Wasu maharba sun kashe zaki a jihar Borno bayan da ya fito gari ya fara addabar jama’a

 Wasu maharba sun kashe zaki a jihar Borno bayan da ya fito gari ya fara addabar jama’a

Daraktan Gandun Daji da Namun Daji na Ma’aikatar Muhalli ta jihar Borno “Peter Ayuba” ya tabbatar da cewa, maharba sun kashe wani zaki a Karamar Hukumar Konduga.

Da yake zantawa da Kamfanin Daillancin Labarai na Kasa “NAN” a ranar Talata a Maiduguri Ayuba yace, ga dukkan alamu zakin ya kufce ne daga Gandun Namun Daji na Wazza dake kasar Kamaru.

Inda ya kara da cewa, an samu irin wannan kufcewar ta giwaye daga gandun namun dajin, inda suka rika shiga kauyuka kamar su Karamar

Hukumar Kala-Balge.

A cewar Ayuba, an samu ma kuraye sun cinye wani mutum a Karamar Hukumar Kaga inda a karshe dai Ayuba ya ja kunnen mazauna

yankunan da su rika sanya ido, inda yace ba

abin mamaki bane zakin da aka kashe ranar

Lahadi akwai yan uwansa da zasu iya fitowa.

Jami’in yada Labarai na Karamar Hukumar Konduga “Asheikh Chabbol” yace sai da zakin ma ya tasa keyar wasu masu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button