Yadda Ake Mayar Da USDT Zuwa nUSD A HOTBIT
Yadda Ake Mayar Da USDT Zuwa nUSD Ko nUSD Zuwa USDT A Kasuwar HOTBIT EXCHANGE
HOTBIT EXCHANGE Kasuwace ta Crypto Currency wadda da wuya ka samu mai yin wannan kasuwancin na Crypto Currency bashi da wannan kasuwar a cikin wayarsa domin yin siye da siyarwa na token ko coin.
Kasuwar HOTBIT tana da coin da token da suke bada riba/alkhairi cikin qanqanin lokaci,
Kasuwar HOTBIT kasuwace da take dauke da token masu qananan farashi, Kasuwar HOTBIT kasuwace da ta yi suna wajen tattara SHITCOIN, shi yasa wasu suke kiranta da gidan SHITCOINs,
Da yawa cikin ma’abota kasuwancin CryptoCurrency ma su amfani da kasuwar HOTBIT (HOTBIT.IO EXCHANGE) ba su san yadda ake mayar da USDT zuwa nUSD ba,
Yau shafin www.nasara.com.ng ya kawo cikakken bayani kan yadda ake mayar da USDT zuwa nUSD ko kuma nUSD zuwa USDT.
nUSDT TRADING PAIR ne a kasuwar HOTBIT,
Abin da ake nufi da TRADING PAIR shine kudin da za ka iya amfani da shi domin yin siyayya a kasuwar Crypto Currency, USDT, BUSD, TUSD, EUR duk misalai ne na kudade da ake iya amfani da su a kasuwannin Crypto Currency domin yin siyayya,
nUSDT shima yana cikin kudaden da ake amfani da su domin yin cinikayya a kasuwar Crypto Currency ta HOTBIT,
A yanzu mafi yawancin token da ake dorawa (Listing) a kasuwar HOTBIT ana iya siyansu ne kadai da nUSD,
Sai dai shi Trading pair na nUSD ana amfani da shi ne kadai a kasuwar HOTBIT, anan ne kadai ake iya yin siyayya da shi,
Sannan a iya kasuwar HOTBIT ne ake samunsa, sannan ba a iya withdraw din sa zuwa wata kasuwar ko kuma a turoshi daga wata kasuwar zuwa kasuwar HOTBIT,
Haka kuma hanya daya ce kadai ake iya samun sa shine ka juyar da kudinka na USDT ya koma nUSD,
Hanyoyin da ake mayar da USDT zuwa nUSD ko nUSD zuwa USDT
- Za ka shiga cikin kasuwar HOTBIT, ka na shiga ba tare da ka je ko ina ba a fuskar kasuwar wato HOME qasa da wajen da suke dora talla za ka ga wajen da aka rubuta EXCHANGE sai ka danna shi, zai kai ka zuwa ga wani shafi a saman shafin za ka ga an rubuta CONVERT, wanda a wannan shafin ne za ka mayar da USDT zuwa nUSD, Idan ka lura a shafin za ka ga an rubuta FROM a qasansa kuma an rubuta TO, ma’ana daga USDT zuwa nUSD ko kuma daga nUSD zuwa USDT, Sannan akwai wasu kibiya (arrow) guda biyu da suke tsakanin FROM da TO daga gefen dama amfaninsu shine mayar da USDT da ke sama zuwa qasa ko kuma mayar da nUSD da ke qasa zuwa sama, A yanzu USDT kake so ka mayar zuwa nUSD, Saboda haka sai USDT ta kasance a wajen FROM yayin da nUSD za ta kasance a wajen TO, Daga gefen USDT an rubutu “Please Enter the number”, ma’ana ka shigar da adadin yawan USDT din da kake son mayarwa zuwa nUSD, Idan kuma duka USDT kake son mayarwa zuwa nUSD za ka ga MAX sai ka dannashi, bayan ka shigar, daga can qasa za kaga an rubuta CONVERT sai ka dannashi nan take za ka ga an rubuta maka successfully converted , ma’ana an mayar maka da USDT zuwa nUSD, shikenan USDT ta koma nUSD sai aje a yi ta siyayya, Haka wannan hanyar za ka bi wajen mayar da nUSD zuwa USDT bayan ka siyar da coin din da ka siya da nUSD, sai dai nUSD za ta kasance a sama qasan FROM yayin da USDT za ta kasance a qasa wajen TO.
- Hanya ta biyu shine za ka shiga WALLET/FUND, ma’ana wajen da kake ganin kudinka da token din da ka siya, sai ka yi searching na USDT ko nUSD, duk wadda ka yi searching sai ka ta6ashi, zai bude maka wani shafi anan za ka ga wajen da aka rubuta CONVERT sai ka dannashi shima zai kaika zuwa ga wani shafi, wanda anan za ka mayar da USDT ta koma nUSD ko kuma nUSD ta koma USDT, sai ka bi irin hanyar da mukayi bayani a hanya ta farko.
Yana da kyau ka san wadannan abubuwa masu muhimmanci da suke da alaqa da nUSD
Yana da kyau ka san duk USDT 1 yana daidai da nUSD nawa ne?
Duk USDT yana daidai da nUSD Biliyan daya ne wato (1 USDT = 1,000,000,000, nUSD), yayin da duk nUSD 1 yake daidai da USDT 0.000000001, Sannan shi wannan juyar da USDT zuwa nUSD kyauta ne babu wani caji da ake dauka.