Shin Ka San Ƙasar Da Babu Gwamnati Ba Shugaban Ƙasa, ba firaminista Ba Sarki Ko Sarauniya?

Shin Ka San Ƙasar Da Babu Gwamnati Ba Shugaban Ƙasa, ba firaminista Ba Sarki Ko Sarauniya?
Wannan Ƙasar tana wajen da ya ke da yanayi na zubar ƙanƙara,
Sunan Wannan ƙasa ANTARCTICA.
Ƙasar ANTARCTICA itace ƙasar da ta fi kowacce ƙasa SANYI a cikin wannan Duniyar ta “Earth”,
Yanayin ƙasar (Temperature) ya na zuwa har ƙasa da -130 a ma’aunin Fahrenheit Wanda ya ke daidai da -90 a ma’aunin Celsius,
Ƙasar ta na da manyan duwatsu ma su aman wuta wanda ake kira da Volacano a turance.
AGOGO ba a buqatarsa a ƙasar ANTARCTICA domin ana đaukan tsawon watanni shida cikin yini ba tare da rana ta fađi ba, haka ana đaukan tsawon watanni shida cikin duhu ba rana.
Akwai wani ƙaton dutsen ƙanƙara a ƙasar wanda Akwai dokoki ma su tsauri akansa, domin akwai wasu guraren da aka ware a bakin iyakar wannan dutsen ƙanƙarar duk Wanda ya ƙetarasu ana iya cin tararsa ta kuđi har kwatankwacin Naira Miliyan Bakwai,
Ha ka idan ka đauki wani abu daga wajen wannan dutsen ƙanƙarar komin ƙanƙatarsa ko da dutse ne ana iya đaureka har tsawon shekara guda a gidan yari.
Wannan Ƙasar ba ta da shugaban ƙasa domin ta hađa yankuna na qasashe har guda bakwai, sune Kamar haka; France, Argentina, Chile, Australia, New Zealand, Norway da UK, dukkan wannan ƙasashen guda bakwai suna da mallakin wani yanki a wannan ƙasar ta Australia.
Haka akwai wasu ƙasashen irin su America, Brazil, Peru da Russia da su ke da burin mallakar wani yanki a wannan ƙasar ta ANTARCTICA sabo da tsammanin qasar tana da albarkatun ma’adanan ƙasa na Mai (oil).
Dukkan kowacce ɗaya daga cikin wađannan ƙasashen ta na so ƙasar ANTARCTICA ta zama mallakinta, Wanda hakan ne ya sa kowacce ƙasa daga cikinsu ta ke fito da wasu tsare-tsare da salo domin ganin ta mallaki wannan Ƙasar ta ANTARCTICA,
Misali; ƙasar ARGENTINA ta đauki Mace mai cikin wata bakwai ta kai ta ƙasar ANTARCTICA domin ta haihu acan, hakan yana nufin Mutum na farko da za a haifa a ƙasar ANTARCTICA ya kasance đan asalin ƙasar Argentina ne,
Haka ƙasar Germany ta je da nata tsarin ya yin da ta aika da jirage inda su ke watsa Tuta mai tambarin qasar Germany.
Har yau kowacce đaya daga cikin wađannan qasashen ta na ta qoqarin ganin ta mallaki wannan qasa ta ANTARCTICA, Amma kuma duk da haka sun amince da su bawa wannan qasa ta ANTARCTICA kariya