YADDA AKE ABITRAGE CIKIN EXCHANGE DAYA TSAKANIN P2P BUY & SELL
YADDA AKE ABITRAGE A SASHEN P2P TSAKANIN P2P BUY & SELL
Kamar yadda a kwanakin baya shafin www.nasara.com.ng ya kawowa mabiyansa cikakken bayani akan yadda ake ABITRAGE TSAKANIN KASUWANNI BIYU, da yadda ake AMFANI DA COINGAPP domin samo token din da zakayi ABITRAGE tsakanin kasuwanni biyu,
Idan har ba ka riski wannan rubutu guda biyu masu muhimmanci ba har yanzu ba ka makara ba,
SHIGA NAN ka karanta cikakken bayani akan Yadda Ake ABITRAGE Tsakanin Kasuwanni Biyu.
SHIGA NAN ka karanta yadda ake AMFANI DA COINGAPP domin samun damar ABITRAGE Tsakanin kasuwanni biyu.
Yau cikin amincewar Allah zamuyi bayanin YADDA AKE ABITRAGE CIKIN KASUWA DAYA A SASHEN P2P TSAKANIN P2P BUY AND SELL.
ABITRAGE CIKIN KASUWA DAYA A SASHEN P2P TSAKANIN P2P BUY AND SELL yana nufin sayan DOLLAR ko wani TOKEN akan farashi mai sauqi a sashen P2P BUY da kuma sayar da shi cikin farashi mai tsada a P2P SELL.
MISALI:- Za ka sayi DOLLAR a P2P BUY akan N560 sai ka sayar da ita a P2P SELL akan N565, wanda hakan yake nufin akan duk $1 kana da ribar N5,
Idan ka sayi $100 kana da ribar N500, idan ka maimaita kamar sau 10 kana da ribar N5,000.
YADDA AKE ABITRAGE A KASUWA DAYA TSAKANIN P2P BUY AND SELL DA ABUBUWAN DA AKE KULA DA SU KAFIN A FARA
Da farko dole ka samu kasuwar da zakayi wannan kalar ABITRAGE din wadda Akwai P2P a cikinta, a yanzu kasuwannin da zaka iya samun wannan damar akwai BINANCE, KUCOI Da OKEX
Bayan ka shigar kasuwar sai ka je 6angaren P2P sai ka duba farashin DOLLAR a sashen BUY sannan ka duba a sashen SELL,
Za ka duba farashin Merchants din da suke saye da sayar da Dollar,
Bayan ka duba farashin DOLLAR a Sashen BUY DA SELL Sai ka duba ka ga shin akwai banbancin farashi a tsakanin Merchants da ke sashen BUY da wanda suke sashen SELL,
Idan ka samu yafi sauqi a sashen BUY ne, sannan a sashen SELL ya fi tsada, sai ka je ka saka ORDER ka sayi USDT din ko kuma token din sai ka zo ka sayar da shi a sashen SELL wajen da yafi tsada domin samun riba,
Abubuwan da yakamata kula da su kafin a fara:-
- Dole ka lissafa ka tabbatar akwai riba.
- Dole ka tabbata ka gane wajen da ribar take, shin a BUY take ko a SELL.
- Yana da kyau ka yi amfani da Bankin da Wanda za ka sayar masa da USDT ko token ba zai cajeka transaction fee ba, haka kaima idan za ka tura kudi bankinka ba zai cajeka transaction fee ba, anan ina baka shawarar ka bude account a KUDA BANK shine bankin da Merchant a P2P ba sa daukan transaction fee SHIGA NAN ka karanta cikakken bayani akan KUDA BANK.
- Dole ka kasance cikin nutsuwa da kuma maida hankali, domin shi Arbitrage irin wannan lokaci gareshi, kana iya samunsa yanzu sannan kana iya rasashi cikin qasa da mintuna 20.
- Sannan Wannan kalar Arbitrage din ana iya yin shi tsakanin kasuwa biyu (Two exchanges), Ma’ana idan ka lura Akwai banbancin farashin Dollar a tsakanin kasuwanni biyu, sai ka sayeta a kasuwar da take da sauqin farashi sannan ka sayarta a kasuwar da take da tsada.
Kafin ka fara duk wani abu a crypto currency da wani ya sanar da kaI, Ka tabbata ka yi naka binciken ma’ana “Do Your Own Research (DYOR) “.
A kullum ina bawa ‘Yan Cryoto Shawarar neman ilimin wannan kasuwancin na Crypto Currency mafi yawancin asarar da muke tana faruwane ta dalilin qarancin Ilimin da muke da shi ne