Shin Ka San Ka Na Iya Sayan Data har 1GB A Layinka Na MTN Ba Tare Da Kuđi Ba?

 

Shin Ka San Ka Na Iya Sayan Data har 1GB Ba  Tare Da Kuđi Ba?

Da yawa zasuyi mamakin hakan amma kuma abu ne mai yiwuwa, amma ta ya ya  hakan zai yiwu?

Da yawa na san ba lalle sun san menene MTN PULSE POINts ba shi yasa zasuyi mamakin cewa za su iya sayan Data ba tare da Airtime ba, ba iya Data kađai ba har Instagram Bundle, Tiktok Bundle duk kana iya saya da Pulse Points.


MTN PULSE POINT wani point ne da MTN suke bada kyautarsa ga wanda suke kan tsarin MTN PULSE yayin da suka sayi DATA ko kuma Sukayi NIGHT SUB ko MUSIC TIME.  

Da yawa ana basu wannan point din ba tare da sun sani ba, 

Wasu kuma ana basu kyautar point din amma kuma ba su san wajen da zasuyi amfani da shi ba wasu kuma ba su san yadda za su duba yawan point din da aka basu ba,

Ni kai na mai rubutun ina daga cikin wanda ake bawa Point din kuma ina gainsa amma kuma ban san yadda zan dubashi ba ko kuma nayi amfani da shi ba duk da wani lokacin idan zan sayi Data suna tambaya na da me nake son sayan Data,  Da Airtime ko kuma Pulse Point Amma kuma ban ta6a gwadawa da Pulse Point din ba sai yau. 


kamar yadda nayi bayani a sama ana samun Pulse Point din ta hanyar sayan Data ne ko kuma Night Sub ko Music Time,

Akwai abubuwa masu muhimmanci game da PULSE POINT wanda yana da kyau ka san su, Wađannan abubuwa ga bayanansu nan a qasa:-

Darajar Pulse Point :- Kowanne Pulse Point Yana daidai da Naira đaya ne wato N1, Sabo da haka idan kana da 50 Pulse Point kana iya sayan Data har adadin 500MB a night Sub ko kuma 40MB na normal Data Bundle. 

Yadda Za Ka Duba Adadin Yawan Pulse Point Da Ka Ke Da Shi :- Idan kana so ka duba adadin yawan Pulse Point da kake da shi zakayi amfani da wannan Code din wato za ka danna wannan lambobin *406*7#.

Zai nuna maka wannan shafin da ke qasa:-


  • Redeem Data Bundle:- nan ne za ka shiga domin yin amfani da Pulse point dinka domin sayan Data.
  • Redeem NightLife Bundle :- nan ne za ka shiga domin yin amfani da Pulse point ka yi NightLife Bundle wato Night Sub.
  • IG and TIkTOK Bundles:- nan za ka shiga domin yin amfani da Pulse point ka sayi Instagram ko Tiktok Bundle.
  • Pulse Point Balance:- Shine za ka shiga domin duba adadin yawan pulse point da kake da shi. 
  • About Pulse Point:- Nan ne za ka samu bayanin yadda za ka samu kyautar pulse point wanda munyi bayaninsa a sama.
  • Expiration:- Ma’ana lokacin da pulse point yake đauka kafin ya lalace; Pulse point yana expire duk qarshen wata ne. 
  • Duk lokacin da ka yi NightLife Sub na N25 za ka samu 1.25 Pulse point ne ko kuma 2.50 akan NightLife Sub na N50.
  • Haka duk lokaci da ka yi amfani da *131* domin sayan Data ko *406# domin yin NightLife Sub za ka zo matakin da za su tambayeka da me kake son sayan Data? Da Airtime ko Pulse Points kamar yadda yake a qasa cikin hoto. 


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button