Shekara 7 Na Yi Ina Rubuta Waƙar Da Na Yiwa Manzon Allah — Alan Waƙa

Shekara 7 Na Yi Ina Rubuta Waƙar Da Na Yiwa Manzon Allah — Alan Waƙa

DAREN LAILATUL QADAR.

 

Daga Mustapha Musa Abu Aisha.

 

Daren lailatul Qadr ya fi watanni dubu wanda ba wannan daren a cikinsa alheri,haka Qur’ani ya bayyana alherinsa ya fi na shekara tamanin da wata hudu.

 

*Me Ya Sa Aka Kira Shi

Da Lailatul Qadri??*

 

1–An ce,saboda girmamawa (saboda kalmar Qadru a larabci tana nifin girma) kamar fadin Allah Madaukakin Sarki:

(Ba su girmama Allah iyakar girmamawa ba).

@Al-An’am : 91

 

Abin da ake nufi, wannan dare ne mai girma,saboda Alqura’ni ya sauka a cikinsa,da kuma abin da yake faruwa na saukar Mala’iku da Albarka da Rahama da gafara a cikinsa”

 

Hadisai sun zo suna bayanin samun wannan dare a cikin watan Ramadana ne.

Sunna ta tabbatar kamar yadda Allah ya ce; [139]

 

2–Wasu kuma suka ce, Alqadru,yana nufin quntatawa, kamar yadda Allah ya yi amfani da wannan kalmar da wannan ma’ana inda yake cewa:

(Wanda aka quntatawa arzikinsa ya ciyar daga abin da Allah ya ba shi).

@Addhaalaq:7

 

Abin da ake nufi da quntatawa a cikin wannan dare, shi ne boye daren da aka yi, ba a bayyana shi ba.

 

3–Wasu suka ce,”Alqadru a nan,yana da ma’anar“Alqadaru” wato qaddara,saboda abin da ake qaddara wa na shekara cikin wannan dare,don Allah Madaukakin Sarki ya ce:

(A cikin wannan dare ne ake rarrabe dukkan wani lamari hukuntacce)

@Addukhan

 

An kabo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi–a ce, (Daren Lailatul Qadari shi ne daren ashirin da bakwai ko ishirin da tara.Mala’iku a wannan daren sun fi yawan tsakuwa a bayan qasa)

@Ibn Khuzaima ne ya

rawaito shi]

 

4–Dare Mai Aminci A Cikinsa Allah Mai Girma Da Buwaya ya ce,

(Aminci ne a cikinta har zuwa bullowar alfijir)

@Alqadri:5

 

Ma’ana dukkan wannan dare alheri ne,babu wani sharri a cikinsa tun daga farkonsa har zuwa bullowar alfijir.

 

5–Dare Ne Mai Albarka Allah ya ce;

(Haqiqa mun saukar da shi a cikin dare mai albarka.Haqiqa mu masu gargadi ne). @Addukhan:3.

 

Abdullahi Dan Abbas ya ce, “Yana nufin daren lailatul Qadri”.

 

6–A Cikinsa Ake Qaddara Dukkan Abubuwan Shekara Allah ya ce:

(A cikinsa ake rarrabe kowanne lamari abin hukuntawa)

@Addukhan:4

 

7–Wanda Ya Yi Qiyamullaili Yana Mai Imani Da Neman Lada To Za A Gafarta Masa Abin Da Ya Gabata Na Zunubinsa Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ce,;

(Wanda duk ya yi tsayuwar daren Lailatul Qadri yana mai imani da neman lada,an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa)

@Bukhari da Muslim ne sukarawaitoshi.

 

FALALAR DAREN LAILATUL QADRI

 

1-Allah ya saukar da Qur’ani a daren.

 

2-Allah ya girmama sha’anin daren.

 

3-Mala’iku na sauka a wannan dare da rahama da albarka da natsuwa.

 

4-Akwai gafarar zunubai.

 

5-Aminci da salama na sauka ga masu imani.

 

6-Ibada a wannan dare ta fi ibadar wata dubu a wani dare wanda ba wannan daren ba.

 

7-Daren ya fi wata dubu.

 

8-babu mai rasata sai marashin albarka.

 

9-kashe garin daren rana

kan fito

 

Allah ne mafi sani

 

Share this:

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button