Yadda wani mutun ya fayde ga kanwar matarsa mai shekaru 10 aduniya.

 Ana Tuhumar wani dan achaba mai suna Godwin, Saka makon fyade ga kanwar matarsa mai shekaru 10 a duniya a wani kauye mai suna Kanshio, cikin ƙaramar hukumar in the Makurdi ta jihar Benuwai.

An tambayi yarinyar da abin ya faru da ita.

Yarinyar da lamarin ya ritsa da ita, ta shaida wa mai sayar da maganin cewa mijin yayarta ya sadu da ita, inda ta ƙara da cewa da ta kai ƙorafi wurin yayarta sai ta manta kawai da lamarin.

Wani mazaunin mai suna Adem ya shaida abin da ya faru kaman haka:

Gabaɗaya lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar, kusan mutum 10 daga ƙauyen Kanshio, a ƙaramar hukumar Makurdi, su ka kawo Godwin zuwa gidan abokina. Sunan abokin nawa Mfe Shaminja, sirikin matar Godwin ne.

Sun bayyana cewa yarinyar taje siyan magani ne lokacin da ta ga wata ma’aikaciyar jinya, inda tayi mata ƙorafin tana fama da matsanancin ciwon ciki.

A lokacin da matar da tambaye ta abinda ya faru, ta bayyana cewa mijin yayarta yana saduwa da ita, sannan ta gayawa yayarta amma bata yarda da ita ba. Ma’aikaciyar jinyar ce ta tona masa asiri inda mutane su ka cafko shi a gidan sa.

Ya bayyana cewa ya je ya kwanta ne inda yaran ke barci inda anan ne lamarin ya auku. Ya ce sau ɗaya kawai lamarin ya auku, amma yarinyar tace ya sadu da ita yakai sai uku. Yarinyar ta kusa kai shekaru 10 a duniya.

Mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Ukan Kurugh, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benuwai, sannan kuma an miƙa Godwin a hannun jami’an hukumar hana safarar mutane a jihar wato NAPTIP.

Kwamandan shiyyar Makurdi na hukumar NAPTIO, Gloria Iveren-Bai, ta ce an cafke wanda ake zargin sannan kuma yarinyar na hannun hukumar su inda ta ke samun kulawa.

A ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu, hukumar NAPTIP reshen Makurdi, ta samu ƙorafi daga wani mutum wanda ya rubuto cewa wani Godwin Shagbaor yayi wa yarinyar sa mai shekaru 9 a duniya fyade

An ceto yarinyar da lamarin ya ritsa da ita inda aka kai ta asibiti domin yi mata gwaje-gwaje, kuma ana jiran sakamakon. Yanzu haka tana amsar kulawa.

Wanda ake zargi da aikata fyaden ya amsa cewa ya aikata laifin amma ya ɗora alhakin hakan akan giya. Wanda ake zargin yana kulle yayin da ake cigaba da gudanar da bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button