Mutane sun shiga jimami da dimuwa bayan da wata Amarya mai suna Hauwa ta rasu washe garin Auren ta

 Bayan daura auren wata matashiyar budurwa mai suna Hauwa Abdullahi Shehu wacce aka fi sanin ta da Ummi, tare da Angon nata mai suna ASP Abdulmuhyi Bagel Garba a ranar Asabat biyar 5 ga wannan watan da muke ciki na Fabrairu, sai Allah ya karbi ran Amaryar mai suna Hauwa Abdullahi Shehu.

Kamar yadda shafin mr_mrs arewa dake kan dandalin sada zumunta na instagram ya wallafa hoton Amaryar tare da Angon nata, da kuma labarin mutuwar Amaryar Hauwa Abdullahi Shehu kamar haka.

Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun: Feb 5th Dan Allah ku karbi wannan a matsayin jan hankali don yiwa Ummi addu’a. Allahumma gafirlaha warhamha waafiha wa’afu’anha” Allah ya yafe mata kura kuranta sannan ya bata jannah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button