Yadda Ake Transfer Na Google Authenticator Accoun Daga Wata Wayar Zuwa Wata Wayar

Yadda Ake Transfer Na Google Authenticator Daga Wata Wayar Zuwa Wata Wayar 


Shafin www.nasara.com.ng zai koyar da mu yadda zamu yi transfer na Google Authenticator account dinmu daga wata wayar zuwa wata wayar, 

Domin da yawa cikin masu amfani da Google Authenticator suna mantawa ba sa ajiye Private Key lokacin da suka yi activating Google Authenticator a exchange ko wallet, 

Wanda shi private key ana bada shi ne sau daya, idan ka manta baka ajiye ba to dole ka samu wata hanyar da zakayi activating din Authenticator account yayin da ka canja waya ko aka sace maka ko kayi restore din wayar,

Wannan hanyar itace zamuyi bayanin yadda za kayi transfer na Authenticator account lokacin da ka canja waya,

Ga bayanin hanyar:-

Da farko Ya kasance akwai wayoyi guda biyu, wadda Authenticator account yake kanta da wadda za a yi transfer din account din zuwa kanta, 

Dukansu wayoyin guda biyu sai ka shiga cikin Google Authenticator, 

Bayan ka shiga, Tsohuwar wayar da Authenticator account din yake kanta idan ka duba daga sama akwai wasu đigo (Dot ⠇) guda uku a jere daya a qasan daya, sai ka ta6ashi, 

Bayan ka ta6ashi zai nuna maka wani dan shafi qarami a sama, sai ka duba wajen da aka rubuta TRANSFER ACCOUNT sai ka ta6ashi,

Bayan ka ta6ashi zai daukeka zuwa wani shafi wanda anan za ka ga an rubuta EXPORT ACCOUNT da IMPORT ACCOUNT,

Sai ka za6i EXPORT ACCOUNT, bayan ka za6a zai buqaci security pattern din wayarka ko fingerprint, ya danganta da wanda kake amfani da shi a wayarka, 

Bayan ka shigar da security dinka, zai kai ka shafi na gaba wanda anan zai nuna maka duk Authenticator Accounts din da yake kan wayar, 

Sai ka duba ACCOUNT din da kake son transfer sai kayi marking, idan duka ne ma sai kayi marking dinsu duka, 

Bayan ka za6i account da kake son yin transfer sai ka danna NEXT, 

Bayan ka dannan NEXT zai kai ka zuwa ga shafi na gaba mai dauke da QR CODE, wanda a saman shafin an rubuta SCAN QR CODE

Wannan duk zakayi su ne a cikin wayar da Authenticator account dinka yake kansu, 

Amma kuma yanzu za ka buqaci sabuwar wayarka bayan ka je shafin da aka aka rubuta maka SCAN QR CODE,

Bayan ka shiga Authenticator a sabuwar wayarka, daga qasa gefen hannun dama za ka ga wata alamar tarawa “Plus Sign” (+), sai ka ta6ata, 

Za ta nuna maka option guda biyu, SCAN A QR CODE da ENTER A SETUP KEY, 

Sai ka za6i SCAN A QR CODE, zai kai shafin da za ka ga ya bude maka camera cikin wani dan akwati,

Sai ka daidaita wannan dan akwatin akan QR CODE din da yake kan tsohuwar wayarka, kamar dai yadda ake yi da XENDER, 

Kana daidaita akwatin akan QR CODE din za ka ga yace maka ACCOUNT IMPORTED,

Idan kuma account  din da kake so ka yi transfer sama da guda daya ne, 

A sabuwar wayar bayan ka dauki QR CODE na farko, zai ce maka “on the other device go to QR CODE 2 of 2″,

Sai ka duba tsohuwar wayar daga qasa an rubuta NEXT, sai ka ta6ashi, kana ta6ashi zai kai ka QR CODE na gaba, shima sai ka daidaita akwatin a cikinsa, zai dauka maka nan take, 

Yana gama daukan QR CODE na biyu zai rubuta maka “ACCOUNTs IMPORTED”,

Shikenan ka yi transfer din Google Authenticator account dinka zuwa wata wayar, 

Yana da kyau ka san cewa dole da EXCHANGE da AUTHENTICATOR su kasance a waya daya kafin Authenticator yayi aiki, 

Ba zaka iya dauko code daga cikin Authenticator da ke cikin wata wayar sannan ka ce za ka shigar da shi a cikin wata EXCHANGE ko WALLET da ke kan wata wayar, 

Sa6anin verification code da ake turowa ta hanyar SMS ko mail shi zaka iya daukoshi daga wata wayar zuwa wata wayar. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button