Saurayi ya gudu ya bar Budurwa da kawayenta bayan sun ci abincin dubu 223.

Saurayi ya gudu ya bar Budurwa da kawayenta bayan sun ci abincin dubu 223.

Budurwar mai suna Siyama Ibrahim ta ce bata taɓa tsammanin Abdul zai gudu ya barsu a kan ₦223,000 ba inda tace “a lokacin da suna cikin mota kan hanyar su ta zuwa Restaurant ɗin har waya yake yi da abokinsa a kan yace ya tura masa miliyan 2 da rabi amma ya turo masa 1.3million” yayin da shima a nashi ɓangare Abdul ɗin ya ce ai ba suyi da ita zata taho da ƙawayenta ta

 

TA YAYA SAURAYI YAKE IYA MALLAKE ZUCIYAR MACE HAR YA IYA YI MATA WASA DA HANKALI? (001)

 

 

 

 

Wannan wata tambaya ce da nake yawan tambayar kaina, musammam idan naji ko na karanta labarin wata ‘ya mace da ta aikata wani abu na Assha, wanda a karshe sai na samu cewa tare da son ranta ta bawa wannan saurayi dama har ya aikata abinda ya aikata da ita.

 

 

 

 

Meye dalilan da suka jawo idanuwan wannan tarinya suka rufe har ta yadda da wannan saurayi ta sallama masa kanta?

 

 

 

 

Ya akai wannan yarda har takai cewa zata iya magana dashi tamkar cewa an daura musu Aure bayan ko saninsa iyayenta basuyi ba?

 

 

 

 

Ya akai ita da kanta zata ketawa kanta mutunci ta iya turawa wani saurayi wanda babu wata alaka tsakaninsu hotunan surar tsiraicin jikinta?

 

 

 

 

Inda gizo ke sakar shine ya za’ai har ta dimauce ta bashi dama ta yadda har ya keta mata Haddinta Tamkar an daura musu Aure?

 

 

 

 

Wannan kadanne daga irin tambayoyin da nakewa kaina idan naji irin wannan labari, Ina hankalin wannan yarinya yake? Ya za’ai ta amince wani ya lalata mata rayuwa bisa yardarta, don kawai La’alla ya mata Al’kawarin Aure?.

 

 

 

 

Tambaya mafi muhimmanci Shine ya akai wannan Saurayi ya mallake zuciyarta har idanuwanta suka rufe har ta Sallama masa kanta da yardarta, ta manta da Abin kunyar da zata aikata tun a duniya kafin aje lahira? Ta manta da cewa wannan Alakar tanada sakamako mafi kankantarsa shine daukar cikin shege, kokuma tama rasa miji tsawon rayuwarta, don babu namijin kirkin da zai auri macen da take Bazawara ce Alhalin bata taba yin Aure ba.

 

 

 

 

Wannan wani dan takaitacccen rubutu ne zan dinga yi kullum akalla sau daya la’alla ya taimaka wajen rufe wata babbar kafa ta lalacewar tarbiyya da ya fara yaduwa a cikin Al’ummarmu ta hausawa, babban abinda ya ja hankalina shine irin wadannan abubuwa da suke faruwa munajin labarinsu ba komai bane face karshen labarin, wato akwai abubuwa da yawa da suke faruwa kafin a kawo nan din wanda mu karshen kawai muke ji, babu yanda za’ayi a gyara matsala kuwa face an kamota tun daga jijiyarta, domin tabbas akwai dalilan da suke sakawa mace mai hankali ta fada irin wannan mummunar hanya.

 

 

 

 

Abubuwan da rubutun ya Qunsa sune:

 

 

 

 

(1) Gabatarwa.

 

(2) Ya Namiji ya dauki mace, Sannan ya Mace ta dauki namiji.

 

(3) Wasu daga cikin Matsalolin da mace take fama dasu musamman yan kasa da shekara 20: (Damuwa, Rasa wanda zai saurari matsalolinta, Samun tausayawa ta gaskiya, Rasa soyayyar uwa, Rashin mai fahimtarta).

 

(4) Hanyoyin da Samari suke bi wajen wasa da hankalin mace.

 

(5) Ta yaya mace zata kaucewa fadawa irin Wannan Haramtacciyar dangantaka?

 

(6) Shawara gareku iyaye.

 

(7) Kuskuren iyaye wajen tarbiyyar ‘yayansu musammaman mata.

 

(8) Wasu Ababe masu Alaka da wannan (duk girman laifin da kike aikatawa barinsa yafi cigaba. Dinyar makaho ta nuna a hannunsa. Soyayyar wahami. Ta yaya zan iya rabuwa dashi?. Aure lokacine da rabo ammafa…

 

(9) Rufewa.

 

 

 

 

Allah ya kiyaye ‘yan matanmu da samarinmu daga afkawa cikin halaka, Allah ya bamu ikon Kammalawa kamar yanda muka fara Allah ya amfanar damu da Al’ummar musulmi baki daya.

 

 

 

 

Gabatarwa:

 

 

 

 

Soyayya Tsakanin mace da na miji a musulunci Iri biyu ce: Na farko shine halastacciyar soyayya, Kamar irin son da mutum yakewa mahaifiyarsa ko Kanwarsa ko matarsa, haka itama mace ga mahaifinta ko yayanta ko mijinta, na biyu shine Haramtacciyar soyayya, wannan itace soyayyar da take tsakanin mace da namiji wadanda babu wata alaka ta halal tsakaninsu wanda muke kira (Saurayi da budurwa).

 

 

 

 

A soyayya ta farko babu wata matsala ko hatsari a ciki domin soyayya ce ingantacciya wanda babu abin tsoro a ciki, Inda matsalar take shine ta biyun inda zaka samu mace da na miji suna soyayya wanda babu wata alaka data halatta musu wannan soyayyar, Sannan shi saurayi a cikin irin wannan soyayya daidai yake da mafaraucin da yake kirkirar dabaru kala kala da zasu bashi damar kama abinda yake hari, Shine abinda Saurayi yakeyi ta hanyar waya, chatting, haduwar makaranta, Jami’a da dai sauransu.

 

 

 

 

Abinda zamu lura dashi shine mafi yawan irin wannan Soyayya amfanin yarinyar shine ta biya masa bukatarsa sannan a karshe ya rabu da ita ya nemi wata.

 

 

 

 

Babban abinda mace bata sani ba dangane da namiji shine Namiji yasha banban da ita, yanda yake tunani ba haka ita takeyi ba, Daga cikin banbancin: ba namijin da zai yarda ya Auri macen ta zama ragowar wani, koda kuwa shine wannan wanin, domin tunaninsa shine tunda har ta yarda ta aikata haram dashi mai zai hana ta aikata da wani nan gaba?.

 

 

 

 

Sannan yanada kyau mu sani cewa mace fa mace ce, Duk garin da ta fito, ko kalarta, ko iliminta, ko addininta, Domin magana muke akan Dabi’ar mace a matsayinta na mace da yanda take tunani, domin Dabi’ar mace shine Zuciyarta tanada taushi sosai, wanda sau da dama tana amfani da wannan taushin zuciyar wajen yin hukunci akan abubuwa, Sannan tanada saurin tasirantuwa da abu, Wannan raunin zuciyar yasa a koda yaushe take bukatuwa zuwa ga wanda zai tallafeta ya kasance a tare da ita lokacin da take cikin wata bukata, shi isa idan mace ta fada soyayya ta gaske tana rasa hankalinta ne gaba daya sai ta zama kamar abinwasa a hannun wannan saurayi, Har ya iya kaiwa ta bashi duk wani da zai iya bukata ba tare da tunanin abinda zai iya kaiwa ya komo ba a karshe.

 

 

 

 

Wadananna dabi’u na mace masu kyau ne, kuma marasa kyau a lokaci guda, Sannan ana iya samun banbanci tsakanin su kansu matan wasu sunfi wasu, Amma a karshe dai irin wannan siffofin Sunfi yawa a wajen mace fiye da namiji.

 

 

 

 

Sannan kafin mu fara inaso nayi wani dan Tambihi kadan: A cikin wannan Silsilar rubutun Idan nace samari ba wai duka nake nufi ba, Ina magana ne akan mayaudara masu wasa da hankalin ‘yan mata, da mugun nufi, ragowar samari kuwa maganata ba A kansu take ba.

 

 

 

 

(1) TUNANIN NAMIJI AKAN MACE DA TUNANIN MACE AKAN NAMIJI

 

 

 

 

Lokacin da saurayi (mayaudari) yake kokarin fara soyayya da mace Yana kallonta ne a matsayin wata hanyar Jin dadi, wato kallo na sha’awa, yayinda ita kuma take kallonsa a matsayin wani tushe da zata samu soyayya da kauna da kulawa.

 

 

 

 

Ita soyayya take nema, yayinda shikuma sha’awace a ransa, tunaninta yafi rinjaye ta bangaren taushin zuciyarta da rauninta, yayinda shikuma da hankalinsa yake amfani wajen yin wasa da nata, La’alla za’a iya samun wani abu na soyayya a ransa, haka itama za’a iya samun wani abu na sha’awa aranta amma dai wancan shine galibi.

 

 

 

 

Sannan zai iya yiwuwa shi din tabbas Ya fara soyayyar ne da niyyar ya aureta, amma mafi yawa dai shine wancan da na fadi, domin soyayya ce da aka ginata akan kuskure don Addininmu ba haka ya gaya mana ake neman aure ba, kuma a karshe ita macen itace babbar wadda zatayi Asara.

 

 

 

 

Domin in ka kalli irin wadannan labari da suke faruwa, zaka samu cewa da zarar ya gama biyan bukatarsa da ita zai rabu da ita ya nemi wata, don baze yarda ya aureta ba, A yayinda ita kuma Abar tausayi zata cigaba da sonsa da tuna alkawuran da yai mata na Aure.

 

 

 

 

Mu sani cewa mace bahaushiya kuma musulma duk inda take hanya ta farko da take fassara soyayya shine aure, ba zata taba yarda da zama ‘yar tsanar wani ba da zaiyi wasa da ita sanda yaga dama ya jefar sanda yaga dama, shi isa zakuga cewa koda yaushe ita maganarta shine aure haihuwar ‘yaya gina family Da kullum take buri, Shikuma baya son dorawa kansa nauyin auren gwara su cigaba a haka ya gama abinda zaiyi ya rabu da ita, (dukda suma matan wani lokacin akan samu masu biyewa abun duniya) amma dai wannan shine mafi yawa.

 

 

 

 

Mu hadu A rubutu na gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button