Yadda Za Ka Rage Nauyin VIDEO Duk Nauyinsa Har Zuwa Qasa Da 50MB Ba Tare Da KYAWUNTA Ya Ragu Ba


Yadda Za Ka Rage Nauyin VIDEO Duk Nauyinsa Har Zuwa Qasa Da 50MB Ba Tare Da KYAWUNTA  Ya Ragu Ba

Wannan wani Application da ake amfani da shi wajen rage nauyin Video,

Da yawa su na ajiye videos a cikin wayarsu wanda hakan yana cinye musu space mai yawa a cikin wayoyinsu,

Wasu ma duk da External memory Card da su ke qarawa cikin wayarsu amma duk da haka wani lokacin sai ka ga suna buqatar space saboda Videos masu nauyi sun cika musu duka external da internal memory card, 


Wannan Application da za muyi bayani zai ba da damar rage nauyin Video sosai, domin yana iya rage nauyin Video duk nauyinta har zuwa qasa da 50MB ba tare da kyawun Video (Quality) ya canja ba ko ya ragu,

Wani abin birgewar ba iya Videos Videos wannan application ya ke ragewa nauyi ba, har hotuna wato pictures ya na rage musu nauyi.


Wannan Application Ya na đauke da Abubuwa (Features) kamar haka:-


1. Compress Video:- Wannan Itace feature da ake shiga domin rage ko kuma matse nauyin Video. 

2. Cut And Compress:- Wannan feature din ana shiga ne idan ana so a rage nauyin video sannan kuma a yanki wani 6angaren na videon domin yin status a WhatsApp ko Facebook ko kuma đorawa a Tiktok ko Instagram. 

3. Fast Forward:- wannan ana shiga cikinta ne domin qarawa video sauri, Misali kana so ka yi status da Video a WhatsApp, amma kuma tsawon mintunan video ya kai Second 40, To za ka shiga cikin wannan feature din ka qarawa videon gudu ya dawo zuwa Second 30 ba tare da ka cire wani yanki na videon ba.

4. Extract Mp3:- idan ka na so ka tace/core Audio daga cikin wata video, sai ka yi amfani da wannan feature din. 

5. Play Video:- Ka na iya amfani da wannan feature din domin kallon video ma’ana ka yi amfani da shi a matsayin Video Player kamar MX player da VLC Player. 

6. Share And Delete:– Wannan ana amfani da su ne domin tura Video ko hoto (SHARE), ko kuma a goge su (DELETE).

7. Edit Video:- Ana amfani da shi ne wajen qara wani abu a cikin video ko kuma a cire wani abu daga cikin video, sai dai kuma shi wannan application din ba ya yin wannan aikin sai dai ya yin da ka danna zai đaukeka zuwa rumbun Manhaja wato playstore domin sauke application din da zai maka wannan aikin, Ana amfani da shi domin gyara Video domin a qara mata wani abu ko kuma a cire wani abun daga cikinta. 


Wajen Da  Za  Ka Samu  wannan Application

Sunan wannan Application da mu ke bayaninsa shine COMPRESS VIDEO AND VIDEO CUTTER, za ka shiga cikin Playstore sai ka yi searching dinsa, ko kuma ka latsa wannan LINK da ke qasa Wanda zai đaukeka zuwa cikin Playstore har kan Application din. 

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.idea.videocompress

Join Our  Social Channels For More Latest Update

TELEGRAM
WHATSAPP
FACEBOOK



Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button