Wani Matashi Ya Kutsa Kai Gidan Shugaban Terraform Labs ($LUNA UST)
Wani Matashi Ya Kutsa Kai Gidan Shugaban Terraform Labs ($LUNA UST)
A ranar Litinin, 16 ga Mayu, wani wanda ya saka hannun jari na 2.3 Million Dollars a crypto ya kutsa kai cikin gidan Do Kwon, Shugaban Terraform Labs, Sabo da asarar da tafka ta maqudan kuđađe bayan karyewar $LUNA da UST,
Wanda ake zargin, wanda aka boye sunansa, an ce ya kutsa kai cikin rukunin gidaje da ke gabashin birnin Seoul, sannan ya ci gaba da buga kararrawa Kwon a lokacin da matarsa ke cikin gidan, a cewar wani rahoto da korean outlet Yonhap ta fitar.
A cewar hukumomi, hakan ya faru ne bayan fita ziyarar da Kwon yayi wanda a lokacin matarsa ce karanta rage a gidan, matar KWON ta nemi ‘yan sanda da su kare su daga wata cutarwa da za ta iya faruwa anan gaba.
Kwon ya fada a baya a cikin sakon sa na yanar gizo cewa Terraform Labs yana aiki kan hanyoyin da za a inganta Terra blockchain da duk da fađuwar da $Luna da UST sukayi.
Ga abin da wanda ya kutsa kai gidan KWON shuhaban TERRA LABS yace bayan hukumomi sun masa tambayoyi kan dalilin da ya sa ya kutsa kai gidan shugaban Terraform Labs;
“Na yi asarar kusan Won biliyan 2 zuwa 3 (dalar Amurka miliyan 2.3),”
wanda ake zargin ya shaida wa manema labarai hakan ne lokacin da ake gudanar da bincike a ofishin ‘yan sanda na Seongdong.