Wata Amarya ta rasa ranta a hatsarin babbar mota yayin da za’a kaita dakin Mijin ta

 A ranar Lahadi wani mummunan al’amarin ya faru a garin kware karamar hukumar mulkin jahar sakkwato, inda wani mai babban moto kirar valvo ya kashe amarya a kan hanyar zuwa kaita dakin mijinta.

Daya daga cikin fasinja ya tabbatarwa da “Hausaloaded” cewa, mai motar ya taso ne daga miyami babban birnin kasar Niger motar babu burki kuma sitiyarin motar baya juyawa idan ta fara tafiya da ta tsayawa.

A lokacin da sunka shigo Nageriya karamar hukumar Tangaza dake jihar Sokoto a lokacin ne ya buge rakumi wanda ya shaida mana cewa

Tun daga nan kwanan rakumin ya kare to shine fasinja da wani abokin tafiyar sa suka sauka daga motar duba da motar babu lafiya sannan suka hau mashin.

Motar ta cigaba da tafiya domin cikin garin Sokoto zata shiga shigowar su cikin garin kware ke da wuya sai ga motar da aka dauko amarya ta taho, to daman babu burki nan take ya murkushe motar da amaryar ke ciki za’a kaita dakin mijin ta nan take rai ya yi halin sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button