Yadda Ake Nemo Contract Address Na Kowanne Coin/Token

 Yadda Ake Nemo Contract Address Na Kowanne Coin/Token


CONTRACT ADDRESS:- Contract Address shine adireshin da yake wakiltar coin ko token cikin lambobi da haruffa wanda matuqa kana neman coin ko token idan har ka samu Contract Address na wannan coin ko token din to kamar ka sami wannan coin ko token din ne.

Kowanne coin ko token yana da nasa Contract Address, kuma na kowanne ya banbanta da na sauran.

YADDA AKE NEMO CONTRACT ADDRESS.

Akwai hanyoyi da ake bi wajen nemo contract address wanda a yanzu shafin www.nasara.com.ng zai yi cikakken bayani akan wasu daga ciki. 

1. ETHERSCAN.IO :- Wannan itace hanya ta farko da ake bi wajen nemo Contract Address na token ko coin, ETHERSCAN.IO shafi ne na yanar gizo wanda yake dauke da bayanan duk wani coin ko token da yake kan ETHERIUM BLOCK CHAIN (ERC20),

Hakan yana nufin kawai coin ko token da yake kan ETHERIUM BLOCK CHAIN ne ake iya samun Contract Address dinsa a shafin ETHERSCAN.IO. 

Saboda haka duk lokacin da ka ke neman Contract Address Na wani token ko coin da yake kan ERC20, Kawai za ka shiga cikin browser ka rubuta sunan coin ko token din sai ka qara contract address a gaba, 

Misali:- kana neman Contract Address na Shiba Inu ne, Sai ka rubuta Shiba Inu Contract Address,

Bayan ka yi searching zai kawoka Shafin da ke dauke da bayanai masu alaqa da wannan coin ko token da kayi searching,

Sai ka duba wanda yake da alaqa da shafin ETHERSCAN.IO kamar yadda yake a qasa cikin hoto sai ka ta6ashi,

Bayan ka ta6ashi, zai kawoka wannan shafin da ke qasa, idan ka duba ga wani wajenan mun nuna shi da Kibiya sai ka ta6ashi, kana ta6awa shikenan zai kwafe (copy) maka Contract Address na Shiba Inu. 

Saboda haka duk lokacin da kake neman Contract Address na token da yake kan ETHERIUM BLOCK CHAIN za ka bi hanyar da muka bi a sama ne.

2. BSCSCAN.COM :- Shima shafin yanar gizo ne wanda yake dauke da coin da token wanda suke kan BINANCE SMART CHAIN BLOCK CHAIN (BSC/BEP20),

Saboda haka duk lokacin da kake neman Contract Address na Coin ko token da yake kan BSC Block Chain sai ka shiga cikin browser ka rubuta sunan coin din sai ka qara Contract Address a gaba sai kayi searching zai bude maka irin shafin da ya bude mana lokacin da mukayi searching na Shiba Inu Contract Addres.

Misali:- muna neman Contract Address na Safemoon, sai muje cikin browser mu rubuta Safemoon Contract Address sai muyi searching, 

Zai bude mana shafi dauke da bayanan da suke da alaqa da Safemoon,

Sai mu duba wanda yake da alaqa da BSCSCAN.COM, gashinan cikin hoto.

Idan ka ta6ashi zai bude maka shafi na gaba, sai ka duba qasa zaka ga wajen Contract Address, sai ka ta6a wajen da muka nuna da kibiya zai maka copy din Contract Address na wannan token. 

Bayan BLOCK CHAIN na ETHERSCAN da BSCSCAN, akwai wasu BLOCK CHAIN din da ba wannan biyun ba wanda suma akwai coins da tokens akansu,

Daga Cikin wadannan BLOCK CHAIN din akwai Solana, TRC20, Huobi, Avalanche, Polygon, Iotex, Harmony, Okex chain, Tomo, Arbitrum One, Kardiachain,  Avalanche dss.

Saboda haka duk lokacin da kake neman Contract Address Na token ko coin sai kaje browser ka rubuta sunan coin ko token din sai ka qara contract address a gaba sai kayi searching za ka samu Contract Address na wannan coin din.

3. COINGECKO da COIN MARKET CAP:- Wannan itama hanya ce mai sauqi kuma mafi inganci da ake nemo Contract Address na coin ko token, 

Domin duk Coin ko token da ka gani a cikin wadannan manhajoji to coin ne na gaskiya ba na jabu ba. 

Za ka je cikin rumbun manhajoji wato Playstore, sai kayi Searching na wadannan manhajoji guda biyu, bayan ka sauke su sai ka shiga cikinsu, 

Idan COINGECKO ka fara shiga, kana shiga zai nuna maka Coins wanda suka fi kowanne coin da token Yawan Market Cap,  Gashinan qasa cikin hoto. 

Idan ka duba wannan hoto da ke sama ga wani wajenan mun nunashi da kibiya, wanda yake da alamar Searching, sai ka ta6ashi, 

Zai bude maka shafin da za ka nemo coin din da kake neman Contract Address dinsa, Saboda haka sai ka rubuta sunan coin din, sai ka danna Search, ko kuma kafin ka danna Search din ma za ka ga ya nuna maka coin din sai ka ta6ashi, 

Bayan ka ta6ashi zai bude maka shafi mai dauke da CHART din wannan coin din, sai ka yi Scrolling zuwa qasa za ka ga wani waje an rubuta Contract Address, daga gefensa kuma akwai wata alama ta littafi ko ta kibiya an rubuta show kusa da ita kamar yadda yake a qasa cikin hoto. 

Idan alamar littafi ce sai ka ta6ashi zai maka copy din Contract Address Na wannan coin din, 

Idan alamar kibiya ce kamar yadda yake a sama  hakan yana nufin wannan coin din yana kan BLOCK CHAIN sama da daya, sai ka danna kibiyar zata nuna maka duk BLOCK CHAIN din da wannan coin din yake kansa, sai ka duba ka ga na wanne BLOCK CHAIN kake nema sai ka ta6ashi zai maka copy din Contract Address dinsa. 

Idan kuma COIN MARKET CAP (CMC) ce, Itama duk hanyar da mukayi bayani akan COINGECKO ita zakabi domin nemo Contract Address na kowanne coin ko token.

Bayan ka shiga ka yi searching na coin, ka dannashi ya bude maka chart, sai kayi Scrolling zuwa qasa, za kaga wajen da aka rubuta CONTRACT sai ka ta6ashi kayi copying, idan yana kan BLOCK CHAIN sama da daya zai bude maka sai ka za6i na wanda kake nema, duba hotunan da ke qasa. 

4. POOCOIN.APP:- Wannan shima shafine na yanar gizo, wanda ake samun bayanan Coin ko token wanda suka hada da Contract Address, Chart, Holders na token, Market Cap na Coin da sauransu, 

Sannan ana iya siyan coin ko token a POOCOIN.APP, 

Sai dai iya Coin ko token da suke kan BSC Block Chain (BEP20) ne kadai ake iya samun bayanansu a POOCOIN.APP. 

Za kaje cinkin browser ka rubuta POOCOIN.APP kayi searching yayin da zai kaika zuwa ga shafin POOCOIN.APP wanda anan za ka ga akwatin da ake rubuta sunan coin ko token domin a nemo shi,

Sai ka rubuta token din da kake neman Contract Address dinsa, sai kayi searching, kafin ka danna Search ma zaka ga ya nuna maka Token din matuqar kana da Network mai qarfi, kamar yadda yake a sama cikin hoto,

Sai dai ka lura sosai lokacin da kake neman Contract Address na token a POOCOIN.APP, domin Token qwaya daya sai ka ga kusan guda uku ko sama da haka sun bayyana maka kuma duk irin su daya, sai dai ba zaka rasa abin da zai banbance maka su ba,

Idan ba ka tantance ba sai ka dauki na jabu wato fake. 

Bayan ka gama nemo COIN ko TOKEN din, sai ka ta6ashi, zai bude maka shafin da yake dauke da farashin wannan coin din da kuma chart dinsa,

A hoton da ke sama idan ka duba akwai wata akwati an rubuta “Enter token name/address”, sannan daga gefe akwai wata alamar pencil sai ka ta6ata, kana ta6awa za ka ga ta fito maka da Contract Address a cikin akwatin, sai kayi copying dinsa. 

Wannan shine cikakken bayanin da shafin www.nasara.com.ng ya gabatar akan wasu hanyoyi da ake bi domin nemo Contract Address na coin ko token.Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button