Yadda za ka dawo da Google Authenticator Account na HOTBIT

 Yadda za ka dawo da Google Authenticator Account na HOTBIT 

Authenticator mataki ne na tsaro wanda yake karfafa tsaro da kariya a kasuwannin Crypto Currency, sannan kawai mamallakinsa ne kadai yake da damar  amfani da shi, shi yasa Kasuwar HOTBIT ta sanya wasu dokoki da matakai da dole sai an bi kafin a dawo da Authenticator account, saboda kar wani yayi qoqarin sace account din wani. 

Biyo shafin www.nasara.com.ng a sannu domin jin yadda ake dawo da HOTBIT Google Authenticator Account.

* Akwai wasu bayanai da za ka tanada sannan ka turasu zuwa ga adireshin email na HOTBIT mai suna support@hotbit.io,

*Sannan yayin da za ka tura saqon dole ka turashi ta email dinka da ka bude HOTBIT da shi, 

* Sannan bayan ka tura saqon zai iya daukan har awa 72 daidai da kwana 3 kenan ko qasa da haka kafin ka samu reply, saboda duk bayanan da ka tura musu sai sun bi shi sun tantance, 

SHIGA NAN Ka Karanta Authenticator Da Ake Iya Dawo Da Account Bayan An Canja Waya Ko An Saceta

Bayanan da za ka tura ta saqon email zuwa ga support@hotbit.io


1. Adireshin email da lambar waya da kayi amfani da su wajen yin rijista da kasuwar HOTBIT, sannan lambar wayarka ya kasance ka rubuta ta da Country code na Nigeria (+234…..), Zero na farko da ke kan lamba cireshi ake yi, Misali idan lambarka ta fara da 070 ko 080 ko 081 sai ka rubuta kamar haka +23470 ko +23480 ko +23481.

2. Za kayi screenshot na deposit da kuma screenshot na withdrawal da ka yi zuwa cikin HOTBIT dinka wanda bai fi kwanaki bakwai da yi ba, amma idan babu wanda bai fi kwanaki bakwai ba sai wanda ya wuce haka sai ka duba wanda yake na qarshe, 

Ina zan samo screenshot na deposit da withdrawal da na yi zuwa HOTBIT ?,

Shafin www.nasara.com.ng yayi cikakken bayani

Deposit screenshot za ka sameshi ne ta hanyar shiga cikin wallet ko EXCHANGE din da ka turo wani coin ko token zuwa cikin HOTBIT, bayan ka shiga cikin BINANCE ko KUCOIN ko ma wata EXCHANGE sai ka nemi NOTIFICATION, 

Idan BINANCE ce sai ka duba daga sama gefen hagu akwai hoton kan mutum, sai ka ta6ashi zai kai ka profile dinka, sai ka duba za kaga NOTIFICATIONs, sai ka ta6ashi zai nuna maka duk wani deposit ko withdraw da kayi, 

Sai ka duba withdrawal da kayi daga Binance zuwa HOTBIT sai ka ta6a shi zai bude maka, bayan ya bude sai kayi screenshot, shikenan ka samu Screenshot na deposit, 

Screenshot na withdrawal shima za ka bi irin hanyar da ka bi a screenshot na deposit,

Sai dai shi withdrawal yana nufin coin ko token da ka turo daga HOTBIT zuwa wata EXCHANGE ko WALLET, 

Idan cikin BINANCE ka turo sai ka bi waccan hanyar ta sama amma fa shi a cikin BINANCE za ka nemi Deposit ne,

Idan ba cikin BINANCE ka turo ba sai ka je cikin wallet ko EXCHANGE din da ka tura sai ka shiga wajen withdrawal history sai ka nemo COIN ko TOKEN da ka turo daga HOTBIT cikin wannan exchange din, sai ka shiga cikinsa ka yi screenshot,

Idan kuma daga cikin KUCOIN ne ka yi withdrawal ko deposit, domin samun yin screenshot na deposit da withdrawal, Za ka shiga KUCOIN sai ka shiga ASSETS

SHIGA NAN Ka Karanta Matsalolin Google Authenticator Tare Da Maganinsu 

Idan screenshot na Deposit ne za kayi, wato coin ko token da ka tura daga KUCOIN zuwa HOTBIT sai ka danna Withdraw

Bayan ka danna withdraw zai nuna maka tokens da coins, sai ka yi searching din wanda ka tura daga KUCOIN  zuwa HOTBIT,

Bayan ka yi searching dinsa, sai ka ta6abashi, kana ta6ashi zai bude maka wani shafi, idan ka duba a shafin daga sama gefen dama za kaga an rubuta HISTORY,

Kana ta6a HISTORY zai kaika zuwa ga shafin da yake dauke da bayanan wannan coin din da ka tura daga kasuwar KUCOIN zuwa cikin wasu kasuwannin,

Sai ka duba wanda ka tura daga KUCOIN zuwa HOTBIT sai ka ta6ashi, zai bude maka sai kayi screenshot, Shikenan ka samu Deposit Screenshot.
Idan screenshot na withdrawal ne, wato coin ko token da ka turo daga HOTBIT zuwa KUCOIN,  sai ka shiga KUCOIN, sai ka  shiga ASSETS ka dannan DEPOSIT, sannan ka yi searching din coin ko token da ka turo daga HOTBIT zuwa KUCOIN, Sai ka ta6ashi zai bude maka, sai ka duba history na wanda ka turo daga HOTBIT zuwa KUCOIN sai ka ta6ashi, sai kayi screenshot,

Bayan ka samu Screenshot na Withdrawal Da na Deposit, abu na gaba shine,
3. Za kayi cikakken bayani na irin Trading  din da kayi a cikin HOTBIT dinka kafin ka rasa Authenticator account dinka, 

Abin da ake nufi da hakan shine zakayi bayanin cewa ka sayi token na Dollar kaza sannan ka siyar da token kaza na Dollar kaza, ko ka sayi token guda kaza ka siyar da guda kaza ka bar guda kaza,

Wato dai za ka musu bayani dalla-dalla akan irin cinikayyar da kayi a HOTBIT dinka, 

SHIGA NAN Yadda Ake Transfer Na Google Authenticator Zuwa Wata Wayar 

4. Za ka tura hotunan wadannan abubuwan:- 
  •  Hotonka kana riqe da ID card ko passport dinka a hannun dama ko hagun, 
  • Sannan za ka samu takarda ka rubuta HOTBIT da kwanan wata da kuma signature dinka, sai ka riqe a daya hannun, ka ga kenan za kayi hoto riqe da ID card ko passport da takardar da ka rubuta wadancan bayanai a daya hannun, Ka tabbata fuskarka ta fito sosai haka shima ID card ka tabbata ya fito sosai. 
  • Sannan Za ka dauki hoton gaba da bayan ID card dinka ko passport,

5. Za kayi bayanin meyasa kake so ka dawo da HOTBIT account dinka, anan sai ka musu bayani cewa kana so ka dawo da HOTBIT account dinka saboda da dukiyarka da take ciki sannan kana so ka cigaba da amfani da kasuwar HOTBIT a kasuwancinka na Crypto Currency.


6. Dawo da Authenticator Account abu ne mai matuqar wahala, saboda haka ka tabbata duk abin da aka buqata a sama ka samar da su daidai da yadda aka buqata. 

7. Bayan ka tattara wadannan bayanan, sai ka turasu ta hanyar saqon email zuwa ga wannan adireshin na support@hotbit.io,  sannan za ka turasu ne ta adireshinka na email da ka bude HOTBIT da shi, 

Bayan ka tura wadannan bayanai account dinka na HOTBIT Zai dauki kwanakin aiki bakwai ( seven working days) kafin ya dawo aiki. 

8. Yayin da za ka tura wadannan bayanai ta hanyar adireshin email na support@hotbit.ioTitle na email dinka shine “RESETTING GOOGLE AUTHENTICATOR”.

Wannan shine cikakken bayani akan hanya qwaya daya da za kabi domin dawo da Authenticator Account dinka na HOTBIT, kuma ita kadai ce hanyar da HOTBIT ta amince domin abi a dawo da Authenticator account na kasuwarta.

Idan kana neman qarin bayani kana iya neman mu ta hanyar saqon whatsapp a wannan Lambar
07035791120

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button