Rai Bakwon Duniya Anyi Jana’izar Ibrahim Abdulkharim daya Rasa Rayuwar Sa a Hadarin Mota Allah Sarki…

Rai Bakwon Duniya Anyi Jana’izar Ibrahim Abdulkharim daya Rasa Rayuwar Sa a Hadarin Mota Allah Sarki…
Aƙalla dai an tabbatar da kisan mutum 22 tare da jikkata wasu da dama, a mummunan harin da zugar ‘yan bindiga su ka kai ƙauyen Majifa, cikin Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara a Jihar Katsina.
Mummunan al’amarin dai ya faru ne ranar Asabar ƙarfe 4 na Asubahi.
Majiyoyi da dama sun tabbatar wa wakilin mu cewa maharan na kan hanyar su ta komawa cikin dazukan da su ka fito ne, bayan sun halarci bukin auren wani hatsabibin ɗan bindiga, wanda ake wa laƙabi da Mai Katifar Mutuwa.
Mai Katifar Mutuwa dai ya yi auren matar sa ta biyu ne a yankin.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa ya tabbatar wa wakilin mu da afkuwar kisan, sai dai ya ce zuwa lokacin da ake haɗa labarin ba shi da cikakken bayanin adadin mutanen da aka kashe.
“Abin da mu ka sani dai a yanzu shi ne ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Majifa. Maharan daga Jihar Zamfara su ka je bukin auren wani gogarman ‘yan bindiga, amma daga can sai su ka afka cikin ƙauyen Majifa.”
Isa ya ce sun kuma ji labarin cewa an sace shanu a harin.
PREMIUM TIMES ta ji daga bakin wasu jami’an tsaro cewa gogarman ‘yan bindigar da ya angwancen ne ya aika da goron gayyata ta gungu-gungun ‘yan ta’addar da ke cikin dajin Zurmi da na dajin Tsafe a cikin Jihar Zamfara, ya gayyace su shagalin bikin da aka kashe dare ana gwangwajewa.
Wani ɗan yankin ƙauyen da mu ka sakaya sunan sa da ke zaune a Ɗanmarke, ya ce ƙauye ɗaya kaɗai maharan su ka shiga. “Sauran ‘yan wasu garuruwa da aka kashe ko aka jikkata kuma sun je yin ceto ne Majifa daga ƙauyukan su, mahara su ka yi masu kwanton ɓauna, su ka karkashe su.
“Wato wajen ƙarfe 4 na Asubahi mu ka riƙa ganin mahara kan babura su na tunkarar dajin Lamba, wanda ba shi da nisa da Majifa. Daga nan mu ka gane cewa ashe Mai Katifa ne ke shagalin auren wata Bafulana da ya yi a cikin wata rugar da ke dajin Lamba.
“Ka san idan ‘yan bindiga na bukin su, su ka cake ko su bugu su riƙa yin abin da su ke so. Daga nan ne su ka afka ƙauyen Majifa, su ka fara harbin jama’a. ‘Yan bangar cikin ƙauyen sun yi ƙoƙarin kare garin.”
Ya ce mahara sun kashe mutum 17 ‘yan Majifa, wasu da dama kuma sun samu raunuka.
“Sauran da aka kashe ɗin kuma ‘yan banga ne da su ka kai ɗauki daga ƙauyukan da ke maƙautaka da Majifa, waɗanda su ka je daga nan Ɗanmarke, Gurbi, Maƙera, Unguwar Sale da Ɗan Mangwaro.” Inji shi.
Wani shi ma ya shaida wa wakilin mu cewa ya ƙirga gawarwaki 17 a Asibitin Ƙanƙara.
Tuni dai zaɓaɓɓen Sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdul’aziz ‘Yar’Adua ya yi tir da wannan mummunan ta’addanci.