Tofa! Ina Jin Kunya Idan Aka Ambaci Sunana akan Hare-haren ‘Yan Bindiga, Ni fa na Tuba Na Rungumi Zaman Lafiya – In ji Turji. kalli anan

 Tofa! Ina Jin Kunya Idan Aka Ambaci Sunana akan Hare-haren ‘Yan Bindiga, Ni fa na Tuba Na Rungumi Zaman Lafiya – In ji Turji. kalli anan

Shahararren dan fashin nan, Bello Turji, ya yi wa sojojin Najeriya da gwamnatin jihar Zamfara ruwan zafafan kalamai a matsayin martani bayan da wasu jiragen yaki suka yi ruwan bama-bamai a gidansa da ke unguwar Fakai a Shinkafi a jihar Zamfara.

Shugaban ‘yan ta’addan a wata hira da PR Nigeria ta samu a cikin sautin murya, ya zargi gwamnati da karya yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi da shi na dakatar da ‘yan fashi, ta hanyar kare mutanen Shinkafi daga duk wani hari.

Idan za a iya tunawa dai gidan Turji din ya sha luguden wuta kimanin mako guda da ya gabata, inda wasu jiragen yakin NAF guda biyu suka kone gidan kurmus, biyo bayan bayanan da suka samu na ayyukan ta’addanci a yankin, lamarin da ya kai ga kashe ‘yan ta’adda da dama.

A halin da ake ciki kuma, shugaban ‘yan fashin Turji, a cewar rahoton na baya-bayan nan, ya nuna bacin ransa game da farmakin da aka kai ta sama da kuma kashe mutane da yi ma wasu masu rauni.

Ya bayyana cewa ‘yan kungiyarsa suna jin cewa gwamnati ta ci amanar su bayan sun hana kai hare-hare a yankin tsawon watanni biyar da suka gabata.

An karbo daga Turji yana cewa: “Babu wani hari a cikin watanni biyar da suka gabata tun bayan da muka cimma matsaya da gwamnati amma yanzu da sojoji suka kai hari gidanmu, muna jin an ci amananmu musamman bayan mutuwar wasu marasa karfi a hare-haren da jiragen suka kai mana.

Ina jin kunya idan aka ambaci sunana bayan harin da wasu ‘yan fashi da ‘yan ta’adda suke kai wa.

Zaman lafiya babu abinda ya kai shi kima, kuma ni a shirye nake in zama mai neman zaman lafiya, sai dai idan gwamnati ta bukaci in koma ruwa in dauki makamaina na yaki to a shirye nake. Na shirya duka ko dai zaman lafiya ko yaki.

Duk abin da gwamnati take so, za mu iya”.

Menene ra’ayinku akan wannan?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button