Yadda Za Ka Fitarwa Da Kan ka EXIT Bayan Ka Samu Riba Ta Hanyar Amfani Da Bollinger Band


 Yadda  Za Ka Fitarwa Da Kan ka EXIT Bayan Ka Samu Riba Ta Hanyar Amfani Da Bollinger Band 


Kamar yadda mu ka sani BOLLINGER BAND đaya ne daga cikin indicators da ake amfani da su a kasuwar crypto currency domin yin technical analysis domin gano lokacin da za ka sayi coin ko kuma gano lokacin da za ka fita bayan ka samu riba, 

A rubutunmu na baya Munyi cikakken bayani akan yadda zaka fitarwa da kanka SIGNAL, ma’ana lokacin da ya dace ka sayi coin ko token ta hanyar yin amfani da BOLLINGER BAND (LOWER BAND).

karanata Yada Za Ka Fitarwa Da Kan Ka SIGNAL Ta Hanyar Yin Amfani Da Bollinger Band 


Yau zamuyi bayani akan yadda zaka fitarwa da kanka EXIT ta hanyar yin amfani da Bollinger Band, 


EXIT shine wajen da yakamata ka sayar da coin ko token bayan ka ci riba domin kiyaye fađuwar coin ko token din a bayan ya tashi ya baka riba, 

Za mu iya kiran EXIT da TP wato “Take Profit”, ko kuma mu kirashi da “RESISTANCE“,

A takaice dai shi EXIT wajene da matuqar COIN KO TOKEN ya je to Tabbas akwai yiwuwar dole zai sauko qasa, Kuma sanin duk wani masanin Technical Analysis ne a crypto currency matuqar coin ko token yaje ya ta6a RESISTANCE dinsa to akwai yiwuwar coin din zai Sauko ya dawo yayi RETRACEMENT ko ma ya fađi, 

Amma ana iya samun coin ko token ya zo ya fasa RESISTANCE dinsa kuma ya cigaba da tashi domin zuwa ga sabon RESISITANCE  

Saboda haka bayanin da muke so mu yi shine ta Yaya za ka yi amfani da BOLLINGER BAND ka sani cewa coin ko token bayan yaje RESISITANCE dinsa dawo qasa zai yi ba zai qara gaba daga nan ba?

Ga amsar a qasa:-

A duk lokacin da ka ga Coin ko token Ya je ya daki UPPER BOLLINGER BAND ya kuma fasashi, bayan ya fasa UPPER Bollinger Band sai kuma ya dawo qasan upper Bollinger Band yayi closing, Bayan yayi closing a qasan upper Bollinger Band wato tsakanin Upper Bollinger Band da Middle Bollinger Band kenan,  bayan yayi closing sai yayi creating na sabon candle wanda kuma candle đin bearish candle ne to tabbas wannan alamu ne da yake tabbatar maka da cewa Wannan coin đin ko token daga nan fa qasa zai yi saboda haka a Wannan wajen ya kamata ka fita daga kasuwa, 

Wannan wajen da za ka fita daga kasuwa Shi ake kira da EXIT kuma shine mu ke wannan dogon rubutun akansa, 

Ga bayanin da mukayi a qasa cikin hoto 


Ga wasu coin da suka yi abin da muke bayani a zahiri 



Amma ya na da kyau ka sani cewa token zai iya closing a qasan upper Bollinger Band ya kuma samar da bearish candle amma kuma ya zo ya qara fasa Upper Bollinger Band ya kuma cigaba da tashi, Ya danganta da Qarfin da coin đin ya fasa Upper Bollinger Band, Duba Wannan hoton da ke qasa domin samun tabbaci, 


Sai dai duk lokacin da ka ga Coin ya baka irin wannan exit đin da mukayi bayani to ka fita daga cikin coin đin sai ka jira ka ga shin zai qara fasa upper Bollinger Band ya kuma cigaba da tashi,

Idan Har hakan ta faru sai ka koma cikin coin đin amma sai ka duba Entry mai kyau ka shiga.


IDAN COIN YA FASA UPPER BOLLINGER BAND SANNAN YAYI CLOSING A SAMAN UPPER BOLLINGER SANNAN YA QARA SAMAR DA WANI BULLISH CANDLE (confirmation candle) A SAMAN UPPER BOLLINGER BAND SHIN ME HAKAN YA KE NUFI??? 

Idan har hakan ta faru to abin da hakan yake nufi shine Coin din zai cigaba da tashi ne kuma tashi na ban mamaki, Domin daga nan wajen da yayi forming na bullish candle a saman upper Bollinger Band bayan wancan candle đin da ya fasa upper Bollinger Band yayi closing tabbas zai iya linka maka kuđinka cikin qanqanin lokaci,

Cikin hoton da ke qasa za ka ga kibiya ta farko ta nuna mana wajen da candle ya fasa upper bollinger band, kibiya ta biyu ta nuna mana anyi forming bullish candle a saman bollinger band, kibiya ta uku har ta qarshe sun nuna mana yadda coin din ya cigaba da tashi. 


NA SAN DA YAWA BA SU SAN MENENE BOLLINGER BAND BA, BA SU KUMA SAN YADDA AKE KUNNA SHI BA KO MA WAJEN DA AKE SAMUNSA, INSHA ALLAH A RUBUTNMU NA GABA ZA MU KAWO CIKAKKEN BAYANI MAI GAMSARWA AKAN HAKAN

SAI A BIBIYEMU A SHAFUKANMU NA SADARWA DOMIN SAMUN SABBIN RUBUTUNMU AKAN WAĐANNAN DA MA SU MASU CIKE DA ILMANTARWA 

*TELEGRAM*
*WHATSAPP*
*FACEBOOK*

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button