Na Rantse Da Allah Zan Iya Bawa Rarara Kyautar Naira Miliyan 150, Naziru Sarkin Yayi Zazzafan Raddin Zuwaga Dauda Kahutu Rarara Kalli Cikakken Videon

Na Rantse Da Allah Zan Iya Bawa Rarara Kyautar Naira Miliyan 150, Naziru Sarkin Yayi Zazzafan Raddin Zuwaga Dauda Kahutu Rarara Kalli Cikakken Videon
Yadda Za’ayi Maganin Olsa (Ulcer) Komai tsananinta. Da izinin Allah
Olsa (Ulcer) cuta ce dakan addabi Al’ummar wannan zamani da muke ciki wanda zaka samu yawanci ana ɗauke da ita, wanda wasu mutanen sun san ita ke damunsu wasu kuma basu sani ba.
Akwai alamomin da olsa (Ulcer) take dashi dayawa wanda wasu da dama basu san cewa itake damunsu ba. Don haka Zamu kawo wasu daga cikin alamomin cutar Olsa (Ulcer) kamar haka:
Ciwon Ciki,Amai mai tsami,Jiki ya Dinga Rawa Idan Kanajin Yunwa,
Rashin Son Cin abinci,Yawan yin Gyatsa,Ciwon Ƙirji,Kashin Jini,Ramewa,Kasalar Jiki,Zafin Ƙirji.
Dadai sauransu domin akwai wasu alamominta da dama
Yadda Za’a Magance ta.
Ga masu Olsar dabata zama Chronic ba wanda sukeji zafin ƙirji ko ciwon ciki.
Zasu nemi Ayaba mai kyau babba guda ɗaya idan kuma ƙarama aka samu guda biyu sai ayi blending dinta ko kuma a kirɓa ta sosai Sai a samu madarar ruwa kota gari kowacce iri saiku haɗa Ayaba da madara kamar cikin kofi guda sai a dinga sha da safe kafin aci abinci, bayan kayi kamar mintuna 30 dasha sai kuci abincin ku. Sai kuma kofi guda bayan anci abincin dare.
In Allah ya yarda wannan Ciwo zai warke da yardar Allah.
SAI KUMA MASU BABBAR OLSA (ULCER) WATO CHRONIC.
Zaku Nemi:
Habbatussauda,Garin Magarya.
Habbatussauda
Zaku nemi Habbatussauda mai kyau a kasuwa, zaku dakata sosai tazama gari, saiku kawo garin Magarya a haɗa a dinga tafasa a saka zuma a ciki a dinga sha Safe, Rana da kuma dare.
Shima wannan Indai an maida hankali da yinsa to Insha Allahu za’a rabu da ita. Da izinin Allah
Allah yabada sa a
Kuma Ina ganin fatan alkairin da ake yi mun kuma ina godiya Allah yabar zumunci
Ni Fatana arayiwa itace na taimaki bayin Allah dake fama da lalura ajikinsu amma basu San magungunan da zasuyi domin rabuwa da wannan ciwoba’
Kuma addu a ta itace Allah yasa dukkan Wanda na dau magani nabasa” ko nayi bayanin maganin ya dauka ya aikata’ Allah yasa karshen wahalarsa kenan”
Allah yasa mudace
Malam Aminu
SAKONNIN SOYAYYA NA BARKA DA SHAN RUWA
MATA .
1} Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan ka
sha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu
nutsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta
gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka sha ruwa lafiya? Ka Huta Lafiya.
2} A dukkan lokacin da na ga daren
Lailatilkadari, zan kasance mai rokon
Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin
mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma
zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar
burinmu? Ina Son Ka.
3} A lokuta da wurare daban-daban ina
ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a
buɗe. Ba na iya yin komai ba tare da
tinaninka ba. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya.
4} Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan
lokacin da idanuwana ke kasancewa a
buɗe. Barka Da Shan-ruwa.
5} Irin kulawar da kake nuna min a
kullum na saka ni tinanin irin yadda
rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zanbzamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.
6} Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin
da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taɓa yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Hutawa.
7} Da a ce zan iya zama komai, da na
zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman
kumatunka, na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da
Shan-ruwa.
8} A dukkan lokacin da kake bukatar
wani ya taya ka hira, karda ka manta
kana da ni, ka nemo ni domin ɗebe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Ka Wuni Lafiya? Yaya
Ibada?
9} A lokacin da na tino irin rayuwar da
na yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaɗai ba tare da kai ba , yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada. Barka Da Shan-ruwa.
10} Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka. Barka Da Hutawa. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya?