aurata da hanyoyin guje:

 

Biyawa kai bukata ta hanyar istimna’i wato masturbation da turanci, ko kuwa “istimna’i” din da harshen larabci, yana nufin duk wata hanya da mutum zai bi don ya samarwa kanshi biyan bukata wato zubar da maniyyi ba tare da saduwa tsakanin jinsin mace da na miji ba.

 

Tarihi ya nuna cewa masturbation ya samo asali ne tun zamanin annabtan Annabi Luth (Lud), lokacin da jama’an wancan lokacin suka shiga cikin bala’in luwadi a tsakanin su, Matsalar da ta zama ruwan dare game duniya tsakanin mata da maza marasa aure wani lokacin ma harda masu auren.

 

Masana a fannin kiwo lafiya a mataki daban-daban sun sha gwagwarmaya wajen yakar wannan dabi’a a tsakanin al’umma lura da iri-iren illolin da wannan al’ada ke tattare dashi ga zamantakewar ma’aurata da kuma lafiyar su.

 

A likitance masana sun bayyana cewa istisma’i ba za’a kira shi da suna ciwo ba, haka kuma babu takamammen maganin da zai kawar da wannan al’amari kai tsaye illa canza ko sauya tunanin jama’a musamman wadanda suka rigaya suka afka cikin wannan dabi’ar. A bisa kula da illolin da wannan al’adar zai iya yi ga rayuwar bil’adama, masanan sun bayyana wasu daga cikin illolinsa, bayan ga haramcinsa a addinin Musulunci da ma na Kiristanci, da dama kamar haka:

 

Iillar istimna’i ga lafiyar bil’adama

 

Masana a fannin kiwo lafiya sun bayyana cewa, duk sanda bil’adama ya fitar da maniyyi, wahalar da jiki kan yi na dai-dai da gudun kilometer 13 (13km) wasu na iya wannan dabi’ar sau 3 ko fiye da haka a wuni, kunga a nan dole matsaloli su biyo baya kamar ciwon jiki da shanyewar hannaye da kuma rama da rashin kuzari. A bisa wannan dai masanan sun tabbatar da wannan dabi’ar na ruguza daukacin tsarin jikin bil’adama.

 

Masanan har ila yau, sun bayyana cewa wannan dabi’ar kan jawo ciwon zuciya ga mai yin ta. Ya kan jawo rashin karfin gaba. Duk mai wannan dabi’ar yau da gobe zai rasa karfin gabanshi kwata-kwata. Har ila yau an tabbatar da cewa duk mai dabi’ar lallai ne sai ya kamu da cutar sanyin mara (gonorrhea) wanda kan iya illanta shi.

 

Illoin istimna’i ga zamantakewar ma’aurata

 

Yana iya haifar da kiyayya da zargi tsakanin mata da miji. Duk ma’auratan da daya daga cikin su ke wannan dabi’ar to tabbas ba zai iya gamsar da daya ba ta hanyar jima’i. Misali, idan miji ya fita aiki yabar matar shi gida sai tayi istisma’i, idan ya dawo aiki yana bukatar ta da jima’i, ba zata kulashi ba saboda ita ta riga ta zubar da sha’awarta, hakazalika na mijin. Kuma ko da jima’i ya kasance tsakani, to za’a samu matsalar rashin jin dadin saduwa saboda waccan dabi’ar ta gusar da sha’awar aboki ko abokiyar saduwa.

 

Masana sun kara bayyana cewa wanna dabi’ar a bisa binciken su kan iya hana haihuwa. Ya tabbata cewa namiji ba zai iya samar da ciki ba har sai an samu kashi 60 zuwa 70 cikin dari na yayan maniyyi, wanda kuma yayan maniyyin ba zasu kammala hakan ba sai mutun ya kasance lafiyayye kuma mai kuzari. Wanda duk mai wannan dabi’ar ana iya samun shi ko samun ta da karancin kuzari wanda hakan na iya hana su haihuwa.

 

Shawara ta yadda za’a iya gujewa dabi’ar istmna’i

 

Da farko in mutun ya tsinci kanshi cikin wannan dabi’ar kuma yana bukatar dainawa, to, sai ya kudurta a cikinn zuciyarsa cewa zai daina sabili da dabi’ar na da makutar wuyar dainawa muddin ta yi wa mutun katutu.

 

Mutum yayi kokarin aure idan da hali

Ka daina kadaita a dakinka ko gidanka, ka rika shiga mutane dan mafiyawa kadaita ke sa wasu mutane wannan dabi’ar.

 

A guji shan kwayar da zata tada sha’awar jima’i.

 

A guji yawan kallon ababen da zai tada sha’awa, hoto ko bidiyo, kana a guji yawan zantutukan batsa.

 

A yawaita jin karatu ko wa’azi a ko da yaushe.

 

Idan aka kiyaye wadannan abubuwa, in Allah ya yarda mai dabi’ar zai iya dainawa. Allah Ya sa mu dace.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button