Yadda Za Ka Magance Matsalar “Volume of order placement must be the integral multiple of 100,000” A Kasuwar HOTBIT

 Yadda Za Ka Magance Matsalar “Volume of order placement must be the integral multiple of 100,000” A Kasuwar HOTBIT

 

Da yawa cikin masu amfani da kasuwar Crypto Currency ta HOTBIT suna gamuwa da wannan matsalar da muka anbata a sama,

Wannan matsalar tana faruwa ne lokacin da aka zo siyan coin ko token wanda Trading Pair dinsa nUSD ne, 

SHIGA NAN ka karanta Ma’anar Trading  Pair da  cikakken bayani akan nUSD da yadda za ka mayar da USDT zuwa nUSD 


Bayan ka daidaita adadin yawan coin ko token din da za ka siya ka danna BUY sai ka ga daga qasa an rubuta maka “Volume of order placement must be the integral multiple of 100,000”

Shin ka san abin da hakan yake nufi?

Ga cikakken bayani akan abin da hakan yake nufi daga shafin www.nasara.com.ng 

Abin da hakan yake nufi shine:-

1. Dole yawan wannan adadin coin din da za ka siya ya kasance idan aka rabashi da 100,000 ba zai bada ragowa ko decimal point ba,

Abin da hakan yake nufi shine, yawan token din da za ka siya ya kasance 100,000 za ta shiga cikinsa ta rabashi daidai ba tare da an samu ragowa ba, 

Misali:-

Dubu dari (100,000) za ta shiga cikin Miliyan daya (1,000,000) ta rabata daidai ba tare da tayi ragowa ba,

Domin ka qara fahimta, shiga cikin calculator ka raba 1,000,000 da 100,000, Idan ka raba zai baka 10, ma’ana 100,000 guda 10 ce a cikin 1,000,000,

Idan ka lura amsarmu itace 10, Sannan babu ragowar komai sannan babu wani decimal point,

Amma kai idan ka je siyayya ba sai ka shiga cikin calculator ka yi wannan lissafin ba, 

Yadda za kayi shine dole ya kasance akwai sifili wato zero (0) daga guda biyar zuwa sama a qarshen lambobin da zaka rubuta na yawan token din da za ka siya, 

Matuqar lambar da ta zo a qarshen “Volume of order placement must be the integral multiple of” Dubu dari ce (1,00,000)

SHIGA NAN ka karanta yadda zakayi siyayya kamar a market price a HOTBIT 
Saboda haka ko da ka saka percentage na yawan kudin da zaka siya matuqar ba a samu sifili daga guda biyar zuwa sama a qarshe ba to zai yi ta rubuta maka “Volume of order placement must be the integral multiple of 100,000, kuma idan za kayi ta danna BUY sai dubu to haka zai yi ta rubuta maka har sai ka canja lambobi guda biyar na qarshe sun koma sifili.

Ba wai kawai iya “Volume of order placement must be the integral multiple of 100,000″ yake faruwa ba wani a maimakon ka ga Dubu dari (100,000) sai ka ga miliyan daya (1,000,000) ma’ana za ka ga an rubuta “Volume of order placement must be the integral multiple of 1,000,000″, Ya danganta da yadda ka gani, 

To kai dai ko ma wannene ka gani abin da za ka kula da shi shine; sifili nawa ne cikin lambar da aka rubuta maka  qarshen “Volume of order placement must be the integral multiple of”,

Idan guda shida ne to sai ka maida lambobin qarshe guda shida na yawan adadin coin din da za ka siya su koma sifili wato zero guda shida, idan biyar sai ka maida su biyar ya danganta da wanda ka gani,

2. Abu na biyu da Volume of order placement must be the integral multiple of 1,00,000″ take nufi shine,  dole yawan coin ko token da za ka siya ya fara daga guda 100,000 zuwa sama,  hakan yana nufin ba zaka iya siyan token din ba qasa da yawan lambobin da suka zo a qarshen Volume of order placement must be the integral multiple of”.

 Wannan shine maganin matsalar “Volume of order placement must be the integral multiple of” Wanda shafin www.nasara.com.ng ya binciko ya kawo muku.

SHIGA NAN ka karanta Yadda ake dawo da Google Authenticator A HOTBIT 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button