Subhalallah Wayyanar Wannan Bidiyon Ya Tada Hankalin Al’umma

Subhalallah Wayyanar Wannan Bidiyon Ya Tada Hankalin Al’umma

MATA KE TILASTAWA MAZA WASA DA AL’AURA

 

Dalili daya ne dani wanda ya tabbatar mini da matan yanzu ke jefa maza cikin bala’in istimna’i wato wasa da al’aura.

Ga dalili na;

Yanzu Allah kawo mu zamanin da kaso 80 cikin dari na samari basa iya diban awoyi batare da sun shiga shafukan sada zumunta ba kamar Facebook, Instagram da sauran su.

 

Kuma a wannan lokaci yan matan hausawa sunyi qaurin suna wajen wallafa hotuna masu saurin daukan hankalin namiji da tayar mishi da sha’awa, zakuga duk wani waje da namiji yafi sha’awa ajikin mace anfi dame wajen kokuma bayyana shi qarara.

 

Hakan tasa maza da dama marasa aure ke zina da irin wadannan hotunan wato instimna’i zinar hannu don korewa kansu sha’awa.

 

Hakika duk wacce ta wallafa irin wannan hoton da ke bayyana wani shashi da namiji zai gani sha’awar sa ta tashi to lallai tsinanniya ce a wajen Allah.

 

Domin Allah ya tsinewa mata masu bayyana tsiraici.

 

Shawara ga samari.

 

Dole ku kiyaye ganin ku, sannan ku guji irin wadannan shafukan, domin duk mai aikata istimna’i hakika yana aikata babban zunubi. Sannan akwai illoli masu tarin yawa dake tartare da wannan dabi’a.

 

Allah ya karemu.

NA KASA DAINA WASA DA AL’AURA (MASTURBATION)

Hanyoyin Rabuwa Da Wasa Da Al’aura.

 

Kada shaidan ya hana ka sharing zuwa ga groups.

 

Hakika matsalar Istimna’i (wato Masturbation) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA. Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu’a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah azuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.

 

Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba’ira bane!!

 

Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala’in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.

 

Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa, to hakanan shima Istimna’i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa.

 

Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna’i, da sauransu.

 

Kamar yadda muka sha fada, Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala’in sun hada da:

 

1. Nisantar duk wani hoto ko Video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)

 

2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.

 

3. Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.

 

4. Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.

 

5. Ka dena zama kai kadai acikin daki in dai ba ibada kake yi ba.

 

6. Yawaita karatun Alqur’ani da zikirin Allah. da sauran ayyukan alkhairi.

 

7. Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.

 

8. Tuna Allah ako yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.

 

9. Tuna kusancin ajalinka, fitar ruhinka, kwanciyar Qabarinka, Awun hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.

 

10. Fita daga duk wani Group ko shafi na batsa a Facebook ko Whatsapp wanda suke Qunshe da abubuwan batsa, tare da nisantar Friends masu sharing din irin wannan.

 

WASIKA ZUWA GA MATASA MASU

AIKATA

ISTIMNA’I

ISTIMNA’I = fitar da mani ko sha’awa

da gangan ta

hanyar da bata dace ba.

Matasa Maza da

mata, suna neman taimako akan

illolin da suke

samu ajikkunansu sakamakon

Istimna’i wato

Masturbation.

an kawo hujjoji

gamsassu daga Alqur’ani da Sunnar

Ma’aikin Allah

(saw) da fatawoyin Amintattun

Malamai duk

akan

HARAMCIN ISTIMNA’I.

Amma duk da haka wasu matasan

basu yarda sun

dena ba. Wasu kuwa sunji tsoron

ALLAH sun riga

sun dena.

Babban dalilin da yake janyo musu

afkawa cikin

wannan bala’in shine :

1. Kallon Fina-finan batsa.

2. Shiga shafukan internet na batsa.

3. Yin zantukan batsa tsakanin

saurayi da

budurwa.

4. Kusantar zina ta hanyar kallo da

shafa, ko

zance

da dai sauransu.

Wasu kuma suna aikata hakan ne

don gudun

afkawa ZINA, basu san cewa shi

dinma ZINAR

bane!!

Idan kun Qi bari domin Allah, to ku

dubi irin illolin

da yake haifar muku ajikinku mana!!!

1. MUTUWAR IDANU.

2. MUTUWAR AL’AURA.

3. CIWON BAYA.

4. BUGAWAR QIRJI.

5. RIKICEWAR TUNANI.

6. YAWAN MANTUWA.

7. KARANCIN ‘YA’YAN MANIYYI.

8. SAURIN INZALI.

9. SHAFAR ALJANU, ETC.

Wadannan ‘yan kadan ne daga cikin

Matsalolin da

ISTIMNA’I yake haifarwa. kuma duk

wanda bai

tuba

ya dena ba, idan ya mutu ahaka zai

je ya tarar da

hisabi.

DON GIRMAN ALLAH!! Matasa ku

kiyayi zina da

duk dangoginta. ku kaurace ma duk

wani abinda

zai rika motsa muku sha’awa. Idan

da hali kuje

kuyi aure. idan kuma babu hali, to ku

yawaita

azumi.

ALLAH YA SAWWAKE.

Don Allah ‘Yan uwa MAZA DA MATA,

DON ku taya

mu isar da wannan sakon ta hanyar

Sharing a

FACEBOOK, TWITTER, BBM,

WHATSAPP, da

sauransu. Insha Allahu wasu da

yawa zasu

amfana.

Manzon Allah (saww) yace:

“WALLAHI IDAN

ALLAH

YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA

DALILINKA,

YAFI

ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA

JAJAYEN

RAKUMMA”

Wani mutum yazo wajen manzon Allah S. A.W. ya ce:

.

Yah-manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.

.

1, Yah-manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane?

AMSA,, sai ya ce “Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa.”

.

2, Ina son na zama mafi arziki a cikin mutane?

.

AMSA,, sai ya ce “Ka zama mai wadatar zuci.”

.

3, Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane?

AMSA,, sai ya ce “Ka zama mai amfanarwa.”

.

4, Menene zai kare ni daga wuta?

AMSA,, sai ya ce “Ka zama mai yawan yin Azumi.”

.

5, Ina son na zama mafi adalci a cikin mutane?

.

AMSA,, sai ya ce “Ka so ma dan’uwan ka abin da ka ke so ma kan ka.”

.

6, Ina son na zama mafi amfanin mutane a wajen Allah?

AMSA,, sai ya ce “Ka yawaita tuna Allah.”

.

7, Ina son imanina ya zama ingantacce?

AMSA,, sai ya ce “Ka gyara halayen ka.”

.

8, Menene yake huce fushin Allah S. W .T.?

AMSA,, sai ya ce “Ba da zakka a boye da kyautata wa ya’n uwa.”

.

9, wani zunubi yafi muni awajen Allah?

AMSA,, sai ya ce “Mummunar hali shine rowa”

.

10, Ina son na zama mafi biyayya ga Allah?

AMSA,, sai ya ce “Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah.”

.

YA ALLAH Ka sa mu gama da Duniya lafiya ameeeen

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button