Wannan gan ganci ne sune suka kai kansu wajan kadar nan shiga kagani indai yaro ne kai ba sai kashi ba wasa sa rayiwa a fili

Wannan gan ganci ne sune suka kai kansu wajan kadar nan shiga kagani indai yaro ne kai ba sai kashi ba wasa sa rayiwa a fili
‘YAN UWA MAZA KAR KUYI WASA DA WANNAN HADIN
Indai kai na miji ne, ko waye kai, ko kafi kowa kwarewa a aikin Likita, kar ka yadda ka zauna baka yin wannan hadin da kuke gani a hoto
Kullun kai ne cin maggi da kayan dandano a girki, kai ne shan kayan zaki da lemon kwalba mai gas, kasha wannan kasha wancan, zaki ya taru maka a mara, baka motsa jiki, kullun kana cikin shan ruwan sanyi, tafiya nan da can akan abin hawa, a gida sanyin AC, a mota sanyin AC, haka a office sanyin AC ke bugaka, sanyi ya mayar maka da gaba kamar lagwanin fitila, tabbas kana cutar da kanka ne dan uwa, Malam ba zaka taba yin lafiya da kwazo ba
A gurin raya Sunnah ta Ma’aiki (SAW) minti biyu kacal ka fado kasa kamar Zakara, Dole matarka ta rena maka, idan bata da karfin imani dole ta fara bin mazan banza, wannan hadin da kuke gani shine maganin matsalarka dan uwa
Tuzurai bana goyon bayan kuyi wannan hadin, amma ga duk wani tuzuru da aka saka ranar aurensa ya tabbata yayi wannan hadin, yafi duk wasu magunguna da zakayi amfani dasu tasiri, zai wanke maka mara tas, zakayi karfi garau
Tafarnuwa ne, da Kajiji, da kanumfari, da citta danye mai yatsu, za’a bare tafarnuwan, cittar za’a tsagata gida biyu, sai a wanke kajijin da kanumfari a cire kasan dake jikinsu, sai a hadasu gaba daya a zuba a cikin bokiti ko wani roba mai murfi da aka cikashi da ruwa mai tsafta, a barshi sai yayi kwana daya kafin a fara sha
Duk lokacin da kasha kofi daya sai ka sake mayar ruwa cikin kofi daya a kai, haka za’a dinga sha kowani lokaci har sai dandanonsa ya kare, a kalla duk bayan wata biyu kayi wannan hadin, kudinsa bai wuce 2K ba
Don Allah dan uwa Magidanci ka kasance mai yawan yin wannan hadin, Wallahi zaka tuna da Datti Assalafiy, kuma zaka sanya wa Datti albarka a matsayin tukwicin godiya
Idan da matarka tana maka raini zata dawo yi maka ladabi da biyayya, idan ka fita daga gida duk bayan awa daya zata kiraka ta tambayi lafiyarka, Allah-Allah take ka dawo gida, kai karan kanka zaka san cewa kai yanzu na miji ne ba mata-maza ba, babu sauran raini kuma
Muna fatan Allah Ya kara mana aminci da zaman lafiya tsakanin mu da matan mu na Aure
≡
Karanta Zafafan Sakonnin Soyayya Na Barka Da Asuba
✔
ZUWA GA MASOYIYATA
ƊANƊANO
Bayyana irin son da nake yi miki a zuciyata, tamkar tirsasa ni faɗar irin ɗanɗanon da ruwa yake da shi ne a cikin baki. Faɗar hakan abu ne mai matuƙar wuya. Ina son ki.
TSARABAR MASOYA NA BARKA DA ASUBA
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
KEWA
A duk lokacin da kike cikin kewata, ki tuna cewa, kina tare da ni a cikin zuciyata a ko yaushe. Matuƙar ina raye, ba za ki kasance cikin kaɗaici ba.
MURYA
Muryarki ce ke raba ni da damuwa a duk lokacin da rayuwa ta yi mini tsanani. Ina godiya a gare ki da kika kasance cikin kulawa da ni a ko wace rana.
MAFARKI
Zuwa ga wadda nake ƙauna fiye da wani nau’in kayan ƙyale-ƙyale na duniya. Ina yi miki fatan kasancewa cikin walwala a wannan dare, tare da yin bacci mai cike da kyawawan mafarkai akan abin so. Ki kwana lafiya masoyiyata.
BURI
Idan har ina raye a duniya, babu wani abu da za ki nema ki rasa, matuƙar damar mallaka miki shi tana hannuna. Na adana miki dukkan wani nau’in jin daɗin rayuwa a gidana. Burina ki zamo mata ta mu rayu tare har abada.
NUMFASHI
Abu mai wuya da zan iya yi a rayuwata shi ne mantawa da ke, wanda yin hakan abu ne da ba zai taɓa yiyuwa ba har zuwa ranar fitar numfashi. Ina son ki.
KEWA
Ina shiga cikin matsananciyar kewarki a dukkan wani taku na rayuwata da na yi ba tare da ke ba. Ina kewarki sosai fiye da adadin ɗigon ruwan da ke zuba daga saman duniya a lokacin damina. Ina fatan za ki fahimci irin damuwar da nake shiga na rashin ki a kusa da ni. Ina son ki.
RAYUWA
Na san ba ki san irin farin cikin da kasancewa tare da ke ya kawo a cikin rayuwata ba. Na yi duk wani tunani, na gano babu wani abu da zan iya biyanki da shi akan hakan, face na ce na gode, kuma zan kasance tare da ke har ƙarshen rayuwata.
SA’A
Ina cike da farin cikin samun macen da babu kamar ta a wannan duniya. A duk lokacin da na tuna da cewa ke tawa ce, sai na kalli kaina a matsayin mai sa’ar da babu kamar shi.
HAƊUWA
Ke ce mafarkina da nake yi a cikin kowane dare. Tun kafin mu haɗu, nake fatan haɗuwarmu domin gina rayuwa a tsakaninmu mai inganci. Ke ce kalar macen da na zaɓa, domin kuwa tun kafin mu haɗu, tsararriyar siffarki ta bayyana a cikin zuciyata. Ina son ki ne don halinki, ba don kyawun da kike da shi ba.
GASKIYA
A daidai lokacin da nake ganin babu wata soyayya ta gaskiya da ta rage a duniya, a lokacin kika sauya tunanina ta hanyar nuna mini ita a zahiri. Na aminta da cewa, kina yi min so ne na gaskiya ba don wani abu da na mallaka ba, hakan shi ne ya ƙara dasa sonki a cikin zuciyata, ta yadda babu wani abu da zai iya goge shi har abada. Ina son ki.
ZUWA GA MASOYINA
SO
Ina son ka irin son da ba zan taɓa yi wa wani irin shi ba, ina son ka da dukkan wani nau’in so da nake da shi, wanda zan iya ba wa wani a wannan duniyar.
TUNANI
A duk lokacin da na rufe idanuwana kai nake gani, kai ne a baccina da farkena. Babu wani abu da nake yi ba tare da tunaninka a cikinsa ba. Kai ne abin son zuciyata Yarimana.
TASIRI
Ina da ikon yin magana a duk inda nake so, amma ina cike da mamakin yadda nake kasa yin magana da wani saurayi bayan kai. Ko ka san mene ne dalili? Tasirin soyayyarka ce a cikin zuciyata, sai nake jin ka a kusa da ni, ko da ba ma tare.
MURMUSHI
Ba zan taɓa daina son ka ba har abada, ba zan iya tsayar da murmushi a saman fuskata ba a duk lokacin da muke tare. Ina son ka.
TUNAWA
Masoyina abin ƙaunata, ina yi maka fatan haɗuwa da tarin alkairan da ke cikin wannan rana, da samun nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin zuciya. Ka kasance cikin farin ciki da tunawa da ni a ko da wane lokaci. Kwana biyu ba ka nema na, anya kuwa kana tunawa da ni?
SAKO MAI MUHIMMANCI
Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko’ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.
MURYAR HAUSA24