Yadda Za Ka Qara Girman Memory/Storage Na Wayarka Har Zuwa Sama Da 100GB Cikin Sauqi

 Yadda Za Ka Qara  Girman Memory/Storage Na Wayarka Har Zuwa Sama Da 100GB Cikin Sauqi

Kamar yadda shafin www.nasara.com.ng a kullum burinsa ne ya ga ya kawowa mabiyansa masu bibiyar rubututtuknsa abubuwan da zasu taimaka musu a rayuwarsu ta yau da gobe wadda take da alaqa da fasahar zamani,

A yau munzo da hanya mai sauqin gaske yadda za ka qara girman storage ko kuma memory din wayarka zuwa adadin da kake so, 

Kamar yadda muka sani Storage/Memory shine kamar wani mazubi ne da ake ajiye abubuwa kamar su Hotuna, Video, Audio, Document da sauransu,

Wanda a yau saboda abubuwa masu muhimmanci kuma masu nauyi da ake ajiyewa ko ake zubawa a cikin wannan mazubi wato Memory yana qaranci a wayoyin da dama daga cikin mutane,

Wanda dalilin haka ne ma ya sa aka samar da wani mazubin na daban wanda ake kira da “External Memory Card” wanda za ka iya sakawa a wayarka domin samun qarin girman wannan mazubin ko ma’adani,

Amma duk da samun qarin wannan mazubin hakan bai iya biyan buqatar da yawa daga cikin mutane ba,

Wanda hakan ne ya sa shafin www.nasara.com.ng yau zai yi bayanin wata hanya da zaka bi domin qarawa wayarka yawan adadin storage yadda kake so koda sama da 100GB ne,

Abu na farko da kake buqata shine  ka sauke manhajar TELEGRAM, 

Wannan manhaja ta TELEGRAM a itane ake iya yin ajiyar da bata da adadi,

Kana iya ajiye Photos da videos da Audios da Documents da Texts masu nauyin gaske akan wannan manhaja ta TELEGRAM, 

Abu mafi ban mamaki da wannan manhaja shine ko da ka gogeta tsawon lokaci ko shekaru to duk lokacin da ka dawo da ita to za ka samu wannan ajiya taka,

Sannan kuma idan har kana so wani ma ya iya samun abubuwan da ka ajiye a cikin wannan manhaja ta TELEGRAM to daga baya kana iya bashi damar yin hakan.


Yadda Za Ka Yi Amfani Da TELEGRAM wajen Ajiye Abubuwa Masu Nauyin Gaske

Bayan ka sauke manhajar TELEGRAM ka yi rijista da ita kamar yadda kake rijista da sauran kafafen sadarwa kamar su Whatsapp, Facebook, Twitter da sauransu, 

Sai ka shiga profile dinka, za ka shiga profile dinka ne ta hanyar ta6a wasu layuka guda uku da suke sama a sukurwar gefen hagun,

Bayan ka ta6a su  za su nuna maka MENU na profile dinka sai ka nemi wajen da aka rubuta NEW GROUP wanda shine na farko sai ka ta6ashi, 

Zai buqaci ka za6i wanda kake so su kasance a cikin group din aqalla shine mutum daya, 

Sai ka za6i ko da mutum daya ne, idan kuma kana da wata lambar wadda itama kayi rijista da TELEGRAM kawai sai ka yi adding dinta ita kadai ba sai ka saka wani ba,

Idan kuma wanin kayi adding to kana gama creating din group din sai kaje ka cireshi sai ya rage sai kai kadai ka rage a cikin ma’adanarka ta TELEGRAM,

Bayan ka zabi wanda zakayi creating din group din da shi sai ka ta6a wata alamar kibiya wanda za ta kaika wajen da za ka rubuta sunan group din, 

Sai ka za6i wani suna, Misali:- My Storage, My Memory, My Store, ko kuma dai sunan da ka ga yayi maka, 

Bayan ka gama qirqirar group din shikenan sai ka dauko duk wani abun da kake son ajiyeshi ka zuba a cikin wannan group din na TELEGRAM da ka bude, wanda hakan zai baka space akan Memory na wayarka,

Duk abin da ka zubashi cikin wannan group din naka to kana iya gogeshi daga kan ainishin Memory din wayarka, duk lokacin da ka tashi nemansa sai ka taho cikin wannan rumbun naka na TELEGRAM group din da ka ajiyeshi.

 Abubuwa Masu Muhimmanci

Akwai wasu settings masu muhimmanci da ya kamata ka yi domin bada kariya ga wannan ma’ajiya taka. 

1. Dole ka mayar da setting din group din ya tashi daga Public ya koma Private , domin idan ka barshi a Public to kowa ma zai iya shigowa cikin group din ko da bashi da link na group din ta hanyar searching din sunan group din, wanda shigowarsa cikin group din zai iya bashi damar riskar abubuwan da ka ajiye, amma idan ka maidashi private ba wanda zai iya shigowa sai wanda ka yi adding dinsa ko ka tura masa link yayi joining. 

Ga yadda za ka maida setting din ya koma private:-

Za ka je ka shiga cikin group din sai ka ta6a kan sunan group din zai kawoka zuwa ga shafi na gaba, sai ka ta6a alamar pencil da ke sama gefen sunan group din,

Bayan ka ta6a alamar pencil zai kawoka wannan shafin da ke qasa, sai ka ta6a wajen da aka rubuta GROUP TYPE sai ka shiga ka maidashi Private , shikenan ka gama wannan.

2. Abu mai muhimmanci na gaba shine “Chart History For New Members” ma’ana bada dama ga sabbin membobi da za ka saka cikin group din nan gaba su iya riskar irin abubuwan da ka tura cikin group din kafin su shigo,

Za6i Biyu ne anan; akwai Visible akwai Hidden ,  Idan ka barshi a Visible to duk abubuwan da ka saka cikin group din tin kafin su shigo to suna da damar riskarsa, shi kuma Hidden ba za su samu damar riskar abubuwan da ka saka kafin su shigo ba sai ka za6i wanda ka ga yayi maka,

Za ka yi hakan ne ta hanyar bin matakan da nayi bayaninsu a sama lokacin canja Group Type, Amma yayin da kaje wajen Group Type a maimakon ka shigeshi sai ka shiga  na qasansa wato “Chat history for new members”.

Duk wani photos ko videos ko Audios ko Documents ko Text da ka ajiyeshi a cikin wannan group din to kana iya riskarshi da kowanne lokaci kuma ka iya saukeshi zuwa cikin ainishin memory na wayarka a duk lokacin da ka ga dama ko da bayan tsawon shekaru ne.

Wannan shine takaitaccen bayani mai dauke da cikakken bayani akan yadda za ka qara adadin yawan Storage din wayarka zuwa adadin da kake so.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button